Saturday, 5 November 2016

[4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 11-15 Soyayya ake t garari tsakanin hajiya d angonta Sadik ,tsawan satin d sukai Sun gurji juna san ransu, hajya jinta take bazata iya rayuwa b habibintaba yayinda shi Sadik Kuwa farinciki y mmayeshi y tsinci kanshi cikin sabiwar duniya d bai taba kisima akwai irinta a doran kasa b. Duk dare sai sunfuta shakatawa sune yau suje nan cin dinner gobe sujecan suci kosuyi takeaway, Rayuwar Sadik t canja baki daya jinsa yake tamkar yafi dukkan mutanen duniya jin dadi. Ana cikin wannan hali dama watan maulidi y kusa hajiya t biya musu ita d habibinta dan suje su yi ummara habawa murna gun Sadik har goya hajiya yayi dan murna tare d zagayawa d ita cikin palour karshe y direta kan gadansu n sunna, a wannan rana Sadik y farantawa hajiya fiye d tunaninta, takara alfahari dashi zamowa miji agareta. Cikin one week suka kammala shiri suka dane jirgi dan lulawa kasa Mai tsarki, cikin jirgi tsoro dik y mmaye zuciyar Sadik jinsa yake tamkar jirgin zai fado sai hirji yakeyi yana ambaton Allah,abinka d farin shiga, fuskantar yanayin d yake ciki yasa hajiya kwantowa jikinsa tana mishi magana kasa kasa tamkar Mai rada, haba swithat ina tare d kai b abinda zai sameka, relaxed nan d yan muntuna zamu sauka, Mutanan cikin jirgin saimamaki suke ganin hajiya n shisshigewa yaro karami wanda baifi saan dancikinta b, ita Kuwa hajiya ko ajikinta, tasanyawa idanunta toka tana balla bushasha tare d warwasawa . Jirgi yayi landing inda akasanar dasu sun iso, hamdala Sadik yayi, mafarkinsa y fara zamowa gaskiya yau shine yazo birnin madina garin manxo yana da Yakinin indai yana tare d Hajiya zai xiyarci kashenshen turai ya dau alwashin zama d hajiya cikin so d kauna tare d sama mata farinciki fiye d yanda take mishi. Sunsauka a masauki, katon dakine Mai dauke d palo d toilet, wanka suka farayi sannan suka kwanta bacci dan rage gajiya d hutawa [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 15-20 A wannan tafiyar d su hajiya sukai sun kara fahintar cewa zama d masoyi b abinda ya kaishi dadi ,shikuwa Sadik yayi experiencing abubuwa d dama, dama masu kudi haka suke enjoyin rayuwa, lallai mutanan kauye Sun zama sorry, yakara kyamar talauchi d talaka ,kaji karfin hali shida arxikin yakeci amma y fara gudun talaka. Hajiya ta kashewa Sadik manyan kudade d ta bashi tsoro duk wani abu d ya bukaci tasai mishi bata nuna gazawarta . Bayan dawowarsu gida Nigeria, hajiya t Bukaci Sadik daya ajiye aikinshi, ita aganinta wahala yakesha, tinda yana tare d ita, babu abinda Zai nema ya rasa, tinani y shigayi n ganin cewa anya hakan Kura hanyace Mai bullewa, yasha matukar wahala kan Allah y taimakeshi y samu, yasha yin kwanaki batare d yaci wani abuba duk sanadiyyar rashin aikinyi, cikin fargaba yace hajiya ni aganina ai aikina bazai zamo takura gareniba tinda n rigada n saba shekara d shekaru, hajiyance t batarai tashiga yin fadace fadace, danma inasan taimakonka n rabaki d talauci d wahala shine zaka badan kasa a ido too shiknn, t nuna alamun yin fishi, hankalin Sadik yayi kololuwa wajen tashi ganin y batawa hajiya rai, kusa d ita y dawo y fara lallashinta d kalamai masu nutsar d zuciya, y fara zolayanta d kalamai dadada da