Saturday, 5 November 2016

[7:32pm, 11/5/2016] Hawwa: [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 66-70 Wannan rana ba karamar wahala deeja tasha ba shi kanshi sadik saida y tausaya mata, ganin takasa mikewa yasanya sadik kuka gami da bata hakuri itama deejan kuka takeyi ganin jinin da tai a jikinta da bata taba ganiba, haka yaita kokari wajen ganin y gyara deeja, wanka y fara yimata sannan ya gasata a ruwan zafi, takusa awa daya ckn ruwan sannan ya umarceta ta tashi, ckn ikon Allah yaga ta taso nan murna t ishi sadik sbd deeja da kafarta taje daki dg bandaki, d yai zaton ko wani gagarumin abune y sami deejan sabida yaga ranar d yatare d hajiya hakan bata faru g hajiyanba. Albrk d yabo ba irin wadda deeja bata samuba a gurin sadik a wnn safiyar jiyai ashe hajiya fankoce ba abinda yake sha a gurinta sai wahala, yanxu yasan yayi aure d sanin dadin auren,rirutawa d tattali ba wacce bayaiwa deeja sakamakon jinta dayai gargarrrrr d ita ba alamar kwancewar noti,yini yai yana dawainiya d deeja koda tai yinkurin yin wani abun saiya hanata. A bangaren ardo kuwa farin ciki y mamayeshi ganin dan nasa cikin farin ciki da amaryarsa, km yaga har sadik ya kwana 5 baida alamar tafiya birni, yau d la'asar sakaliya ne sadik yaje gaida mahaifinsa, tarar dashi yai a kan dakali yana hutawa, sun gaisa yake tmbyr sa deeja yace lafiya lau take,madallah yace sukaci gaba d hira can ardo yake tambayr sadik yaushe zai koma birni,dammm yai sannan yace inasa rai jibi zan koma, nan ardo yake cemishi inson samune ya tafi da matarsa,yankewa gaban sadik yai ya fadai gami d zaro ido yace baffa ai banida inda zan ajiye deeja a birni nima a shagon abokina nake,ardone yace to yanxu tinda kayi iyali saika kama daki ai,gyara zama sadik yai gami da yar dariya yace baffa kenan kasan kuwa daki a birni tsadane dashi bazan iya biyan kudinba dan albashina ma bazasu isa nai wahalar gida sanna n biya hayaba, ardo yai mamakin jin kofofin d sadik kemasa duk ta inda ya bullo saiya bille kmr mara gaskiya baisan kuwa mara gaskiyar bane cigaba sukai d hira har aka kira sallahr magriba. A wannan daren sadik yaso kara aikata abin da ya aikata a daren jiya saidai y hakura sakamakon rashin samun hadin kai gurin deeja sbd ba karamar gurzuwa taiba dan har lokacin jikinta ciwo yake,duk d haka sadik bai hakura ba saida ya hana deeja ishashshen bacci. Can bangaren kuwa hajiya t gama zaucewa da tunanin sadik, mafarke mafarke d sumbatu b irin wanda bataiba sanadiyyar rashinsa,farin ciki d nisha yai kaura dg gareta,in ka kalli fuskarta zaka rantse bata taba walwala d fara'a ba,duk tafita hayyacinta kamar bata taba tarayya da d'a namiji ba,abinci kuwa bata iyaci ta maida tunani d kuka y zama abinci d abin shanta duk sanida sadik bayanan ni shatuwalle su hajiya har dasu kuka,wannan shine sabon salo tusa a loudspeaker. Da zarar mun hada ido d ita sainai mata alamar taban tausayi da zarar t juya baya kuwa na tintsire d dariyasu hajiya anfada tafkin kogin son sadik shiko yanacan y manta d batunta. Haka sadik y cinye mako guda yana shan amarci har yaji bayason yai nisa d deeja dan yanxu tafiye masa kwanciyar hankali akan hajiya,kuma a ranar yai shirin komawa garin kaduna,sadik d deeja ba irin kukan rabuwar da basuyi dan iya zamansu sun shaku d juna haka y lallabata sukai sallama gami da yimata alkawarin zai dunga zuwa duk sati, gidan ardo ya nufo yai masa sallama tare d sanar masa yanan tafe duk karshen mako,daga nan bai zame ko inaba sai tashar mota. Cikin farin ciki nishadi ya baro mahaifar tasa dan a lokacin yagama