Saturday, 5 November 2016
[5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. …………Story:-Hawwa Saleh. 111-115 Tin dawowar sadik daga kauye tsanani y kara yawaita a tsakaninsa da hajiya saboda ta fuskanci sadik akwai abinda yake boye mata dan haka ta kara takura masa gami d sakar masa duukan ragamar aikin gidan,dan a halin yanzu sadik shike dukkan wani aiki kama dg shara,moppin, wanke-wanke,girki, harma da wanki duk saiya y kammalasu ya wankewa hajiya mota sannan yai shirin tafia makaranta, komai makarar da xaiyi saiya tabbatar d yagama sannan ya tafi. A halin yanxu sadik baya samun saken zuwa kauye saidai yai satar hanya a ranakun makaranta ya dau excuse gurin principal yaje batare d hajiya tasani ba, duk d wannan dabarar da sadik keyi saida hajiya tasha jinin jikinta sabida tasaba karfe 2:00 sadik kedawowa gida yanxu kuwa saiya yakai 3:00 ko 3:30 baidawo b idan ta tsareshi da tambayer meya zaunar dashi sai yaita kame kame da soki burutsu, ganin hakane ya sanya hajiya ta baza C.ID din d zasu ringa bibiyarsa batare d sadik y saniba, dama ai shi ramin karya kurarrene. A yau ne deeja ta cika wata hudu a gidan mijinta, d safiyar wannan ranar ne tana sharar tsakar gida ciwon ciki ya turniketa sharar d bata karasaba kenan, dakyar ta iya jan jiki zuwa daki, murkususu take famanyi sabida axabar ciwon dake cinta, wayar d sadik y bata ta lalibo ta kira lambar sadik amma a kashe gashi gida ita kadai,haka taita faman juyi a tsakar daki har kusan shabiyu na rana tarasa yadda zatai,tana cikin wannan hali Allah ya jefo d kanwarta harira antasosu daga makarantar allo, sallama tai jin baa amsa mata bane yasanyata hanzarin karasawa dakin, tana daga labule ta hango deeja yashe a kasa tagama galabaita ciwo ya gama cinta, ninfashinta dake kaiwa da komowa ne yasanya harira rudewa ta juya d gudu tai gidansu. Cikin dimuwa harira ta fada gida ko sallama babu tana kuka tana kiran inna! inna!!, dasauri inna ta fito daga daki danjin irin wannan kira ba lafiya ba, tambayarta take harira meyafaru? amma fadi take Zata mutu inna, zata mutu wllh tsuwace ta kauracewa inna ta jijjiga harira tace wace zata mutu? kofar fita harira take nunawa inna tana cewa deejace deejace……… subhanallah inna take fadi ta shiga daki ta dakko mayafinta tai waje. Tafiya inna take cikin sauri kamar zata fadi dan batasan inda take jefa kafarta ta mayarba ta nufi gidan deeja, tana shiga taga halin d deeja take ciki tagama galabaita, sallallami tashigayi tana ambaton sunan Allah,juyawa tai ta nufi gidan ardo ta sanar dashi halin d deeja take ciki, rudewa ardo yai ya nufi titi dan taro mota,sannan inna ta juya ta koma gun deeja,idon inna ba abinda yake banda zubar da hawaye saboda tausayin deeja,dan ita ta gama fiddarai d deeja mawuyacine tai rai, ganin idon deeja ya fara kafewa ne ya sanya inna rushewa d kukalokacin ardo yai sallama gami dacewa kumaza kufito g mota mutafi asibiti, dakyar inna ta iya takaikayo deeja zuwa motar sabida duk jikinta ya saki ta kara nauyi,direct babban asibitin garin suka nufa da deeja. Suna isa asibitin likita yai umarni d aimaza a kaita deeja emergency room sabida ganin halin da take ciki,lokacin d aka shiga d deeja dakin taimakon gaggawane muma mukai d'uuuuuu zamushiga, juyowa likita yai ya dakatar damu ta hanyar cewa anan xaku jira baa shiga dakin,nan mukai curko curko a tsaye muka xubawa sarautar Allah ido,muna jiran tsammanin marabbuka malam yaki noma dan zakka,daidai lokacin na kara saita birona bisa littafina ina jira azo ace abu kazane yasami deeja na nado muku rahoto amma shuru matakau kakeji ba likita ba alamarsa kamar an aiki bawa garinsu dan innama tagaji da safa da marwar d takeyi ta zauna ta zabga takugi ba abinda take a zuciyarta sai adduar nemawa yarta lafiya. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 116-120 DEDICATED TO UMMAKULSUM( MUM APIPA) FIRST CLASS GROUP Likita ne ya fito da gudu inna ta tashi ta karasa gareshi, tambayarsa take jikin deeja yace mata dasauki tasamu bacci, umartarta yai da tabiyoshi zuwa dakin,kafin ya fadamata abinda yake damun deeja ta kagu ta tambayeshi likita meyasameta? nan yake tambayarta tana da aurene, tace eh, yace to gaskiya matsanancin ciwon marane yake damunta dan haka koda yaushe mijinta ya ringa kasancewa da ita inba hakaba duk randa yakuma tashi zata iya rasa ranta sbd yanzuma da kyar suka shawo kan ciwon saboda yaci karfinta, cikin mamaki inna ta ke amsawa likita da insha Allah zaa kiyaye mijin natane ba mazauniba shiyasa, nan likitan yace to gaskiya yatafi da ita shine kawai mafita sannan ya mika mata katin magungunan gami d cewa idan ta tashi saiku tafi, ta karba katin taimasa godiya. Ahalin yanzu principal ya gaji d baiwa sadik permission koda yaushe, dan haka abin duniya duk ya isheshi ga hajiya itama ta kafa ta tsare, dan haka sadik idan antashi dg makaranta yake zagayawa kauye yai maxa ya dawo batare da wani abu ya shiga takaninsa da deejaba sai dan kawai gudun fadan ardo, ganin sadik baya dawowa sai 6:00 ne yasa hajiya tasa driver ya dinga zuwa yana dakkoshi da zarar antashi wataran ma sai driver ya tsaya antashesu, "dandan dandan dandan ga akuya ga kura" Jin jawabin likita d innatai ne yakara daga mata hankali bayan sun koma gidane take sanarwa da ardo abinda likita yace takara da cewa in hakane wannan auran na deeja bai kara musu komaiba sai janyowa yarsu ciwo har anacewa zata rasa ranta,jikin ardone yai sanyi yashiga bata hakuri d cewa bazaai hakaba insha Allah zai daumataki zai aikawa sadik yaxo yatafi da matarsa,inna tace to shikenan,sallama sukai d inna yatafi, dg nan bai zame ko inaba sai gidansu nasiru akace bayanan yaje kasuwa,sallahu y bayar da cewa inya dawo ace yana nemansa dan Allah. Bayan sallahr laasar nasiru y dawo gida ko zama baiba aka fada masa ardo yazo nemansa dan haka ya fasa zsma ya juya yanufi gidan ardo, yana isa sukai kachibis dashi yafito dg cikin gida, gaisawa sukai ardo yake fadamasa dama zuwa yai ya kiramasa sadik zasuyi magana, nan nasiru ya kira wayar sadik a kashe,jin akashe takene yasa ardo jikinsa ya kara sanyi yaimasa godiya yatafi, tinda ardo y shiga gida baisake futowaba saidayaji kiran sallahr magriba ba abinda yake sai xulumi d tunanin sadik wane irin abu yakeyi a birni da kullin wayarsa a kashe, kardai sadik wata harkar daban yakeyi ba koyarwaba a birni, hakadai yaita tintintini. Alhmdllh deeja tadan samu sauki dan inna bata bari anmaidata dakintaba gidanta tatafi da ita dan tafi samun kula,acewarta koda wani abunne zai kuma samunta gara tana gaban idonta tinda can gidanta tazama yar gadinsa. Tsohon wannan dare sadik kasa bacci yai jikinsa na bashi wani abu yafaru a kauye, da sassafe yai shirim tafiya makaranta ko breakfast baiba balle ya sanarwa da hajiya yatafi dan bacci take, haka yasa kansa yai waje batare dayayi aikace aikacen gidan da yasababa, gidansu salele ya nufa yakarbi wayarsa yana budewa ya lalibi lambar nasiru ya kira, ringin biyu nasiru ya dauka, sungaisa kafin nasiru yagayamasa ardo na nemansa sadik yace dan Allah ya kaiwa ardo wayar zasuyi magana ya amsa masa d nan da minti biyar yakara kira, cikin hanzari nasiru ya kaiwa ardo wayar, jim kadan sadik ya sake kira nan ardo ya fadashi da fada yaimasa kaca kaca tare da zayyanamasa abinda likita yace km ya umarceshi karya sake makonnan ya cinye baixoba kuma ya tabbatar ya nemi dakin dazaisa deeja a birni inba hakaba zaihanashi aikin dayakeyi, shuru yai yana sauraron mahaifin nasa ya gaza cewa uffan saida ya tabbatar ya gama maganarsa ya bude baki zaiyi magana yaji ankashe wayar saboda ardo baya bukatar jin abinda zaice umarni ya bashi aceawarsa,nan y mikawa nasiru wayarsa gami d godiya ya shige gida sabida ransa ya baci sosai. Sadik kiran wayar yakarayi amma maimakon yaji muryar ardo saiyaji nasirune ya tambayeshi ardo yace yashiga gida, nan nasiru ya karamasa nasihohi sabida yaji akan abinda ardo yake fada godiya sadik yaiwa nasiru cikin sanyin jiki ya kashe wayar. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 121-125 DEDICATED TO BINTA SALEH ( MAMAN AYSHA )FIRSTCLASS GROUP Asanyaye sadik y karasa makaranta jiki ba kwari yaje yai signin a staff room ya shiga ya zauna jiki lakwas tinani yashiga zabgawa akan maganar baffansa ta ina zaifara? ya zaai ya kunce kullin bakin wannan buhun?idan har yazo d deeja garinnan ya zaiyi?ya zai yi ya dinga kwana a gurinta? idan hajiya taji wannan labarin wane hukunci zatai masa? Idan ardo yaji labarin sa na auren hajiya wane mataki zai yanke masa? Kodai sakin deeja zanyi ne nahuta? Aikuma ina sonta baxan iya sakinta ba, wata zuciyar tace masa towai kai kasaki hajiyan man ko kagudu ka barta tinda batasan garinkuba? tabb hajiy ai itace rayuwata bazan iya sakinta ba amsar d wata zuciyae tabashi kenan, "kwadayi mabudin wahala su sadik baa sadudaba ashe" tambayoyi dai barkatai zuciyarsa taita jero masa wadda ya tabbatar da baida amsoshinsu, can wata zuciyar tace kawai ka amince ka taho da deeja,to idan nataho d ita ya xanyi da bukatarta? to basaika ringa zagawa d ranaba, wata xuciyar tace idan hajiya tabarka ba, kadai san kai MIJIN HAJIA ne, yana kaiwanan a tunaninsa sai kwalla zarrr ta biyo kuncinsa. Haka sadik yaita tufka d warwara idan wannan zuciyar ta tufka masa sai dayar ta zago ta warwaremasa yarasa abinda yake masa dadi,kasa tabuka komai yai a wannan ranar shikuwa salele tinda ya shigo makaranta bai zauna a staff room b balle yasan halin d sadik keciki. Kamar ancewa sadik miki ka kalli window yai ido hudu da motar hajiya ta kunno kai cikin makaranta, direct office din principal ta nufa, sun gaisa d principal cikin girmamawa take cewa dan Allah zuwatai ta daukarwa sadik permission wata tafiyace ta taso cikin gaggawa zasuje, nan principal ya bata dama sukai sallama taimasa godiya, shiko sadik jikine yadau kyarma meyakawo hajiya makarantarsu? Baisamo amsarba yaganta kmr wadda aka jefota cikin staff room din, suna hada ido ta dokamsa harara cikin kaushin murya tace ka kyauta daka fito ka barmin gida kaca kaca bakai abinda d yazamema wajibiba, wuce kashige mutafi ka gyaramin gidana tana nuna masa kofa da hannunta, "Oh ni 'yatasua yau su hajiya d angonta ba harkar murmusawa juna a gaba ta tisashi har gaban mota gami da umartarsa yai driving, ita km tashige baya ta hakince,HHHHHHH su sadik yau anzama driver,lallai yau sadik angama cika MIJIN HAJIA,driving yakeyi kawai batare d hankalinsa n jikinsa ba abu goma da ashirn ya hade masa baffa ya hadamasa zafi ga hajiya t kunno masa wuta mai huci. Kyal kyal kyal dariya mai kafa uku rak naiwa sadik kar nima na kara ruramasa takaici. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 126-130 Da safiyar yau laraba misalin 8:30 sadik ya fito dg gidan hajiya bayan ya gama dukkan wani aiki d yasaba yi,yai wa hajiya sallama akan cewa yatafi makaranta saidai b makarantar xaijeba kauye ya nufa dan yasan inyaje makarantar principal bazai bashi permission ba dan haka yai tafiyarsa kauye kai tsaye,yana isa kofar gida ya iske ardo ya zabga uban tagumi, sallama yaimasa cikin sanyin murya ya amsa, bayan sun gaisane ardo ya ninfasa yace dafatan da shirin tafiya da matarka kazo ko? Shiru yai a zuciyarsa yana cewa ashe da gaske baffa yake nai zaton bacin raine ya sanyashi fadar haka ko rashin lafiyar deeja ce tasa………………bai karasa tinaninsa ba yai tsinkaye d muryar ardo cikin tsawa yace ba magana nake dakai ba? sadik bafa zaka maidani mutumin banxa a garinnan ba na fadama yau kafarka kafar matarka dan naga take takenka na shure maganar da nake fadamaka kuma kafata kafarka zamu tafi naga mahallin da zaka kaita, lokacin gaban sadik y kara fadin rassssss, hakuri ya dingi baiwa ardo dakyar ardo ya yadda kan yarjejeniyar ranar lahadi zaizo su tafi. Gidansu deeja ya karasa ya dubata, gani ranewar da tayine yasanya sadik ya tausaya mata danba karamar ramewa taiba saidai bai mata magana akan ramar da yaga tayiba, itama deeja ganin ramar da sadik yai ne yasanya deeja tambayarsa yataga ga rame? Ko baida lafiya ne? dariyar yake yai wadda tafi kuka ciwo yace rashinta kusa dashine ne yasanyashi rama da kuma rashin lafiyarta, tausaya masa tai gami da yimasa dadadan kalamai, sundan taba hira sannan yaimata sallama dacewa ranar lahadi zaizo sutafi, wani farin cikine ya ziyarci zuciyar deeja wanda har fuskarta saida ta bayyana irin farin cikin da takeji, murmushin kashe zuciya ta sakarwa sadik wanda shima saida ya maida mata martani tace Allah y kaimu,ya amsa da amin ya tafi. Sadik ko gidan ardo bai komaba ya nufi hanyar titi ciki d tausayin deeja sabida ganin irin farincikin da ya bayyana a fuskarta da yace zaixo sutaho ya tabbata tana cike da bukatarsa tayi kewarsa kamar yadda shima yai kewarta dan yanxu hajiya bata wadatar dashi kamar yadda deeja take masa. 1:20 daidai sadik ya sauka garin kaduna,masallacin dake kusa d gidan su salelr ya nufa yai sallahr axahar, bayan y idar ne ya kaiwa