suka sanyata dariya harda kyakyatawa hajiya macece dakesan agirmamata a kuma kambamata, shikuwa Sadik y lakanci abarshi dan haka yake binta yanda takeso. Rayuwar jin dadi suke gudanarwa, indai b Sadik aiki y futaba too suna tare d Hajiya,duk tafiye tafiyen d takeyi kasashen waje dan saro kaya tare suke zuwa, kafarta kafarsa, shike daukar mata jaka d sauran kayayyakin bukata,duk wani aiki n wahala d hajiyan y kamata tayi y dauke Matashi [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 20-25 Yau kimanin wata shida auren hajiya d Sadik, kullum Sadik y kwanta bacci mafarki yake d ardo, tinyana sharewa har abin y komamai jiki duk dare sai yayi. Acan kauye Kura ardo yashiga halin kunci rashin sanin takamaimai halin d dannasa yake ciki, ba abinda yafi daga Mai hankali illa yayanshi, kullun basu d zance saina mahaifinnasu, abinda yafi daga hnklin ardo shine tin tafiyar Sadik birni bai taba shafe wata biyu baizo garesu ba, amma gashi yanxu har kusan wata bakwai, jikin ardo yayi samyi addua y shigayi Allah dai yasa lafiya, kullum cikin baiwa yaran hakuri yake tare d cemusu insha Allah yana nan zuwa ya ganku. Tunani yakeyi wacce dabarar zaiyi dan hajiya t kyaleshi yaje koda kwana dayane yaje y dawo, suna kwance yai gyaran murya yace hajiyata, farincikina, abar alfaharina, guda tamkar d dubu gareni, habawa nan hajiya taji wani farinciki y mamayeta tare d washe hakora, ya kara d cewa ranki y dade inaso zanje gaida kanin baffana dazu akaimin waya baida lafiya, hajyance tace to ai b matsala yaushe kakeso muje? gabansa yajji ya fadi, y kara d cewa ai ina tunanin b sai kinjeba tinda kinada abubuwan yi d yawa, ba wani dadewa zanyiba kwana biyu kawai zanyi, hajiyance tace habibina yanxu kana tunanin zan iya yini batare d Kai gefenaba balle kwana har biyu,inma mafarki kakeyi to ka farka hakan b mai yiwuwa bace, ai bazan iyaba sai ciwo y sameni, kaka tsara kaka, ya kara d cewa To shiknn zanyi kwana daya sai n dawo, hajya tace aa kafata kafarka, shiru yai yana tunanin ai bama zai taba yiwuwa yatafi d Hajiya, balle har y gabatar d ita g ardo matsayin mata, abune wanda ba Mai yiwuwa bane, inbaso yake ardo y tsine Mishi b, yace har yakai yayi aure b tare d saninsuba,da kyar y shawo kan hajiya t abari nan gaba saje tare amma yanxu zaije ayini daya y dawo, nanne fa hankalin hajiya y dan kwanta tare d murmushi a fuskarta ,bata kawo komai azuciyartaba, tace yawwa habibina har hankalina y kwanta, sai K musu tsaraba kace injini kannazo gaidasu har gida, yake yayi tare d cewa angama ranki shi dade, dubu ashirin t bashi tace yai musu tsaraba, dubu goma kuma y rike saboda halin hanya [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 26-30 D sassafe y tashi, dokin san y je yaga yayanshi d mahaifinshi, baccin safiya ma ayau gagarar shiyayi har hajiya t gane irin farincikin d yake ciki tamkar wanda yai shekaru baije ba, misalin karfe goma yaiwa hajiya sallama Dan tafiya, sai hajiya tace habibina kodai nataso mutafi banasan kayi nesa dani zanshiga tunanin,yace ai mungama magana tinjiya hajiyata tace to ko da direba zaku tafi dan hankalina zaifi nutsuwa,cikin dabara y karaso kusa d ita yana cewa haba hajiyata kikwantar d hankalinki indai nine Sadik namiki alkawarin nakine kedai har abada, dadine