tinani da tanadin abinda zai zayyanawa hajiya da zata yadda dashi batare da samun matsala a gurinta ba. Ayushailiasu.blogspot.com [7:14pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 71-75 Tinda sadik y taho deeja take cikin kunci saboda bataso tafiyar sa ba, taso ace koda zai taho sutaho tare gata gashi saidai hakan baisamuba sbd kasancewar sadik baida gaskiya. A cikin mota kuwa gaban saadik sai dukan uku uku yake, fargabar irin hukuncin d Hajiya zata yanke mishi yake kanya farga har sun iso garin kaduna, achaba y tare y hau tare d umartarsa y kaishi gidansu abokinshi salele wanda suke koyarwar guri daya, salele saurayine Mai hangen nasa d zurfin tunani kullum suka hadu d sadik nasiha zakiji yanaimasa tare d tunatar dashi duk wanda y hau motar kwadayi zata saukeshi a tashar wulakamci, kullum yana nuna mishi wadatar zuci ita tafiyewa dan Adam zaman lfy, dariya Sadik yakeyi tare d cewa lallai abokina n yarda har yau a duhu kanka yake, sanadiyyar haduwata d hajiya n keta hazo n ziyarci kasashen laraba harma dana masu jajayen kunnuwa, inci Mai kyau n sha Mai kyau, n kwana a AC, direba y jani a mota, duk wani abun rayuwa danake bukata van rasashi b, sannan kana batun n rabu d hajiya, inma mafarki kake toka farka maganganunka kuma shiga suke suna futa kamar busar iska,zama d Hajiya yanxu n fara, dama zuwanai n sanar dakai nayi aure AURe ,dariya kabiru yayi tare d cewa mutumina wasa kake, n tabbatar hajiya bazata amince K auri wata diya mace a duniya mace aba, murmushi Sadik yayi yace bansanar d itaba, kaikadai n budawa sirrina ina fata zaka rikemin, abin y baiwa kabiru mamaki shidai Sadik yama fara bashi tsoro ,Adduar fatan alkhairi yai mishi d fatan zaman lfy, Sadik y zaro wayarshi daga aljihu y mikawa kabiru tare d cewa ajiya n kawoma, yanda n baka ita haka dan Allah karka kunna, kabiru yace karkasamu damuwa, yanda kace haka zaayi. Sukaiwa juna sallama Sadik y nufi gidan hajiya. Bangaren hajiya Kuwa tin abinnadamunta, harta fara tunanin cewa d gayya habibinnata y kashe wayarsa, inba hakaba kullum saita kirashi fiye d sau 30 ,harsai cajinta y Kare zata hakura d dialling number dinsa, ta dau alwashin cin zarafinsa, tare d alkawarin yanda y wahalar d ita, saita gasashi itama. Ayushailiasu.Blogspot.com [7:35pm, 11/5/2016] Hawwa: [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 76-80 Kwance take bisa lallausan gadonta tayi lamo d ita, idonta a lumshe kmr mai bacci saidai b baccin take ba dan yai kaura dg idonta tunini kawai take ya rayuwar habibinta take, sabida mai ya nisanceta tsahon sati daya, daga sama taji sallama kmr a mafarki, firgigit t juyo gami d sake murje idonta, tabbas b mafarki takeba sadik tagani suna hada ido ya karaso d sauri ya rumgumeta tare d sumbatarta waishi a lallai yana nuna yai missing dinta alot, batasan ya riga ya gama shirya irin karuwanci alalan geron d zai mataba dan yasanta da son a nuna mata salon soyayya kmr wata juliat ko lailah majnoon,abin nemane ya samu matar falke ta haifi jaki tini hajiya ta fara mayar masa d martani, sundau lokaci a haka harsaida suka fita a hayyacinsu,suka lula wata duniyar daban kasancewar hajiya a matse take, saida komai y kammala sannan suka dawo wnn duniar tamu.duk wani cin zarafi d Hajiya tai alkawarin yiwa sadik amma t kasa. Lokacin d suka dawo hayyacinsu ne y karewa hajiyar dake kwance kallo ya rausayr da murya tare d kashe ido kmr dan daudu, kwantowa daidai kirjinta yai yace hajiyata meya sameki naga kin rame? ko rashin lafiya kikai? Marairaicewa tai cikin shagwaba tac haba habibina