Allah kukansa ya kawo masa sauki da rangwame gami d mafita a wannan alamari da ya kunno masa ,su Sadik sai yanxu akatuno d ubangiji sannan ya fito ya nufi gidansu salele duk d yasan yanzu baidawo dg makaranta ba amma saiya zauna a kofar gidan ya na jiran dawowarsa,duniyar tinani sadik ya fada,sanda yai nisa a tinaninsa ne yaji an dafa kafadarsa yana dagowa yaga salele ne, tambayarsa salele yashigayi meyahashi zuwa makaranta yau ga driver yaxo daukarsa? Sai a lokacin sadik ya tuna da driver n xuwa daukarsa, cikin sanyin murya yace salele zauna kabani shawara yadda zanyi, wllh duk alamura sin jagulemin, salele yace meyafaru kuma? Nan sadik ya zayyanawa salele yadda sukai da ardo, jinjina kai salele yai yace sadik kayi ganganci, amma yanxu akwai wani care taker saimuje ya samoma daki mai saukin kudi,sadik yace to gami da tashi suka rankaya, sunyi saa kuwa da zuwansu ansamu dakin kan kudi naira dubu goma sha biyar, nan suka ce da maibada dakin yai musu lamuni abiya albashi zasu kawo saboda lokacin daf ake da biyan albashin, kasancewar care taker yasan salele yasa ya lamince masa, godiya sukaimasa sannan suka dunguma ya nuna musu gidan. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 131-135 C.I.D din d hajiya ta baza su ringa bibiyar sadik ne sukai sallama lokacin hajiya na zaune a palo ranta a bace, umarni taimusu sushigo, suka shigo bayan sun gaisa ne suke sanar da ita yau sunga sadik a wani kauye da safe, tambayarsu tai mai yajeyi? suka ce basu saniba amma tabbas sunganshi acan, tace sun tabbata ko yanzu zasu iyai mata jagora kauyen? Sukace eh zasu iya, godiya taimusa gami d kyautar kudi suka tafi,ran hajiya ya kuma baci matuka dajin wannan labarin ga kuma driver ya zo yafada mata yaje dakko shi a makaranta ance masa baizo ba ma kwata kwata,kudara tai ranta yau sadik saiya fada mata inda yaje da abinda yake boye mata sannan taci zarafinsa wata zuciyar kuma tace a'a bahaka zakiba a hankali cikin siyasa zaki gane komai,yadda hajiya tai d shawarar da xuciyarta ta bata. Karfe 3:00 sadik ya shigo gidan hajiya,ko kallonsa bataiba balle taimasa magana,ganin haka d sadik yai yasa yawuce sumsum yana sunkui da kai ya fada daki, kayansa ya cire gami d watsa ruwa ya fito palo, guri yanema nesa da hajiya ya zauna yace hajiyata sannu da hutawa, yawwa sannu da alamunka yau kasha aiki a makaranta tace masa tacigaba d abinda takeyi, shuru sadik yai baice komaiba dan yasan magana hajiyar ta dankara masa,sundau lokaci batare da kowa y sake maganaba sannan hajiya tace inbaxakaci abinciba ina bukatar kazo ka yanken farce,shafa keya yai yamike ya nufi dining. Sunkuye yake yana yanke mata farcen kafa tai gyaran murya tace sadik ya dago da sauri ya kalleta saboda jin tace sadik yace da wata akasa yau dan bahaka tasaba kiransa ba, cigaba tai da magana kaga yau kimanin wata takwas da aurenmu yaci ace nasan mahaifarka, iyayenka sun sanni na sansu bawai muyita zama bansansu ba, dummmm sadik yai ya tsaya cak da yankan farcen gabansa ba abunda yake sai dukan uku uku shuru yai yakasa magana,jin yai shuru ne yasa hajiya tace koba haka ba? Cikin karfin hali ya kakaro murmushi yace eh hakane, tace to inason ka shirya ranar lahadi sai muje ko,"tab akwai gwarama" jin tace lahadi ne yasanya sadik zaro ido a tsorace yace lahadi kuma hajiya? hajiya ta lura da furgicin da yashiga ta basar , dan son tagano abinda yake boye mata tace eh lahadi,yace dadai an canja wata ranar, tace ranar lahadin nakeson zuwa umarni nabaka bawai shawararka nanema ba ba dan haka inason kazama cikin shirine ma yasa na fadamaka koda abinda zakai tanadi kafin ranar dasai dai ranar lahadin nace kafito mutafi. Acan kauye kuwa farinciki ya ishi deeja da inna harma da ardo sabida tafiyar deeja birni, shirye shirye gadan gadan inna tashiga yiwa deeja don tafiya garin gwamna ranar lahadi. Bangaren sadik kuwa rudu, dimuwa, tashin hankali sune suka kaiwa zuciyarsa farmaki,yaka xaune yakasa tsaye a lallai saiya samo mafita, kwanciyar hankali da nutsuwa sunyi kaura daga gareshi. Tabbb tashin hankali balagar tsintsaye hajiya da ardo sun hadawa sadik zafi, makaranta littafin MIJIN HAJIYA ku tayani tinani anya kuwa sadik zai samo mafitar yadda zaiyi da hajiya kafin ranar lahadi? Ina sauraranku………… *INVITATION !!!