y kara lullube hajiya, kiss tamishi a kunci sannan tace safe journey. Fitar shikeda wuya kasuwa y shiga dan sayawa mahaifinnasa shadda hade t takalmi d turare, d turmin zani guda biyu dan adinkawa yayansa takalma d yari d dankunne saboda gabatowar karamar sallah, y hada d yan tsince tsincen d zai rarrabawa yan uwa, tsarabar da bai taba yi ba tim zuwansa burni, atasha y kara musu d biredi d kuma gugguru( popcorn). Mota ta daga misalin karfe daya ya isa mahaifarshi, wani dadi yaji hade d farinciki tamkar wanda ke dauke d kayan nauyi axuciya aka saukemai, ,ardo yayi farinciki d ganin dannasa saboda farinciki har kwalla yayi tare d cewa yanxu Sadik abinda kayiwa yaranka ka kyauta katafi tsawan wani lokaci b aike b zuwa, aikoba komai ganinka ko aiken gaisuwa zai sanya hankalinmu y kwanta,a halin yanxu tsufa y kamani yaci ace kana waiwayo gida,inba mutuwa akwai larura kosokake sai ance n mutu zakazo, ardo cikin goge kwallar Data kara zubo masa y kara d cewa duk laifina dana bari katafi batare d nasamarma iyali anan ba, da kanada iyali dole K dinga waiwayomu, Sadik ya shiga bawa ardo hakuri tare d karyar cewa yayi ciwone wanda y kaishi harda kwanciyar asibiti,n tsawan lokaci shiyasa baizoba ,y baiwa ardo hakuri, tare d alkawarin insha Allah hakan bazai kara faruwaba, duk cikin yayan ardo yafi ji d Sadik kasancewarshi y rabu d mahaifiyar Sadik din tin yana kankani, Sadik y sha wuya gun Matar ardo hinde kanya girma, duk cikin yayan ardo Sadik yafi mishi biyayya shiyasa yake kewar dannasa, ardone ya aika cikin gida akira Mishi yaran Sadik, suna futowa sukai ido biyu d abbansu habawa d gudu suka karaso wajen d yake zaune suka haye kanshi suna murna d farinciki, uba d yaya sai allah ,shima murnar y shigayi ganin yaran Sun fara girma, mita suka shiga yimasa abba ka tafi K barmu, dan Allah abba inzaka tafi zamu bika, shiru kawai yayimusu, tare d tanbayarsu bayan rabuwa, duk suka gaya mishi irin azabar d matar ardo ke musu, kuma ardon baida bakin d zaimata magana, ya shiga gida Sun gaisa d matar ardo, b laifi t amsa b yabo b fallasa sabanin d dabata amsa gaisuwarshi, gaskiyar bahaushe d yake cewa kowa y bar gida ...........,duk d irin daular d Sadik yake ciki sai yaga zama d iyaye, yaya da yanuwa b abinda yafishi dadi Ayushailiasu.blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 31-35 Sun zauna suna hira d ardo nan yake sanar d ardo cewa ayau zai juya yatafi, abin y daurewa Ardo kai, gyaran murya ardo din yayi yace sadiku sai kace Wanda ake kora, duk d tsawan lokacin daka dauka bakazoba shine zakace haka, kasa yayi d kai yana cewa walhi ardo aiyukane sunmin yawa, dayake yanxu anmaidani babbar sakandari ta maza bakamar d, danake a firamare ba, Ardo yace too b laifi Allah y kara daukaka, ya dauko tsarabar daya kawo ya bawa ardo tasa tare Data yaranshi, yabawa matar ardo hinde mayafi, malam yayi farinciki d wannan tsaraba tare d yiwa dannasa Adduar samun nasara a rayuwa. Ardo ke tanbayar Sadik tinda ayanxu kana d jinjinar sanaa yakamata ace ka ajiye iyali, gabansa ne y fadi daya tuno d Hajiya, cikin in ina ta mara gaskiya yace e e e ardo in insha Allah zan yi kokarin n nemo innakoma, dariya ardo yayi irinta manya yace Sadik agida nan kauye nakeso ka zabi yar uwarka