ba dole na rame ba sabida rashinka kusa dani kasanyani cikin kogin tunani nakasa ci na kasa sha bacci yai kauracen, banajin nishadi da walwala sbd rashinka,tsayawa n zayyana muku abinda hajiya take fadawa sadik na irin kewarsa da tai zaa dau shafuka baa gamaba, take sadik yaji tausayinta gami da bata hakuri ta hanyar cewa shima haka y tsinci kansa sabida rashinta kusa dashi. Wannan ranar hajiya kasa bayyanawa sadik bacin ranta tai na tafiyar da yai har sati daya saboda kawai tanadon ya biya mata bukatarta da tasaba duk dare gashi tai sati guda bata samuba. Sunyi sallar azahar suka nufi dining,ranar abinci ma abaki sadik kebawa hajiya dan ya nuna mata har ynx tana zuciyarsa,amma a bangaren zuciyar tasa ba haka bane deeja ce kwance a cikinta kawai sabida kwadayi dason abin duniya yasa sadik bazai iya rabuwa da hajiyar ba amma deeja tafiye masa nutsuwa yanxu,abinci yake bata suna hira take cewa habibina ai ban taba tsammanin zaka iya kwana daya batare daniba,fuska y canja yace haba hajiyata kinsa ni nakine fa, tace ai abin ne yaban mamaki meya zaunar dake ka barni inata adduar Allah ys lafiya dai,daidai lkcn ya kara kai spoon daidai bakinta t kauda kai alamar takoshi, ajiye spoon din yai ya nisa gami d ajiyar zuciya alamar mara gaskiya shafa keyarsa yai yace wllh hajiya ina zuwa kauye baffa yace dama ni yake jira zanmasa rakiya wani kauye ashe b ranar zamu dawoba, hmmmm tai tace amma ba irin kiran wayarka da banyiba switched off yace wllh service ne babu a garin ,karshema aka sace ta, shiyasa kikaji bankirakiba ,hakadai sukaitayi intace kaza yace kaza,su sadik akwai kofofi kamarta chali har saida yaga hajiya tana dariya sbd duk sanda zai mata magana da alamar raha, wasa da tsokana yake mata.tare d shafo wani sashe n jikinta Palo suka dawo suka xauna sukaci gaba da sheka soyayya dan wani abu d hajiya taiwa sadik batasan ina labe b zaro ido d tsoratar da nai ne yasa biron hannuna ya fadi kasa jikake 'kirrrrr, jin karar ne yasa sadik juyowa nan mukai ido hududashi ya dokan uwar harara d sauri nadau biyona na felle a miliyan ?karyacewa hajiyarsa labe nake musu ta zauneni niko gani yar firit dani kmr allura. Ayushailiasu.blogspot.com [5:04pm, 11/5/2016] A AYSHA: 👱🏻👱🏻👱🏻MIJIN HAJIA👱🏻👱🏻👱🏻 ✍🏻………Written:-Ayusha Iliasu. 👂🏻………Story:-Hawwa Saleh. 81-85 I DEDICATED DIS PAGE TO NAMESAKE AYSHA BAWA( GENTLE) *After 2 weeks* Sadik ne zaune cikin staffroom y hada kai d guiwa ya rasa abinda yake masa dadi sabida yaiwa deeja d ardo alkawarin zai dinga zuwa duk karshen mako gashi yanzu har mako biyu ya wuce baije ba, tinani kawai yake yadda zaiyi, wace karyar zaiwa hajiya ta barshi ya kara xuwa kauye dan yanxu a matse yake yaga deeja,gashi kuma hajiya takasa ta tsare bata barinsa ya sake kamar da, haka y gama tinaninsa har aka tashi baisami mafita ba. Can kauye kuwa Ardo ya tashi hankalinsa sbd rashin ganin sadik gashi har yau alhamis zaa cinye sati n uku baizoba,ardo baiyi kasa a guiwa ba da yammacin wnn ranar ya tashi yaje gidansu a bokin sadik, yana isa ya tarar dashi a dandali suna shan rake, suna kwasar hira d abokansa,takaicine y kama ardo a zuciyarsa yana cewa duba dan Allah gwanin sha'awa yara sunata hira amma nawa dan ya tafi birni yabar mahaifarsa .da yananan da mai zaikawoni gurin wnn yaran, karasawa yai garesu yai musu sallama, cikin nutsuwa suka gaisar dashi y amsa tare d cewa nasiru abokin sadik din yanason magana dashi, gefe suka koma yake sanar dashi zuwa yai don Allah ya kira masa sadik a waya yaji ko lapiya sunata tsumayin ganinsa har gashi zaa cinye mako na uku