* Karan katakaf kafitanin ilahirin gaba daya kwatar makaranta littafin MIJIN HAJIA, ni AYUSHA ina gayyatarku rakiya da taken baya zuwa kauye dan ku ganewa idonku yadda wannan gwarama zata kasance tsakanin sadik,hajiya,da ardo basai kunjira labari daga gareni ba gara kuga kwal uwar daka d idon ku. *………waiting………* Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 141-145 Misalin karfe 10:00 na safiyar ranar asabar sadik d hajiya na zaune a dining suna breakfast, fork da knife din dake hannun ta ta ajiye gami da daukar mug din tea ta kurba,sannan tace sadik ka shirya zamuje kasuwa domin yiwa su baffa tsaraba dagowa yai ya kalleta ta sakar masa murmushi batare daya maida mata ba yace to, ta lura da yanayin sadik ta kara cewa me da me yaka mata musiyo musu? sakin fuska yai kadan yace duk abinda aka siyo yayi,haushine ya kama hajiya tace kai nakeson ka fadaamin ai, yace ke me kikaga ya dace a sai musu? cikin fara'a hajiya tace asiyo atampha da shadda sannan a saiwa yaranka kaya d takalmi, sai kuma kayan abinci da sannan muje mall ai musu tsarabar abin tabawa ko baiba? haushine y kama sadik saidai bai nuna a fuskaba yace yayi hakan Allah ya kara budi, amin t amsa masa gami dacewa sai muje mu shirya,"niko nace yau hajiya shiri akeji da sadik". 11:30 daidai su hajiya aka fito cikin shirin tafiya kasuwa,jerowa sukai cikin takun kasaita suka nufo parking space inda motar hajiya take, mukullin dake rike a hannunta ta mikawaa sadik ya karba ya bude motar, drivers seat ta umarceshi ya zauna ita km ta zauna a kusa dashi, tada motar yai yaji hajiya nacewa habibi kasuwar zamu fara zuwa amma, to yace mata dan har lokacin fuskarsa ba walwala. Sun isa kasuwa sunyi siyayya sannan suka wuce mall, sun gama siyayyar dazasuyi sun dakko hanyar gida ne hajiya kecewa wllh nagaji habibi da mun biya nakarbo dinki na, sadik yace to mexai hana mubiya, a'a tace muwuce gida anjima sai kazo ka karbar min dan nagaji kwanciya nake sonyi "abinka da katuwar mace" sadik dan haushi ko amsa mata baiba yacigaba da tukin da yakeyi,har suka kusa karasawa gida ba wanda y kara magana tsakaninsu dan shi sadik ba abinda yake illa tinanin samun mafita kafin gobe,amma har suka je gidan ba wata dabara da tafado masa koda guda daya. Bayan sallahr azahar ne hajiya na kwance akan gadonta sadik y shigo umartarsa tai yadau mukullin motar ta yai sauri ya karbo mata dinki, ba musu ya dauka yai waje, tafiya kawai yake a cikin motar amma yagaza nutsuwa sai can wata zuciyar tace ka biya wajen salele man ka fadamasa ko zai samoma mafita,sadik baiyi kasa a guiwaba ya juya akalar mota yanufi gidansu salele, da zuwansa ya aika yaro yaimasa sallama dashi, yaron ya fito yace wai bayanan,takaici ne ya dira a zuciyar sa ya juya yashiga mota ya tayar yana tafiya a hankali, yana fita dg lungun gidan zai hau titi yahangi salele ya taho,hamdala yai yai saurin parkin ya fito,kira y kwallawa salele, jin da salele yai ankira sunansa ne yasashi juyawa sukai arangama da sadik, karasawa yai inda yai parkin yana washe baki yace da sadik lallai kaga MIJIN HAJIA tawaru ta warware maka kenan da hajiyar taka irin wannan dalleliyar mota haka, haushine ya kama sadik jin salele yace MIJIN HAJIA cikin fusata yace dallah malam wace warewa bayan dukunkunewa tai, dariya ?salele yai yace mekuma yafaru?nan sadik ya kwashe duk yadda sukai da hajiya yafadawa salele, shi kanshi salele kasa magana yai saidaga baya yace lallai kam t dukunkune, amma shawarar dazan baka yau yau da daddare kasan yadda zakai ka gudo dg gidan hajiya kazo ka kwana anan shagona dasafe sai ka tafi tinda hajiya batasan gidan nanba kuma batasan kauyen kuba balle tabika kaga dole ta hakura inyaso inka dawo kwayi wacce zakuyi kadai je kauyen, murnace ta kama sadik gami dacewa shiyasa nake sonka mutumina suka tafa, godiya sadik yaiwa salele yace saina zo din,sukai sallama. Sauri yai ya je yakarbo dinki yakawowa hajiya ransa kal da shawarar salele har Allah Allah yake dare yayi ya gudu,dinkin hajiya ta gwada gami da juyi ta kalli sadik tace ya kaganni habibi gobe, mirmishi yai yace ai zakiyi kyau tace bari kawai Allah dai ya kaimu goben yace amin. Agogo hajiya ta kalla tace habibi gaskiya nagaji d kallon nan bacci nakeji kaga 9:00pm tayi kataso mu kwanta, murmishi yai yace hajiyata gashi habibin naki yana son kallon film din yaimasa kyau ya zai kenan "Oh shiri yatashi kenan tsakanin masoya" kallon satai irin kallon masoya ido cikin ido tace to gaskiya ni kahakura mukwa.