bafulatana konina zabarma kamar wancan karan, gumine y fara tsattsafowa Sadik jin ardo yace zai zabar mishi mata,y shiga uku dan inhakan t tabbata baisan wana hukunci hajiyan zata yanke mishi dawana idan zai kalli hajiya yace mata zai kara aure, kaka tsara kaka dinfa kenan. Lokaci daya yaji cikinsa y kurda, yana d bukatar zagawa amma haka y daure suka ci gaba d magana Shirun dayai ne ya sa ardo cewa too tinda yau zaka koma b batun kazaba, Da zaka kwana zuwa gobe kasuwar garinnan zataci saika zaba cikin yammatan garinnan anma yanxu na dau nauyin zabama, zannema ma yarinya Mai hankali d nutsuwa, Allah yaima albarka ,abinda nakeso dakai nan d karamar sallah ya zamo katanadi duk wani abuna bukata dan gudanar d auren,zan tura komai d ake bukata kafin zuwanka, godiya y shiga yiwa ardo, badan xuciyarshi tayi na am d hukuncin ardon ba Y zaga gidajen yanuwa d abokan arziki, karshe yayima ardo sallama ya dauko hanyar dawowa kaduna cikin kasala d rashin walwala sabanin yanda ya tafi, misalin shida y isa gidan hajiyarsa, a bangaren hajiya wunin ranar cikin rashin walwala tayi n kewar habibinta, jitake dama tabishi sunje tare, jitake tamkar bazai dawoba, jin sallamar shiyasa tai ajiyar zuciya, tare d amsamushi, oyoyo habibina tashiga fada, welcm back. Ayushailiasu.Blogspot. Com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 36-40 DEDICATED TO ABEEDA (HUMAIRA B NOVEL GROUP) Hajiya tayi murna d dawowar Sadik Matuka jitake tamkar ta goye shi dan murna, tataimaka mishi y rage kayan jikinshi ya fada toilet danyin wanka y rage gajiya. Sadik y shiga halin damuwa, tunani yakeyi n makomatshi inhar hajiya taji abinda ardo ke shirin kullawa babban tashin hnklinshi d hajiyan batasan hayar iyaye yayi aka daura musu aure ,abin duniya y taru yayi mishi yawa, yarasa mafita gashi tinda y auri hajiya y rabu d dukkan abokanshi shi a ganinsa wai yafi karfin ajinsu ayanzu kinga d ko shawararsu y nema dansamun mafita. Karshe ya yanke shawarar sanar wada hajiya danta samar Mai mafita, wata zuciyar ke gargadinsa Sadik K rufawa kanka asiri inbaso kake hajiya taci zarafinkaba, yanda take jida kai ,aibazata so taga wata mace ta rabeka ba. Sadik y shiga damuwa matuka, y shiga yawan tunanin d yasanya hajiya t gano yana cikin matsala, tanbayarshi ta shigayi habibina lfy KuWA, naga tinda kaje qauye ka dawo baka cikin nutsuwa, koduk rashin lafiyar baffannaka ne ya sa haka,yake yayi tare d cewa ko daya wallahi hajiyata, kamar y gaya Mata saikuma y waske yace wallahi ardone yace lallai yanada bukatar wasu kudade daga gareni zai siya wata gona nikuma a yanxu b kudi hannuna, murmushi tayi tare d cewa haba habibi dan wannan yar matsala kankanuwa saika nemi hanamu kwanciyat hankali, nawa ardon keda bukata? Yace dubu dari biyune ba yawa, hajiyance tace ai kafi karfin komai agurina kofin haka ardo y tanbaya ni Mai iya badawane duk sanadiyyar kaunarka Da nake ka futar damuwa a ranka duk randa K shirya zuwa K sanar dani sainabaka saboda murna baisan lokacin d ya yi hugging dinta, soyayi y dagata yayi juyi d ita cikin palon amma kasancewarta lukuta ya kasa koda dagata, yayi yayi amma ina, y gagara abinka d dan santolo l Ayushailiasu.Blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 41-45 DEDICATED TO MARIYA AHMAD ILIASU Tindaga wannan rana sadik y rage nuna damuwar d yake ciki gaban hajiya, gefe daya yana murnar kyautar kudin d hajiyat zata bashi, tin tsawan rayuwarshi bai taba rikesu a dunkule lokaci gudaba. Yagamayin budget din yanda zai sarrafa kudin, dama akwai yan kudade a hannunshi, zai hade su yayi hidimar biki sannnan kuma y kara gyare dakin d marigayyiya tsohuwar matarshi tazauna ciki dan amaryar t zauna, dan bazai taba zuwa d ita burniba balle asirinsa y tono agun hajiyarshi Akwana atashi b wuya bangaren hajiya jinta take tafi kowacce mace saa a duniya tinda ta mallaki santalelan saurayi sankowa kin WAnda y rasa, burin hajiya ace yau t samu ciki,t haifi diya macen da zatayo mahaifinta. yau ne akatashi d azumin watan ramadan, kuma sadik yanasane d cewa ardo yace ana sallacewa zai mishi aure, ranar d azumi y kai shabiyar y Sanar d Hajiya cewa zaije yiwa su ardo sannu d shan ruwa, ta hada mishi goma shatara t arziki, buhun shinkafa dana gero d sikari d wake d Mai da turmin xani d shadda yakaiwa su ardo, tsoro kayan suka baiwa Sadik yace hajiya ai sunyi yawa, amma sai cewa tayi kafi gaban haka gareni, dukiyata duka zan iya salwantarwa dan samarma farinciki, hade d jimillar kudi dubu dari biyu, kasuwa yafara zuwa y hada lefe daidai gwargwado irinna mutan kauye, tare d yin tsaraba, tasha y nufa, yai sa a saura mutum daya mota t cika yana shiga mota t daga sai mahaifarsa.ardo d yaranshi sunyi farinciki d zuwan Sadik din. Ayushailiasu.Blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 46-50 DEDICATED TO MRS JEE (Allah y kawo Baby muzo musha suna Cikin sakin fuska d nuna tsantsar farincikiy ya tarbi dannasa, tare d tambayarshi aiki d abokan zamanshi, Sadik yace duk suna lfy,sunmace agaisheku. Y gabatarwada ardo dukkannin kayan d y hado n hidimar auren tare d kaiwar d Hajiya t bawa yakai injita, amma sai yace d ardo awajen aiki aka rabamusu kayan abinci n azumi, ardo sai godiya yake, y kasa rufe bakisaboda murna, a hsashen d yake akalla kayan abinci zasukai mishi wata shida kofiye d haka. Bayan y dan huta ardo ke sanar dashi matar d ya zaba Mai, shiru Sadik yayi tare d sunkuyar d kai nuna alamun biyayya, fargabarshi Allah dai yasa b adangi ardo ya saboo mishi matarba gudun tonan asirinsa, ardo y cigaba d cewa b wata bace illa deeja kanwarka yar wajen kanwar mahaifiyarka, gabanshine yai muguwar faduwa, bai so haka, amma bashida zabi saina amincewa, tare d kara yiwa ardo godiya. Kamar yanda ardo y tsara ankai kayan lefe d sauran kayayyaki n bidiar auren fillo, ansa biki sati uku masu zuwa, ardo y barwa sallahun jigilar d dawainiyar gyaran gurin d amarya zata tare. Yaje ya ga deeje ,b laifi yarinya ce kankanuwa wadda batafi shekara 15 ba, amma kyakkyawar gaske, idanuwanta su sukafi daukan hankalin Mai kallonta kasancewarsu dara dara kuma sexy, sai pointed noise d dankaramin bakinta, kirjinta cike yake Da dukiyarsu t fillo, doguwace, gata d shiru shiru, magana ma bata dameta ba, ba laifi y yaba d ita, amma hankalinsa n kan hajiya Da irin wadaka datake ,d ace babu auren hajiya kansa, yasan zaiji dadin zama d deeje kasancewarta Mai tarbiya d kawaici. Ya tanbayeta irin abubuwan d take bukata n game d aurennasu, kunya t hanata cewa kanxil, kuji yarinya Mai tarbiyya " sabanin yammatan wannan zamani wanda kan saurayi y fara tambayarsu abinda suke bukata su yi masa dogon lissafi " Ganin bata d niyyar cewa komai yasa y bata daidai karfinsa , yaimata sallama kancewa gobe zai koma birni kan bakin aikinshi. Ayushailiasu.Blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 51-55 DEDICATED To AYSHA BAWA Sunyi kwanan hira d ardo, inda y dinga bawa ardo labarai n mutanan burni d irin zamantakewar rayuwarsu, ardo Kuwa jiyake d Da hali d zai fiso Sadik yabaro birni y dawo kauye su cigaba d rayuwarsu, saboda yanajin dadin zama d dannasa, amma yasan hakan b abubane Mai yiwuwaba. Sadik y sanardashi gobe zaikoma saboda yawan ayyukan d ya baro. Washegari yazaga gidajenyanuwa, yaiwa ardo alkawarin yana lissafe d ranakun d akasa, insha Allah cikin satin zai zo dan ayi shaanin biki dashi, ardo yaso Sadik y dauki hutu koda n satine saboda bikin amma yasan hakan b mai yiwuwa bane, haka sukai sallama y baro kauyen. Tinda y cika umarnin mahaifinshi y tsinci kansa cikin matsanancin farinciki, yadau alwashin kan cewa bazai taba barin hajiya t gano auren d ardo ke shirin yimasa, sun cigaba d gudanar d rayuwarsu kamar yanda suka saba shida hajiyarsa, duk wani abu d yake bukata kan y furta hajiya t gamayimai, y manta d wani abu waishi talauci ,direba kekaishi aiki y daukoshi, yaso hajiya ta saimishi mota, ta mishi alkawarin insha Allah akwai kudadenta da take tsimaye, suna futowa inshaa Allah zata saya mishi Akwana atashi b wuya, shirye shiryen bikin Sadik d deeje y kankama, ardoma y kammala gyarawa amarya sashen d zata tare, abangaren Sadik Kuwa y shiga damuwa, wacce karyar zai yiwa hajiya danta barshi yai kwanaki koda biyune. Suna kwance, bacci yama fara daukan hajiya, yadan bubbuga hannunta, tare d cewa hajiyata, cikin magagin bacci tace na am habibi ya akai, yace dazu ardo y kirani, yake sanar Dani lallai lallai gobe naje yanada bukatar ganina, mutssike idanuwa tayi tare d mikewa zaune tace inceko dai lfy habibi, yace tonimadai tinda y kirani n kasa samun nutsuwa, addua t shigayi Allah dai yasa lafiya, yakara d cewa inshaa Allah d asuba zanyi sammakon tafiya ,hajiya cikin tausayawa d jimami tace Allah y kaimu asuban fatana dai Allah yasa lafiya, yace amin.ganin t amince d batunnashi hartana Addua Allah yasa kiran n alkhairi yaji dadi aranshi, cikin nutsuwa y shirya, d kanta takaishi hartasha tare d bashi kudi y zuba a aljihu saboda bukatun d kantaso b shiri wannan ai shine MIJIN HAJIYA Ayushailiasu.Blogspot.com [5:36pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 55-60 I Dedicated this page to Sistr jidda (Admin hausa novel group 1) Ardo yayi murna d zuwan dannasa akan lokaci, ko ina ka juya wasanni ake gudanarwa kofar gidan ardo n murnar auren sadik. Ansha shagalin biki sosae inda y banbanta da wancan auren nasa kai hatta bukukuwan da akeyi a garin wannan y banbanta dashi saboda wayewar da sadik yai a birni da irin kaya da kudin d aka kashe,duk inda ka zaga a kauyen ba abinda ake sai maganar bikin sadik da irin shagalin da akai. Daren ranar juma'a aka kawo amarya kasancewar anriga an daura aure tin bayan sallahr juma'a,aladar garin ce randa aka daura aure ranar ake kai amarya sannan kashe gari ayi budar kai da jere da daddare a raka ango dakin amarya. Bayan anyi budar kai da daddare abokan sadik su biyu suka rakashi daki amarya andan taba hira sanna sukai addua d fatan alkhr, suka kara yiwa sadik nasiha akan hakkin aure duk d sunaan ba auren fari ne gareshi ba, yaji dadin adduar d nasihar sannan ya rakosu bakin kofa sukai sallama yai musu godiya suka tafi. Deeja tinda suka shigo tsoro y darsu a zuciyarta, jikinta yai sanyi,takurewa tai a bakin gado lkcn d yashigo y umarceta tasaki jikinta danya lura d yanayin da take ciki, ckin lallami yashawo kanta har sukaci abinda ya shigo dashi n amarci, ganin tsoron d deeja keciki ne ya sanya sadik daga mata kafa badan yaso ba, hira suka fara tabawa gyangyadi ya fara daukar deeeja,ganin hakane ya sa sadik umartarta dataje t kwanta. A wannan daren bacci barawone y sace sadik badan yasani b saidan kogin tunani d kewar hajiyarsa da yakeyi d tunanin irin karyar d zai mata yasamu mafita a gunta, itakuwa deeja baccinta take bilhakki batamasan yanai ba wai kunu a wani gida,dg karshe tunani yazo masa ya kashe wayarsa ydd hjyar zatai ta kira a kashe inyaso inya koma ta tambayeshi sai yace mata tafiya sukai d Ardo kuma kauyen da sukaje ba service shiya ya kashe wayar. Jin kiraye kirayen sallahr asuba ne ya farkar da sadik, cikin hanzari ya mike gami d ficewa ya dauro alwala sannan y dawo ya tashi deeja datake shara baccinta dan tayi sallah, yana fitowa bai zame ko inaba sai masallaci,bangaren deeja ma tana tashi alwala ta dauro ta dawo daki t gabatar da sallahr asunba,zama tai inda tai sallah dan jiran shigowar angon nata amma shuru takeji kmr an shuka dusa,shikuwa sadik daya fito dg masallaci bai tsaya ba sai a kofar gidansu dan ya gaida mahaifinsa. Lokacin da gari yai shaaaaa (yai haske) deeja t muke tanufi bandaki danyin wanka,fitowarta dg bandaki tai daidai d shugowar sadik da gudu ta karasa daki tai maza ta zura hijab dinta sbd daurin kirjin datai wai a lallai ita kunya dariya abin y baiwa sadik a zuciyarsa yace ni danake d hajiya harda wani abu d mace zata boyen, karasawa dakin yai yana tsokanar deeja d cewa dan kin ganni kike gudu harda sa hijab to kwalliyarma ni zanyi miki naga tafadi wai kwarkwata ta kada kudi ido ta zaro tace aa kayi hakuri zanyi d kaina, yace to meye na gudu dan kin ganni? bakomai tace masa yai dariya yace to ayi kwalliyar nagani, lkcn ta rissina tace masa ina kwana? ya amsa da lpylau amaryata, murmushi ta sakar masa wanda saida hakoranta suka bayyana tare d dinful dinta kyanta ya kara bayyana a gareshi take yaji kauna d kwadayin son y kasance d ita ya kamashi. Shiri tsaf tayi ckn atampha riga d zani sunyi mata kyau, tayi kwalliyarsu irin ta fulani wdd takara futo mata da dogon hancinta d dara daran idanunta, duk ji da birnancin da sadik yake saida ya yaba kyan da tai, tsam y taso dg mazaunin da yake ya dawo kusa d ita y zauna, lkcn d ya janyota jikinsa ya matseta ta saki wata yar kara sbd jin zarrrr wani saban yanayi dataji yana yawo ckn jininta,cikin kidimewa sadik ke tambayarta lafiya,kallanshi tai d sexy eyes dinta take yaji wasu sakonni suna shiga jikinsa, jin sallamr yaron d ardo ya aiko ya kawo musu karin kumallo ne ya katse su dg kallon junan dasuka dau lokaci sunayi. Ayushailiasu.blogspot.com

No comments:

Post a Comment