shuru,take nasiru ya zaro wayarsa dake aljihu y lalubo wayar sadik bugu daya aka cemasa switched off maana akashe take, nan ya fadawa ardo , godiya ardo yai masa tare d rokonsa dan Allah anjima ya sake kiransa sannan ya fadamasa lafiya suna tsimayinsa,amsa masa yai dacewa insha Allah zan kirashi kuma zanzo har gida nafada maka yadda mukai nan sukai sallama ardo ya nufi gida cikin zulumi. Dazarar sadik ya dawo dg makaranta hajiya zata karbe wayar data saimasa tinda y dawo dg kauye, sbd yace waccan ansace, tare d sabon sim card ta kashe, bazaa kunnaba sai gari ya waye zai tafi makaranta ,shima dan tanason ta ringa kiransa ne danjin muryarsa,ace warta wai sadik ba shida wanda zai kirashi a waya inba itaba,balle kuma ta barshi ya fita hira majalisa, hatta jam'in masallaci hajiya ta hana sadik zuwa duk abin duniya ya taru yai masa yawa.maganin Mai kwadayi 😂😂😂,kuda wajen kwadayi akan Mutu. Bayan sallar magriba nasiru ya sake kiran wayar sadik akashe haka y je yafadawa ardo baisamu wayarba, sannan ya kara masa da cewa ya tura masa sako (text message ) inya bude wayar zai gani, godiya ardo ya kara yimasa, bacci a wannan ranar ardo kasawa yai sbd zulumi d tunanin wane hali sadik din yake ciki,abinda yafi damun ardo shine deeja d aka rabo d iyayenta. Yau juma'a sadik ya gama shirin tafiya makaranta, sallama yaiwa hajiya cewa yatafi nan taimasa adawo lafiya tare d cewa habibina kafa kulamin da kanka kasan weekend zaa shiga,karasawa yai yamata kiss gami dacewa angama hajiyata ya fito, yana fitowa bai zame ko inaba sai gidansu salele dan karbo wayar da yabashi ajiya sbd ya manta bai fada masa jiya da aka tashi dg makarnanta ya taho masa d ita yau ba,mamakine ya kama salele ganin sadik ya biyo ta gidansu, sun gaisa yake cewa wayarnan xaka bani, yadda sadik y baiwa salele wayar nan a kashe haka y dakko ya danka masa karbayai yaimasa godiya ya juya yace saika karaso. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: 👱🏻👱🏻👱🏻MIJIN HAJIA👱🏻👱🏻👱🏻 ✍🏻………Written:-Ayusha Iliasu. 👂🏻………Story:-Hawwa Saleh. 86-90 Kunna wayar sa ke da wuya da zummar kiran nasiru ya tambayeshi lafiyar gidansu sakon da nasirun yaimasa a daren jiya yashigo cikn habzari y bude y karanta hankalinsane ya tashi da jin sakon mahaifinsa, tinani y shigayi y zaai ya je kauye ayau ko gobe, duk da sadik bai samu mafitar yadda zai yaje kauyeba ya kira nasiru byn sun gaisa yake sanar dashi yaga sakonsa,dan Allah yaje y fadawa ardo gobe yanan tafe sannan yace masa aikine yai yawa yara sun kusa fara jarrabawane shiyasa baizoba, nan nasiru yace insha Allah zaije ya fadamasa, sallama sukai yaimasa godiya ya nufi hanyar makarantarsu jiki a sanyaye. Wannan ranar sadik kasa tabuka komai yai a makaranta idan monitor tazo tai kiransa saiyace yana zuwa dalibai suita jiransa amma shiru har period din tafita baijeba. Uban tagumi ya zuba a ckin staff room yarasa madafa,salelene ya taso dg gaban table din d yake xaune y karaso inda sadik yake dafashi yai yace mutumina lafiya kake kuwa yau?ko hajiyarce ta tabaka ne? Ajiyar zuciya sadik yai sannan y nisa yace kaidai bari kawai wllh kaga tinda nadawo dg kauye yau sati uku kenan bankomaba km nace d baffana da matata zan dinga zuwa duk karshen mako,gashi yanxu bankoma b harsaida baffa yasa akaimin waya, yar dariya salele ya saki yace to meya hanaka xuwa? Yace wllh hajiyace ta hanani sakewa nan sadik y kwashe duk abinda hajiya tak masa na takurawa y fada mishi,shiru sukai n wani lokaci sannan salele yace sadik ba irin shawarar d ban bakaba game d auren hajiya kashafawa idonka toka kai, ka biyewa son zuciya da kwadayi, ai gashinan dama duk wanda y hau motar kwadayi bazata saukeshi ko inaba sai tashar wulakanci, gashinan kazana MIJIN HAJIA ai. Haushine y kama sadik saboda maganganun salele sun masa ciwo ransa y baci saidai bai nunawa saleleba y daure yace abokina kabani shawara kawai yadda zanyi dan nace afadawa baffana gobe zanzo,tinani salele y shigayi can yace dashi kasan ydd zaai? Aa ya cemasa, yace idan kakoma kacewa hajiya principal yace gobe zaka kai students escortion saboda karatowar jarrabawarsu,kaga dole tabarka kazo kana fitowa saika cale kauye, wani ihu sadik y saki tare d rungumeshi yana nagode d shawararka mutunima suks tafa, tafawar dasu kai tai daidai d kada bell time din tashi yayi sabida ranar juma'ace d wuri ake tashi,wayar daya karba a gurinsa ya mikamar yace ka ajiyen gobe inzan wuce zanzo n karba, dariya salele yai ya karba ya sa a alhihunsa. Cikin murnar samun mafita sadik y karasa gida lkcn hajiya ta dau wanka tana jiran dawowar habibinta, jin sallamarsa ne yadawo d hnkalinta bakin kofa ckn fara'a yaxo y rungumeta, sannu d xuwa taimasa gami dacewa habibina kahuta kaci abinci sai kai wanka zamu fita,zumudine y kama sadik ckn wage baki y amsa mata, kashe ido hajiya tai cikin shagwaba t matso d bakinta daidai kunnensa tace habibina kasan inda zamu?shima cikin shagwaba y matso kusa d kunnanta yace saikin fada hajiyata, tace gidansu abdul zamuje yaronsa baida lafiya zamu je mudubashi amma sai munfara zuwa store an saimusu kayan dubiya, yace to bari naje na watsa ruwan naci abinci sai mu tafi, cikin tsokana tace ko nazo naimaka wnkan, dariya yai yace saidai in kinyarda kisake wankan sai muyi tare,murmushi sukaiwa junansu sannan ya shige daki. Ayushailiasu.blogspt.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 91-95 Fitowa yai cikin milk din shadda dinkin boda wadda akaiwa aiki da bakin zare tai masa kyau yasa bakin takalmi covered, agogon daya sama abin kallone shima black, kallo daya zakai masa kasan ya hadu to d core, yadda fatar jikinsa ke sheki zaka tabbata yana jin dadi sosae,kamshi ne kawai ketashi n designer perfume din d hjy t sayo mishi a london, ya taje sumar kansa d sajensa sun kwanta sunyi liff, duk wata budurwa mai ji da kanta inta kalleshi sau daya zata ji sanshi,sadik kenan yaro dan kwalisa, kamshin tiraren d yake tashine ya tabbatarwa da hajiya cewa angon nata ya hadu, yana karasowa suka kashewa juna ido gami dace masa woawwww habibina, hakika tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wanna sura mai kyau d nutsar da zuciya, gaskiya habibina ka hadu kayi kyau, gaskiya nayi dace da samun wannan halitta kyakkyawa, murmushi ya sakarmata mai dauke d sakonni kala kala yace haba hajiya banda zuga fa har nakaiki kyau? itama murmushin taimasa tace ai habibi tsayawa na lissafama irin haduwar dakai zamu bata lokaci. Lokacin daya tako zuwa gareta ne tai saurin cewa tsaya tsaya dole nadau pix din wannan kwalliyar ko naringa kallonta nasamu nutsuwa,chak ya tsaya yana yar dariya, wayarta ta dakko datake ajiye a gefenta taimasa pictures sannan y karaso y zauna daf da ita. Kallo ta kare masa tace anya kuwa habibina zamu fita unguwarnan?kallonta yai yace saboda me hajiyata?tace jikina yai sanyi ne saboda wannan kyau d kwalliyar daka dauka, dariya yai yace to saime? tace kaga fa har store zamu tsoro nake kar wata taganka taimin snatchin taga dan saurayi hadadde, kissindinta yai yace kin manta ni nakine, aa ban mantaba, yace to kibar wannan tinanin kuma ki rubuta ki ajiye sadik nakine har abada,huggin dinsa tai tace shikenan habibi amma ina tsoron yanmatan yanzu shiyasa banason ka ringa yawan fita waje, dariya yai yace to mutafi ko, tace ai bakaci abincinba yace ai tinda naganki naji na koshi, marairaicewa tai tace plxxx kaci ko kadan ne banason ulcer ta kamaka ko kasha drink, yace to bari nasha drink kawai tare d mikewa ya nufi fridge ya dakko,abin na bawa sadik haushi duk ji dashi d hajiya take bai isa takawo masa abinci ba saidai komai yai da kansa badai taimasa kamar yadda kowace mata kewa mijinta. Niko nace Allah y kara kwadayi mabudin wahala kenan kuma dama inda kwadayi da wulakanci ai kadan ma kagani sadik tafi tafi ma da sannu reshe zai juye d mujiya saika koma MIJIN HAJIA na kwarai. Atare suka jero suka fito parking space din gidan, motar hajiya suka nufa da take rife da tempol, duk irin wannan gayun da sadik yai da kansa ya cire tempol din yasa a boot sannan ya zo y budewa hajiya motar tashiga sannan shikuma je ya shiga drivers seat kasancewar shi zaiyi driving din, tada motar yai tare d yiwa gate man horn ya bude musu lokacin nai tsalle d ihu n kwashe d dariya ?saboda tino sadik danai y gama cire tempol din d aka rufe motar yana karkade kurar da ta sauka jikin gogaggiyar shaddarshi maganin dan iska karen maguzawa kenan, ai dama hajiya tasan sabida kudinta sadik ya yadda ya aureta da batada sisi bazai rabeta ba. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 95-100 Mall suka fara zuwa sukaiwa fauzan son din Abdul shopping din kayan dubiya suka zarce gidan,a tare suka shiga palon sallamarsu tai daidai d fitowar matar Abdul maryam dg kitchen, ganin hajiar su abdul sun jero d sadik ne yasa maryam tai saqare ya jakar gyartai akwanika,kasancewar abdul ya sanar da ita cewa hajiyarsa zatazo ita d mijinta, mamakine ya kama maryam da alamu ydd hajia ta riko hannun sadik shine mijin nata, dan a iya sanin d taiwa hajiya batasan wannsn yaron d sukaxo dashi tareba kuma bata taba ganin mijin d hajiya ta auraba balle ta tantance, dariyar yake maryam ta amsa sallamarsu tare d yimusu iso zuwa ckn palon, ganin sun zauna daf d junansu ko kunya hajiya batajiba a gaban surukarta, yasanya maryam tabbatar d cewa shine angonnata. Har kasa maryam t tsuguna ta gaida hajiya tare d sadik ckn girmamawa suka amsa tare d tanbyr jikin fauzan, kitchen ta nufa ta kawo musu abinci d drink d ruwa, sun dansha drink din sannan suka mika mata kayan dubiya tai musu godiya suka taho, tinda suka taho maryam b abunda take banda mamakin son zuciya d son kuruciya irin ta hajiya data auri dan cikinta dan baifi sa'an abdul ba.dariya tayi a zuci hahahhh tace wannan kece hajiyar gidigo. Acan kauye kuwa bayan sallar juma'a nasiru ya nufi gidan ardo dan ya shaida masa sakon sadik,yana isa kofar gida ya aika yaro ayomasa sallama d ardo,yaron d ya aika ya fito yace yana zuwa, b jimawa ardo y fito, ganin nasiru ne ya sanyashi yin fara'a, bayan su gaisa ne yake shaida masa cewa sadik yace yananan zuwa gobe,jin wannan labari ba karamin dadadawa ardo rai yaiba, godiya yai masa tare d cewa Allah y kaimu goben sukai sallama ardo ya koma cikin gida, yana shiga ya aiki yaron mirigayya ladingo yaje ya fadawa deeja gobe sadik zaizo , da gudu yaro ya tafi ya fada mata,jin yarom yace d deeja gobe babansu zaixo ne ya sanya deeja murna d farinciki nan take ta shiga shirye shiryen tarbar miji. Bayan sallahr magriba sadik d hajiyarsa na zaune suna kallo a palo, gyaran murya sadik yai yace hajiyata tace naam habibina yace gobe in Allah y kaimu principal yace zamu kai dalibai escortion saboda sun kusa fara jarrabawa, shagwabewa hajiya tai tace amma meyasa principal zai min haka baisan weekend likacina bane zaice kuje gobe, gaskiya baxakaje ba kawai kabani number dinsa nakirashi na fadamasa wani malamin ya wakilceka kana da uziri, gaban sadik ne yai mugun faduwa ya zaro idoyace haba hajiyata kinsan harkar aiki b yadda bata kamawa kiyi hakuri baxamu dadeba zamu dawo,dagewa hajiya tai itafa Allahn katafar sadik bazai jeba hakan yasa hankalin sadik yai kololuwar tashi ya rasa yadda zaiyi can dabara ta fado masa, take y fara yiwa hajiya abubuwan da tafiso cikin hikima ya shawo kanta ta yadda zaije. A wannan daren sadik ya farantawa hajiya yadda bata zataba duk dan t yarje mishi zuwa escortion ,dan cimma burinsa n xuwa kauye, saboda haka ya jajirce kasancewarsa gwarzo jarumin namiji irin wanda hajiya takeso don yana biya mata bukatarta fiye d zatonta. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 101-105 8:00 na safe bayan sadik ya gama breakfast ya shirya tsaf , lokacin hajiya n kwance tana bacci bama tasan ya shirya haryai karin kumalloba, nemar gefen gadon yai ya zauna yana karewa haiya kallo tare d tunanin hikimar d zaiyi wajen tashinta yace yatafi, gefen fuskarta ya shafa d lassausan hannu sa da yake ta kamshin perfs take hajiya taji wannan kamshin ya ziyarci hancinta, ido ta bude a hankali taga sadik ne zaune kusa d ita, bude baki tai d niyyar magana yai saurin manna mata kiss take tai shiru, rike kuncinta yai d hannayensa y matsar d bakinsa daidai nata yace hajiyata nifa nagama shiri zan wuce kallonsa tai tace harka shirya d sassafe zaku tafi yace yanxufa 8:30 tayi dandai kina baccine shiyasa kike ganin safiya ce, murmushi tai daga baya kuma d ta tuna sadik fa tafiya zai ta bata rai tace gaskiya habibina dolece zatasa kafita yau kodai kajirani na shirya mutafi tare,wani abu yaji ya tsirga masa a cikin jinansa zarrrrrr sai kawai y daure bai nunawa hajiya firgicin da yaji a zuciyarsa, murmushi ya sakarmata yace kin manta bani kadai bane da dalibai zamu,huggin dinsa tai tace adawo lafiya ka kulamin da kanka kaji habibina Allah y kiyaye hanya, amin yace tare d saurin mikewa ya nufi kofar fita.hamdallah y shiga jerowa a zuciyarsa Yana fitowa bai zame ko inaba sai gidansu salele dan karbar ajiyar wayar, yana zuwa cikin hanzari suka gaisa, salele na cewa mutumina plan dinmu yahau ashe, ajiyar zuciya yai yace dakyar ba ai sai da naci kwakwa kfn ta yadda dan harcewa tai zata boyini ko nabata number principal takirashi,dariya ce ta subucewa salale batare d yai niyyar yiba, karbar wayar yai sukai sallama ya nufi tashar motar da zata sadashi d mahaifarsa. Tin asubar ranar asabar deeja d tatashi tai sallahr asuba bata kara rintsawaba tashiga gyare gyare, ta share dakinta tsaf tare d lailaye gado ta kunna tiraren wuta ko ina y dau kamshi sannan tai wanka ta shirya tsaf ckn riga d skirt n material sun matakyau, abinka d diyar fulani ta gyare gashinta sannan ta zubo dashi har gadon bayanta, nima saida na yaba kwalliyar nan kafin ango sadik y yaba dan nasan baxai ki yabawa ba, guri t nema t zauna ita a lallai tsumayin karasowar sadik take wata zuciyar t raya mata ,"dama ace sadik ya shanyaki yaki zuwa naga y zakiyi safiyar ranar deeja ko karin kumallo bataiba sabida zumudin tarbar ango. 10:30am daidai sadik y sauka a kauyensu,kofar gidan mahaifinsa ya nufa suka gaisa, ardo ba karamin farin ciki yaiba d ganin sadik, nan suka taba hira yake bashi labarin zulumin da suka tsinci kansu sabida rashin zuwansa nan shima ya bashi hakuri d hada karya d gaskiya ya shararamasa,ardo ne ke cemasa amma ai zaka kwana biyu ko? yace masa a'a yau zai juya,fada ardo ya fara yimasa ta inda yake shiga batanan yake fitaba har yana cewa zai hanashi komawa birnin tinda hakane ya xai auro yar mutane ya shalla ya barta, jikin sadik duk yai sanyi dajin kalaman mahaifinsa ya kasa magana, lokacin ardo ya kara d cewa lallai tinda haka zai ringa yi inya shuda ya tafi sai an nemeshi baxai waiwayi iyalinsaba to ya nemi daki a birni ya tafi da matarsa, ganin ran mahaifin nasa ya baci ne yasa ya bashi hakuri tare da alkawarin insha Allah zai nemi daki, sallama sukai ya bashi tsarabar dayayo musu sannan y mike cikin rashin kuzari ya nufi gidansa. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 106-110 Deeja n zaune ba abinda take illah tinanin sadik kardai bazai zoba dan ganin rana tayi har 11:00, kamar daga zama taji sallamar sadik dan ta tabbatar wannan muryar tasace take taji farinciki y mamaye zuciyarta, amsa sallamar tai tare da tasowa ta fito, tana dago labule suka hada ido da sauri ta karasa ta rungumi shi tana mai tsananin nuna farin cikinta sabida ganinshi,kayan hannanusa ta karba tanai mishi sannu d zuwa,hannunsa yasa y tallafo daidai kugunta suka jera daki, suna shiga wani kamshine ya kawowa hancin sadik ziyara take yaji jikinsa ya mutu,lemon da tahada masa d meat pie din d tai dan tanadin zuwanshi ta kawo masa sannan taiwa kanta mazauni kusa dashi, ganin deeja tasha kwalliya y sanya sadik mantawa d maganar da sukai d ardo, bayan sun gaisa yasha lemo d meat pie ne suka fara bayyanawa kansu missin din junan da sukai,a wannan lokacin ne sadik yace dani nafiya naci duk inda yai saina biyoshi ynx d ranar ma zan musu labe d gudu y fatattakoni yace baxan dau rahoton basaidai kuyi hakuri masu bibiyata dan nima dakayar nasha d ya tisoni a dari saidana fadi na kuje guiwa. Jin sadik ya daina sumbatu deeja ta daina yan koke-koke ne yasa na tabbatar komai ya kammala tsakaninsu, cikin sanda nai sadaf-sada nakoma na rakabe dan nacigaba d gashi suya sai ranar sallah ,deeja na hango tana kwance a kan kirjin sadik tana bacci shima baccin yake yi, aikuwa ba inda zan matsa n samu guri n zauna ina jiran su tashi dan ci gaba da gashi. Bayan sallahr azahar ne sadik badan y soba yaiwa deeja sallama dan komawa birni,deeja rasa abinda yake mata dadi tai dan jin sadik yau zai tafi, haka sukai sallama ba yabo ba fallasa a fuskarta,ya damka mata sabuwar wayar nokia Dan su dinga gaisawa, deeja tayi murna d kyautar wayar dya Mata,gidan ardo ya nufa shima yai masa sallama, nan ardo ya kara jaddamasa bukatarsa ta neman daki, gidan su nasiru ya ratse suka gaisa tare da yimasa godiyar isar masa d sakonsa,sannan ya nufi tashar mota. Karfe 4:10pm sadik ya sauka a garin kaduna, gidansu salele ya fara zuwa dan kaimasa ajiyar wayar daya karba, salele ne kecewa har kadawo d wuri haka hararara sadik ya doka masa yace hakane wuri?4:30 takusafa kaga natafi inbaso kake hajiya ta gane ba, dariya salele yai yace angaida MIJIN HAJIA saboda tsabar haushi sadik bai tanka masaba ya juya yanufi gidan iko wato gidan hajiya. Agogon dake makale a dakin hajiya ta kalla karfe 4:30pm amma ba alamar sadik, sakawa da kuncewa tashigayi a zuciyarta tana cewa wannan wana irin escortion ne tin 8:30am har gashi 4:30pm tayi? wata zuciyar ke fada mata anya kuwa ba kauye sadik ya tafiba yau fa asabar ba wani raka dalibai? ajiyar zuciya tai tace lallai kuwa idan hakane zan ci zarafin sadik, zandau kwakkwaran mataki akansa, tana kaiwa nan yai sallama. Ayushailiasu.blogspot.com

No comments:

Post a Comment