………,kafin takarasa yai kissin dinta yace hajiyata tai hakuri habibinta ya gama kallo, noke kafada tai alamar a'a lallai su hajiya a dole sai anyi acting irin na yara haka sadik yaita lallaba dakyar ta yadda saida ya rakata har daki ya kwantar da ita atsakiyar gado gami da yimata liff liff irin n yara sannan ya dawo palo yana godiya ga Allah, xama yai yacigaba da kallo saidai hankalinshi baya tare dashi, saida ya daidaici hajiya tai nisa da bacci sannan ya kashe TV din ya nufi gate ,maigadi ne yace da sadik ranka ya dade bada mota zaa fitaba ne, yace eh ba nisa inda zani shiyasa, adawo lafiya yai masa ya fito ya dau hanya sai gidan su salele. Karfa 10:00 na dare tayi salele yaga sadik shuru baixo ba har yafara tinanin ko bazai zobane sai yaji sallamar sadik ya shigo cikin shagon, shewa sukai gami d tafawa salele yace nazata baxaka zoba yace ai saida nabari tai bacci sannan na taho, shewa harda tafa hannu sukai, salele yace angaida MIJIN HAJIAni kuma sanda sukai shewa nace su sadik duniya tai dadi har ansamu damar shewa. Can kuwa hajiya baccin take tayi bata farkaba sai 12:00 na dare, ganin ba sadik ba alamarsa ne yasa tai saurin miqewa ta fito palo, wayam tagani ba sadik tashiga tinanin ina sadik y tafi, karfim hali tai tafito gurin maigadi ta tambayeshi yace mata tabbas yafita amma baudawoba, juyawa tai takoma daki tana cewa aranta dama da abinda sadik ke nufi tinda tace zasu kauye ya musa mata ta kudirce a ranta lallaifa ba fashi gobe zatasa c.i.d dinta su rakata kauyen ko tambaya ne tayi indai dan garin ne bazai buyaba, haka taita tunanini har bacci ya dauketa. Sadik kuwa kwana sukai suna zabga hira da salele dan bacci barawo kasa daukarsi yai sai chasar hira suke, sadik jinsa yake wasai dashi zuciyarsa shar da ita saidai idan ya tuna inya kawo deeja nan garin ya zai ringa kwana agunta ne sai jikinsa yai sanyi, hakadai sukaci gaba da hira har akai kiran assalatu. *YAU TAKE LAHADI………* Hausawa sunce rana bata karya saidai uwar diya taji kunya kuma rana dubu ta barawo rana daya tak tamai kaya, duk abin d akasawa rana zaizo dan haka ni AYUSHA nake cewa ina fata makaranta littafin MIJIN HAJIA sun shirya tsaf domin zuwa kauye ganewa………… dan yau take *LAHADI* ranar d xaa ware tsakanin tsaba d tsakuwa. Inkun tabbata kun shiry ku biyoni ………………… Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. …………Story:-Hawwa Saleh. 146-150 *LAST PAGE* *TO DAY IS SUNDAY* Allah ya kawomu wannan rana wadda bahaushe ke mata kirari da rana bata karya saidai uwar diya taji kunya, ranar d zaa ware zare d abawa,ranar da zaa ware tsakanin tsaba da tsakuwa,ranar da ido zai raina fata, ranar nadama da dansani,ranar tonan silili, ranar gori harda goriba,Allah y rabamu d irin wannan ranar amin. _Ina fatan makaranta littafin MIJIN HAJIA sun gama shiri dan anjima kadan zance ku biyo bayana_ Da safiyar wannan ranar ne sadik yai sallama da salele ya nufi hanyar tasha, motar d zata sadashi da mahaifarsa y hau,cikin lokaci kadan motar ta cika driver ya dau hanya,tsabar farin cikin d sadik ke ciki bazai misaltuba bai ankara ba yaga har anzo inda zai sauka,dakatar da drivern motar yai t hanyar cewa akwai mai sauka nan mota t tsaya ya sakko ya tari mashin ya hau dan ya karsa dashi ciki kauyen. _lokacin nace da makaranta littafin MIJIN HAJIA kubiyoni_ Kofar gidan ardo sadik y umarci mai mashin ya tsaya ya sauka, ya biyashi kudinsa _lokacin nima d tawagata muka karaso_, kai tsaye sadik ya shiga cikin gidansu a dakin dake bakin zaure ya iske ardo yana jan carbi kasancewar safiyace bai fito shan hantsi kan dakali ba,sallama yai masa cikin sakin fuska ardo ya amsa, jin dadin ya cika alkawarine yasa ardo yin haba haba dashi tare da umartarsa y zauna, guri sadik ya nema ya zauna suka gaisa cikin nutsuwa,ardo ne yake cewa d sadik ya hanya amma kayi sammako, sadik yace ai motar sassafe na biyo dan ina idar da sallahr asuba nai azamar tahowa,ardo yace koda najifa ai gara da ka iso da wuri dan mutafi da wuri ko madawo muma d wuri sadik yace ai shiyasa nai sammako, _nan na barsu suna hirar da da uba nace bari kuma mu leka gidan hajiya danjin yata tashi._ Misalin karfe 7:30 da rabi na safiyar wannan ranane hajiya taiwa c.id dinta waya suzo maza maza tanason ganinsu,angama hajiya sukace mata, wanka tashiga tai sannan ta shirya cikin kaya na gani nafade tsayawa baku labari ma daukar lokacine shiya nace ku taho kugani da idonku, dining ta nufa tai breakfast sannan ta dawo palo ta hakince tana jiran karasowar su, jin shirun da hajiya tai ne yasa ta kara kiran wayarsu suka sanar da ita suna hanya,tace sai sun karaso,10:15 daidai suka karaso cikin gidantsayawar motarsu d hajiya taji ne yasanyata yin ajiyar zuciya, sallama sukai tai musu izini d sushigo, bayan sun gaisane take fada musu cewa kauyen d sukaga sadik zasu kaita, batare d bata lokaciba suka amsa mata dacewa angama hajiya muna saurarom fitowarki a waje,yawwa tace musu suka mike sukai waje. Acan kauye kuwa labari ya zaga gari cewa yau deeja zata tafi birni, kowa sha'awa yake inama yarsace dansu zuwa birnima wahala yakewa mutanen kauyen,dan haka mutan kauyen suma sukace sai sunwa deeja rakiya har titin daxasu hau mota, bangaren deeja kuwa murna bazata misaltuba lokacin da sadik ya karasa gidansu dan sanar mata ta shirya ya karaso dan da wuri yakeson sutafi dan su baffa sudawo suma da wuri,sallama sukai tashige gida dan shiryawa,cikin murna take fadawa inna cewar su shirya sadik yazo yace kuma d wuri zasu tafi, farin ciki d murna inna takeyi hatta kanwar deeja murna takeyi yar uwarta zata tafi birni. Karfe 11:00 hajiya ta fito parkin space din gidanta har lokacin c. id din suna tsaye suna jiran ta, daya dg cikinsu ta mikawa key din motarta tace yai driving dinsu sukuma sauran su wuce gaba suna binsu a baya, haka akai kuwa b bata lokaci suka dau hanyar kauyen. Can kauye kuwa shiri y kammala t kowane bangare, inda aka fito d kayyakin deeja yan rakiya zuwa bakin titi kowa y dauka, dungumawa sikai suka nufi titi gaba dayanasu suna tafiya rafrafraf sina hira nan danan sai gani mukai mun kusa d titi, wata dalleliyar motace t kunno kai da wata n biye da ita saurin matsawa mukai dan kamar zasu bigemu muke gani,ganin motar dake biye a bayan dayar ne y sanya sadik yin saroro danya shaida motar sarai t hajiyace. Hajiyace ke cewa matukin motar y tsaya su tambayi wadannan mutanen tun kafin suyi nisa cikin kauyen, batare d ya musa mataba yai parkin gami d fitowa, inda tini daya motar tayi gaba, ganin motar hajiya ta tsaya ne yasa sadik kara daga kafa yana sauri, mutumin d yafito dg motar ne yatsai d wani saurayi yace d dan Allah malam ina tambaya, saurayin ya tsaya yace Allah isa nasani, yace masa dan Allah yasan wani sadik a kauyen nan sunan mahaifinaa ardo? "faduwace tazo daidai d zama ashe nasiru ake tambaya", nasiru y ce eh yasanshi gashi can ma kunyi sa'a dan birni yanzu zasu tafi da matarsa shine zamu rakasu titi,lokacin d mutumin y juya yake fadawa hajiya abinda nasiru yace masa ne nasiru ya kwallawa sadik kira, chak sadik ya tsaya batare d ya juyoba,hajiyace ta zaro ido tace what?,gami d fitowa daga cikin motar, ganin sadik ya tsaya kamar wanda aka kafene yasa ardo dake biye dashi cewa ya naga katsaya?ko ka manta wani abune?shidai sadik har lokacin bai motsaba bai kumayi magana ba,muna yan rakiya tsayawa mukai mukai chirko chirko ganin mai gayya mai aiki jagaban tafiya shima ya tsaya. Takowa hajiya tai d kafarta har inda sadik yake, gabansa ta tara ta tsaya shikuwa ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa dogoshi,can gefe guda innace d deeja a tsaye, daya barin kuwa ardone shima y kama kugu inda mukuma yan rakiya muka zagayesu. Dandan dandan dandan ga akuya ga kura,yau ake yinta g sadik, deeja, ardo, inna da yan rakiya, nikuwa nace wannan shine ana dara ga dare yayi, can ardo dake gefe abin nabashi mamaki ne ya karaso yace baiwar Allah meke faruwa na? Har lokacin sadik ya kasa motsi kamar wanda aka dasa, lokacin d hajiya ta dafa kafadar sadik ne gaba daya kallo ya koma sama yau g shaho ya dau giwa,tana cewa sadik ka munafimce ni, ka cuceni ka ha'inceni, sadik ashe kai butulune macuci azzalum……………bata karasa ba inna ta karaso tace ke baiwar Allah yazaki zo kina wannan maganganu na batanci a bainar jama'a , daga mata hannu hajiya tai cikin kaushin murya tace ke rufemin baki anata d'an marayan zaki wayake ta d'an gwani kakkausa, tsit inna tai hajiya taci gaba dacewa kinsan abin da ke tsakaninmu d shi ne da zaki tsomon baki, har lokacin sadik baice kala ba bai kuma dago ba kansa na sunkuye tabbacin munafikine,hajia taci gaba dacewa dama tinda naga take takenka nasan kai munafikine, cin zarafi da wulakanci, tonon silili da gori b wanda hajiya bataiwa sadik a bainar jama'a ba,saida ta zayyane musu kaf abinda yafaru tindaga aurensu har zuwa yanzu, mamakine ya kama mutanen gurin kowa yana Allah wadai d son abin duniya irin na sadiki,shiko gogan naka ba abinda yakeyi sai kuka shabe shabe, nadama da danasanin aure hajiya yake kawai a ransa, dan takaici ardo kasa magana yai tinda hajiya tafara magana saida takai aya sanna ya ninfasa yace da sadik banida abin cemaka sai godiya,nayi nadamar haihuwar ka sabida bata amfanan komaiba sai bakin ciki, gashi ka janyo min tijara da cin zarafi a abainar jama'a amma banma bakiba n barka da hakkin wannan cin mutuncin da kajowon dan bakai akaiwa ba ni akaiwa da zan zauna agari ni mutane zasuita zindena suna nunani duk inda na zaga ana cewa ga wanda dansa ya janyomasa tijara da bankada sabida yaje birni yai auren da ake kira MIJIN HAJIA,nagode kwarai ardo yana kaiwa nan ya juya ya nufi hanyar gidansa cikin kunar zuciya. Allah wadaran son abin duniya da son xuciya mutanen gurin suka dingayiwa sadik ihu d dankira afili,sanan hajiya tace kuma kai gaggawar sakina gami d dungure masa kai tace kwadayayye ta juya ta tafi, gani hajiya ta tafine nima nace da yan rakiyata suzo mutafi,muna tafiya sauran mutan kauyen suka watse suna Allah ya kara maganin mai kwadayi kenan dama ai duk wanda yahau motar kwadaya ba indazata saukeshi sai tashar wulakanci gashi kuwa anzo tashar ta sauke sadik, watswa mukai mukabar sadik a tsaye agun kamar bishiyar d aka dasa.atake agun Kuwa inna tace Aikuwa nima nan n tafi d yata, bazamu hada zuriya d irin kwadayiba abarwa jikokina abin gori a gari ,danhaka zaman ku d da deeja y Kare daga yau, inajiran K aiko mana d takardartakwadayayye . Abin duniya ya ishi Sadik, yarasa abinda ke mishi dadi, juyawa yai yana yiwa mahaifarsa kallon bankwana, saboda y kudiri aniyar bazai kara zuwa ba har abada gudun wake wake da dankira na yan kauye Gani g wane dai ya ishi wane tsoron Allah, kuma ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka,Allah karka nuna mana ranar nadama d danasani dan kayace a baya ake barinta.Manzon Allah SAW yace "mai hankali shine wanda ya wa'azantu da waninsa",Allah yasa wannan littafi yaxama wa'azi tsakanin alumma, amin. *ALHAMDULILLAH!!!* *GODIYA* Dukkan yabo d godiya sun tabbata ga ALLAH, Al-kaliqu wanda ya halicci sama d kasa batare da dogaroba, tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta baki daya wanda akai duniya da lahira danshi, akai wuta da aljanna dan masoya da makiyansa, d yabani ikon kammala wannan littafi MIJIN HAJIA,Allah y bamu ladan daidai din d mukai ya yafe mana kuarakuran d mukai acikinsa bisa tuntunben hannu d harshe.Amin. *INA ALFAHRI DAKU:-* Mahaifiyata Allah y kara miki lafiya da nisan kwana mai amfani, Mahaifina da yarigamu gidan gsky ubangiji yai masa rahma ys aljnn makoma d sauran alummar Annabi.Amin. *ABOKANAN TAFIYATA:-* 'Yan uwa najini Hafsat, Hajara, Aminatu, Asma'u d Musa,Allah y iya muku a rayuwarku. *YARA MANYAN GOBE:-* Fatima (Ihsan),Ahmad,Usman (Sudaiz),Al-ameen, Abdurrahman (Haneef) d Hajara (Ihsan),Allah yai muku albarka. *KULLIN KUNA RAINA:-* Masoyana Ummukhulsum (Mmn afeefa),Abeeda, Baseera,Deeja,Aysha (Mmn zahra),Lubabatu, da Takwarorina Aysha Iliasu Bauchi State,Aysha Iliasu Zamfara,Marubuciyar kinmin halacci wato Aysha Tsafe, Allah yabar kauna cikin aminci, Amin. *BAZAN MANTA DAKUBA:-*Aysha (Ummu Abdullah), Mmn Musaddiq d Mmn Eeman,Allah y barmu tare,Amin. *GAISUWATA A GAREKU:-* Aysha Humaira (Melody),Aysha Bawa, Aneesa Abubakar Rimi (Aneelurv), Huwailat (Mrs jee),Hawwa Jidda AKA, da sauran Online Hausa Writers. *JINJINATA GAREKI:-* 'yar uwa, kanwa kuma abokiyar shawara Hawwa Saleh,Allah ya barmu tare har aljanna,Amin. *SAKON KARSHE:-* Zuwa g masu karanta littafina nagode Allah y saka muku da Alkhr ya faranta muku a rayuwarku,Amin. *TAKU HAR KULLIN:-* Ayusha Iliasu nake cewa Tammat bi hamdillah,sai kunjini a littafi nagaba. Ayushailiasu.blogspot.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment