Saturday, 5 November 2016
[5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. …………Story:-Hawwa Saleh. 111-115 Tin dawowar sadik daga kauye tsanani y kara yawaita a tsakaninsa da hajiya saboda ta fuskanci sadik akwai abinda yake boye mata dan haka ta kara takura masa gami d sakar masa duukan ragamar aikin gidan,dan a halin yanzu sadik shike dukkan wani aiki kama dg shara,moppin, wanke-wanke,girki, harma da wanki duk saiya y kammalasu ya wankewa hajiya mota sannan yai shirin tafia makaranta, komai makarar da xaiyi saiya tabbatar d yagama sannan ya tafi. A halin yanxu sadik baya samun saken zuwa kauye saidai yai satar hanya a ranakun makaranta ya dau excuse gurin principal yaje batare d hajiya tasani ba, duk d wannan dabarar da sadik keyi saida hajiya tasha jinin jikinta sabida tasaba karfe 2:00 sadik kedawowa gida yanxu kuwa saiya yakai 3:00 ko 3:30 baidawo b idan ta tsareshi da tambayer meya zaunar dashi sai yaita kame kame da soki burutsu, ganin hakane ya sanya hajiya ta baza C.ID din d zasu ringa bibiyarsa batare d sadik y saniba, dama ai shi ramin karya kurarrene. A yau ne deeja ta cika wata hudu a gidan mijinta, d safiyar wannan ranar ne tana sharar tsakar gida ciwon ciki ya turniketa sharar d bata karasaba kenan, dakyar ta iya jan jiki zuwa daki, murkususu take famanyi sabida axabar ciwon dake cinta, wayar d sadik y bata ta lalibo ta kira lambar sadik amma a kashe gashi gida ita kadai,haka taita faman juyi a tsakar daki har kusan shabiyu na rana tarasa yadda zatai,tana cikin wannan hali Allah ya jefo d kanwarta harira antasosu daga makarantar allo, sallama tai jin baa amsa mata bane yasanyata hanzarin karasawa dakin, tana daga labule ta hango deeja yashe a kasa tagama galabaita ciwo ya gama cinta, ninfashinta dake kaiwa da komowa ne yasanya harira rudewa ta juya d gudu tai gidansu. Cikin dimuwa harira ta fada gida ko sallama babu tana kuka tana kiran inna! inna!!, dasauri inna ta fito daga daki danjin irin wannan kira ba lafiya ba, tambayarta take harira meyafaru? amma fadi take Zata mutu inna, zata mutu wllh tsuwace ta kauracewa inna ta jijjiga harira tace wace zata mutu? kofar fita harira take nunawa inna tana cewa deejace deejace……… subhanallah inna take fadi ta shiga daki ta dakko mayafinta tai waje. Tafiya inna take cikin sauri kamar zata fadi dan batasan inda take jefa kafarta ta mayarba ta nufi gidan deeja, tana shiga taga halin d deeja take ciki tagama galabaita, sallallami tashigayi tana ambaton sunan Allah,juyawa tai ta nufi gidan ardo ta sanar dashi halin d deeja take ciki, rudewa ardo yai ya nufi titi dan taro mota,sannan inna ta juya ta koma gun deeja,idon inna ba abinda yake banda zubar da hawaye saboda tausayin deeja,dan ita ta gama fiddarai d deeja mawuyacine tai rai, ganin idon deeja ya fara kafewa ne ya sanya inna rushewa d kukalokacin ardo yai sallama gami dacewa kumaza kufito g mota mutafi asibiti, dakyar inna ta iya takaikayo deeja zuwa motar sabida duk jikinta ya saki ta kara nauyi,direct babban asibitin garin suka nufa da deeja. Suna isa asibitin likita yai umarni d aimaza a kaita deeja emergency room sabida ganin halin da take ciki,lokacin d aka shiga d deeja dakin taimakon gaggawane muma mukai d'uuuuuu zamushiga, juyowa likita yai ya dakatar damu ta hanyar cewa anan xaku jira baa shiga dakin,nan mukai curko curko a tsaye muka xubawa sarautar Allah ido,muna jiran tsammanin marabbuka malam yaki noma dan zakka,daidai lokacin na kara saita birona bisa littafina ina jira azo ace abu kazane yasami deeja na nado muku rahoto amma shuru matakau kakeji ba likita ba alamarsa kamar an aiki bawa garinsu dan innama tagaji da safa da marwar d takeyi ta zauna ta zabga takugi ba abinda take a zuciyarta sai adduar nemawa yarta lafiya. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 116-120 DEDICATED TO UMMAKULSUM( MUM APIPA) FIRST CLASS GROUP Likita ne ya fito da gudu inna ta tashi ta karasa gareshi, tambayarsa take jikin deeja yace mata dasauki tasamu bacci, umartarta yai da tabiyoshi zuwa dakin,kafin ya fadamata abinda yake damun deeja ta kagu ta tambayeshi likita meyasameta? nan yake tambayarta tana da aurene, tace eh, yace to gaskiya matsanancin ciwon marane yake damunta dan haka koda yaushe mijinta ya ringa kasancewa da ita inba hakaba duk randa yakuma tashi zata iya rasa ranta sbd yanzuma da kyar suka shawo kan ciwon saboda yaci karfinta, cikin mamaki inna ta ke amsawa likita da insha Allah zaa kiyaye mijin natane ba mazauniba shiyasa, nan likitan yace to gaskiya yatafi da ita shine kawai mafita sannan ya mika mata katin magungunan gami d cewa idan ta tashi saiku tafi, ta karba katin taimasa godiya. Ahalin yanzu principal ya gaji d baiwa sadik permission koda yaushe, dan haka abin duniya duk ya isheshi ga hajiya itama ta kafa ta tsare, dan haka sadik idan antashi dg makaranta yake zagayawa kauye yai maxa ya dawo batare da wani abu ya shiga takaninsa da deejaba sai dan kawai gudun fadan ardo, ganin sadik baya dawowa sai 6:00 ne yasa hajiya tasa driver ya dinga zuwa yana dakkoshi da zarar antashi wataran ma sai driver ya tsaya antashesu, "dandan dandan dandan ga akuya ga kura" Jin jawabin likita d innatai ne yakara daga mata hankali bayan sun koma gidane take sanarwa da ardo abinda likita yace takara da cewa in hakane wannan auran na deeja bai kara musu komaiba sai janyowa yarsu ciwo har anacewa zata rasa ranta,jikin ardone yai sanyi yashiga bata hakuri d cewa bazaai hakaba insha Allah zai daumataki zai aikawa sadik yaxo yatafi da matarsa,inna tace to shikenan,sallama sukai d inna yatafi, dg nan bai zame ko inaba sai gidansu nasiru akace bayanan yaje kasuwa,sallahu y bayar da cewa inya dawo ace yana nemansa dan Allah. Bayan sallahr laasar nasiru y dawo gida ko zama baiba aka fada masa ardo yazo nemansa dan haka ya fasa zsma ya juya yanufi gidan ardo, yana isa sukai kachibis dashi yafito dg cikin gida, gaisawa sukai ardo yake fadamasa dama zuwa yai ya kiramasa sadik zasuyi magana, nan nasiru ya kira wayar sadik a kashe,jin akashe takene yasa ardo jikinsa ya kara sanyi yaimasa godiya yatafi, tinda ardo y shiga gida baisake futowaba saidayaji kiran sallahr magriba ba abinda yake sai xulumi d tunanin sadik wane irin abu yakeyi a birni da kullin wayarsa a kashe, kardai sadik wata harkar daban yakeyi ba koyarwaba a birni, hakadai yaita tintintini. Alhmdllh deeja tadan samu sauki dan inna bata bari anmaidata dakintaba gidanta tatafi da ita dan tafi samun kula,acewarta koda wani abunne zai kuma samunta gara tana gaban idonta tinda can gidanta tazama yar gadinsa. Tsohon wannan dare sadik kasa bacci yai jikinsa na bashi wani abu yafaru a kauye, da sassafe yai shirim tafiya makaranta ko breakfast baiba balle ya sanarwa da hajiya yatafi dan bacci take, haka yasa kansa yai waje batare dayayi aikace aikacen gidan da yasababa, gidansu salele ya nufa yakarbi wayarsa yana budewa ya lalibi lambar nasiru ya kira, ringin biyu nasiru ya dauka, sungaisa kafin nasiru yagayamasa ardo na nemansa sadik yace dan Allah ya kaiwa ardo wayar zasuyi magana ya amsa masa d nan da minti biyar yakara kira, cikin hanzari nasiru ya kaiwa ardo wayar, jim kadan sadik ya sake kira nan ardo ya fadashi da fada yaimasa kaca kaca tare da zayyanamasa abinda likita yace km ya umarceshi karya sake makonnan ya cinye baixoba kuma ya tabbatar ya nemi dakin dazaisa deeja a birni inba hakaba zaihanashi aikin dayakeyi, shuru yai yana sauraron mahaifin nasa ya gaza cewa uffan saida ya tabbatar ya gama maganarsa ya bude baki zaiyi magana yaji ankashe wayar saboda ardo baya bukatar jin abinda zaice umarni ya bashi aceawarsa,nan y mikawa nasiru wayarsa gami d godiya ya shige gida sabida ransa ya baci sosai. Sadik kiran wayar yakarayi amma maimakon yaji muryar ardo saiyaji nasirune ya tambayeshi ardo yace yashiga gida, nan nasiru ya karamasa nasihohi sabida yaji akan abinda ardo yake fada godiya sadik yaiwa nasiru cikin sanyin jiki ya kashe wayar. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 121-125 DEDICATED TO BINTA SALEH ( MAMAN AYSHA )FIRSTCLASS GROUP Asanyaye sadik y karasa makaranta jiki ba kwari yaje yai signin a staff room ya shiga ya zauna jiki lakwas tinani yashiga zabgawa akan maganar baffansa ta ina zaifara? ya zaai ya kunce kullin bakin wannan buhun?idan har yazo d deeja garinnan ya zaiyi?ya zai yi ya dinga kwana a gurinta? idan hajiya taji wannan labarin wane hukunci zatai masa? Idan ardo yaji labarin sa na auren hajiya wane mataki zai yanke masa? Kodai sakin deeja zanyi ne nahuta? Aikuma ina sonta baxan iya sakinta ba, wata zuciyar tace masa towai kai kasaki hajiyan man ko kagudu ka barta tinda batasan garinkuba? tabb hajiy ai itace rayuwata bazan iya sakinta ba amsar d wata zuciyae tabashi kenan, "kwadayi mabudin wahala su sadik baa sadudaba ashe" tambayoyi dai barkatai zuciyarsa taita jero masa wadda ya tabbatar da baida amsoshinsu, can wata zuciyar tace kawai ka amince ka taho da deeja,to idan nataho d ita ya xanyi da bukatarta? to basaika ringa zagawa d ranaba, wata xuciyar tace idan hajiya tabarka ba, kadai san kai MIJIN HAJIA ne, yana kaiwanan a tunaninsa sai kwalla zarrr ta biyo kuncinsa. Haka sadik yaita tufka d warwara idan wannan zuciyar ta tufka masa sai dayar ta zago ta warwaremasa yarasa abinda yake masa dadi,kasa tabuka komai yai a wannan ranar shikuwa salele tinda ya shigo makaranta bai zauna a staff room b balle yasan halin d sadik keciki. Kamar ancewa sadik miki ka kalli window yai ido hudu da motar hajiya ta kunno kai cikin makaranta, direct office din principal ta nufa, sun gaisa d principal cikin girmamawa take cewa dan Allah zuwatai ta daukarwa sadik permission wata tafiyace ta taso cikin gaggawa zasuje, nan principal ya bata dama sukai sallama taimasa godiya, shiko sadik jikine yadau kyarma meyakawo hajiya makarantarsu? Baisamo amsarba yaganta kmr wadda aka jefota cikin staff room din, suna hada ido ta dokamsa harara cikin kaushin murya tace ka kyauta daka fito ka barmin gida kaca kaca bakai abinda d yazamema wajibiba, wuce kashige mutafi ka gyaramin gidana tana nuna masa kofa da hannunta, "Oh ni 'yatasua yau su hajiya d angonta ba harkar murmusawa juna a gaba ta tisashi har gaban mota gami da umartarsa yai driving, ita km tashige baya ta hakince,HHHHHHH su sadik yau anzama driver,lallai yau sadik angama cika MIJIN HAJIA,driving yakeyi kawai batare d hankalinsa n jikinsa ba abu goma da ashirn ya hade masa baffa ya hadamasa zafi ga hajiya t kunno masa wuta mai huci. Kyal kyal kyal dariya mai kafa uku rak naiwa sadik kar nima na kara ruramasa takaici. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 126-130 Da safiyar yau laraba misalin 8:30 sadik ya fito dg gidan hajiya bayan ya gama dukkan wani aiki d yasaba yi,yai wa hajiya sallama akan cewa yatafi makaranta saidai b makarantar xaijeba kauye ya nufa dan yasan inyaje makarantar principal bazai bashi permission ba dan haka yai tafiyarsa kauye kai tsaye,yana isa kofar gida ya iske ardo ya zabga uban tagumi, sallama yaimasa cikin sanyin murya ya amsa, bayan sun gaisane ardo ya ninfasa yace dafatan da shirin tafiya da matarka kazo ko? Shiru yai a zuciyarsa yana cewa ashe da gaske baffa yake nai zaton bacin raine ya sanyashi fadar haka ko rashin lafiyar deeja ce tasa………………bai karasa tinaninsa ba yai tsinkaye d muryar ardo cikin tsawa yace ba magana nake dakai ba? sadik bafa zaka maidani mutumin banxa a garinnan ba na fadama yau kafarka kafar matarka dan naga take takenka na shure maganar da nake fadamaka kuma kafata kafarka zamu tafi naga mahallin da zaka kaita, lokacin gaban sadik y kara fadin rassssss, hakuri ya dingi baiwa ardo dakyar ardo ya yadda kan yarjejeniyar ranar lahadi zaizo su tafi. Gidansu deeja ya karasa ya dubata, gani ranewar da tayine yasanya sadik ya tausaya mata danba karamar ramewa taiba saidai bai mata magana akan ramar da yaga tayiba, itama deeja ganin ramar da sadik yai ne yasanya deeja tambayarsa yataga ga rame? Ko baida lafiya ne? dariyar yake yai wadda tafi kuka ciwo yace rashinta kusa dashine ne yasanyashi rama da kuma rashin lafiyarta, tausaya masa tai gami da yimasa dadadan kalamai, sundan taba hira sannan yaimata sallama dacewa ranar lahadi zaizo sutafi, wani farin cikine ya ziyarci zuciyar deeja wanda har fuskarta saida ta bayyana irin farin cikin da takeji, murmushin kashe zuciya ta sakarwa sadik wanda shima saida ya maida mata martani tace Allah y kaimu,ya amsa da amin ya tafi. Sadik ko gidan ardo bai komaba ya nufi hanyar titi ciki d tausayin deeja sabida ganin irin farincikin da ya bayyana a fuskarta da yace zaixo sutaho ya tabbata tana cike da bukatarsa tayi kewarsa kamar yadda shima yai kewarta dan yanxu hajiya bata wadatar dashi kamar yadda deeja take masa. 1:20 daidai sadik ya sauka garin kaduna,masallacin dake kusa d gidan su salelr ya nufa yai sallahr axahar, bayan y idar ne ya kaiwa Allah kukansa ya kawo masa sauki da rangwame gami d mafita a wannan alamari da ya kunno masa ,su Sadik sai yanxu akatuno d ubangiji sannan ya fito ya nufi gidansu salele duk d yasan yanzu baidawo dg makaranta ba amma saiya zauna a kofar gidan ya na jiran dawowarsa,duniyar tinani sadik ya fada,sanda yai nisa a tinaninsa ne yaji an dafa kafadarsa yana dagowa yaga salele ne, tambayarsa salele yashigayi meyahashi zuwa makaranta yau ga driver yaxo daukarsa? Sai a lokacin sadik ya tuna da driver n xuwa daukarsa, cikin sanyin murya yace salele zauna kabani shawara yadda zanyi, wllh duk alamura sin jagulemin, salele yace meyafaru kuma? Nan sadik ya zayyanawa salele yadda sukai da ardo, jinjina kai salele yai yace sadik kayi ganganci, amma yanxu akwai wani care taker saimuje ya samoma daki mai saukin kudi,sadik yace to gami da tashi suka rankaya, sunyi saa kuwa da zuwansu ansamu dakin kan kudi naira dubu goma sha biyar, nan suka ce da maibada dakin yai musu lamuni abiya albashi zasu kawo saboda lokacin daf ake da biyan albashin, kasancewar care taker yasan salele yasa ya lamince masa, godiya sukaimasa sannan suka dunguma ya nuna musu gidan. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ……....Story:-Hawwa Saleh. 131-135 C.I.D din d hajiya ta baza su ringa bibiyar sadik ne sukai sallama lokacin hajiya na zaune a palo ranta a bace, umarni taimusu sushigo, suka shigo bayan sun gaisa ne suke sanar da ita yau sunga sadik a wani kauye da safe, tambayarsu tai mai yajeyi? suka ce basu saniba amma tabbas sunganshi acan, tace sun tabbata ko yanzu zasu iyai mata jagora kauyen? Sukace eh zasu iya, godiya taimusa gami d kyautar kudi suka tafi,ran hajiya ya kuma baci matuka dajin wannan labarin ga kuma driver ya zo yafada mata yaje dakko shi a makaranta ance masa baizo ba ma kwata kwata,kudara tai ranta yau sadik saiya fada mata inda yaje da abinda yake boye mata sannan taci zarafinsa wata zuciyar kuma tace a'a bahaka zakiba a hankali cikin siyasa zaki gane komai,yadda hajiya tai d shawarar da xuciyarta ta bata. Karfe 3:00 sadik ya shigo gidan hajiya,ko kallonsa bataiba balle taimasa magana,ganin haka d sadik yai yasa yawuce sumsum yana sunkui da kai ya fada daki, kayansa ya cire gami d watsa ruwa ya fito palo, guri yanema nesa da hajiya ya zauna yace hajiyata sannu da hutawa, yawwa sannu da alamunka yau kasha aiki a makaranta tace masa tacigaba d abinda takeyi, shuru sadik yai baice komaiba dan yasan magana hajiyar ta dankara masa,sundau lokaci batare da kowa y sake maganaba sannan hajiya tace inbaxakaci abinciba ina bukatar kazo ka yanken farce,shafa keya yai yamike ya nufi dining. Sunkuye yake yana yanke mata farcen kafa tai gyaran murya tace sadik ya dago da sauri ya kalleta saboda jin tace sadik yace da wata akasa yau dan bahaka tasaba kiransa ba, cigaba tai da magana kaga yau kimanin wata takwas da aurenmu yaci ace nasan mahaifarka, iyayenka sun sanni na sansu bawai muyita zama bansansu ba, dummmm sadik yai ya tsaya cak da yankan farcen gabansa ba abunda yake sai dukan uku uku shuru yai yakasa magana,jin yai shuru ne yasa hajiya tace koba haka ba? Cikin karfin hali ya kakaro murmushi yace eh hakane, tace to inason ka shirya ranar lahadi sai muje ko,"tab akwai gwarama" jin tace lahadi ne yasanya sadik zaro ido a tsorace yace lahadi kuma hajiya? hajiya ta lura da furgicin da yashiga ta basar , dan son tagano abinda yake boye mata tace eh lahadi,yace dadai an canja wata ranar, tace ranar lahadin nakeson zuwa umarni nabaka bawai shawararka nanema ba ba dan haka inason kazama cikin shirine ma yasa na fadamaka koda abinda zakai tanadi kafin ranar dasai dai ranar lahadin nace kafito mutafi. Acan kauye kuwa farinciki ya ishi deeja da inna harma da ardo sabida tafiyar deeja birni, shirye shirye gadan gadan inna tashiga yiwa deeja don tafiya garin gwamna ranar lahadi. Bangaren sadik kuwa rudu, dimuwa, tashin hankali sune suka kaiwa zuciyarsa farmaki,yaka xaune yakasa tsaye a lallai saiya samo mafita, kwanciyar hankali da nutsuwa sunyi kaura daga gareshi. Tabbb tashin hankali balagar tsintsaye hajiya da ardo sun hadawa sadik zafi, makaranta littafin MIJIN HAJIYA ku tayani tinani anya kuwa sadik zai samo mafitar yadda zaiyi da hajiya kafin ranar lahadi? Ina sauraranku………… *INVITATION !!!* Karan katakaf kafitanin ilahirin gaba daya kwatar makaranta littafin MIJIN HAJIA, ni AYUSHA ina gayyatarku rakiya da taken baya zuwa kauye dan ku ganewa idonku yadda wannan gwarama zata kasance tsakanin sadik,hajiya,da ardo basai kunjira labari daga gareni ba gara kuga kwal uwar daka d idon ku. *………waiting………* Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 141-145 Misalin karfe 10:00 na safiyar ranar asabar sadik d hajiya na zaune a dining suna breakfast, fork da knife din dake hannun ta ta ajiye gami da daukar mug din tea ta kurba,sannan tace sadik ka shirya zamuje kasuwa domin yiwa su baffa tsaraba dagowa yai ya kalleta ta sakar masa murmushi batare daya maida mata ba yace to, ta lura da yanayin sadik ta kara cewa me da me yaka mata musiyo musu? sakin fuska yai kadan yace duk abinda aka siyo yayi,haushine ya kama hajiya tace kai nakeson ka fadaamin ai, yace ke me kikaga ya dace a sai musu? cikin fara'a hajiya tace asiyo atampha da shadda sannan a saiwa yaranka kaya d takalmi, sai kuma kayan abinci da sannan muje mall ai musu tsarabar abin tabawa ko baiba? haushine y kama sadik saidai bai nuna a fuskaba yace yayi hakan Allah ya kara budi, amin t amsa masa gami dacewa sai muje mu shirya,"niko nace yau hajiya shiri akeji da sadik". 11:30 daidai su hajiya aka fito cikin shirin tafiya kasuwa,jerowa sukai cikin takun kasaita suka nufo parking space inda motar hajiya take, mukullin dake rike a hannunta ta mikawaa sadik ya karba ya bude motar, drivers seat ta umarceshi ya zauna ita km ta zauna a kusa dashi, tada motar yai yaji hajiya nacewa habibi kasuwar zamu fara zuwa amma, to yace mata dan har lokacin fuskarsa ba walwala. Sun isa kasuwa sunyi siyayya sannan suka wuce mall, sun gama siyayyar dazasuyi sun dakko hanyar gida ne hajiya kecewa wllh nagaji habibi da mun biya nakarbo dinki na, sadik yace to mexai hana mubiya, a'a tace muwuce gida anjima sai kazo ka karbar min dan nagaji kwanciya nake sonyi "abinka da katuwar mace" sadik dan haushi ko amsa mata baiba yacigaba da tukin da yakeyi,har suka kusa karasawa gida ba wanda y kara magana tsakaninsu dan shi sadik ba abinda yake illa tinanin samun mafita kafin gobe,amma har suka je gidan ba wata dabara da tafado masa koda guda daya. Bayan sallahr azahar ne hajiya na kwance akan gadonta sadik y shigo umartarsa tai yadau mukullin motar ta yai sauri ya karbo mata dinki, ba musu ya dauka yai waje, tafiya kawai yake a cikin motar amma yagaza nutsuwa sai can wata zuciyar tace ka biya wajen salele man ka fadamasa ko zai samoma mafita,sadik baiyi kasa a guiwaba ya juya akalar mota yanufi gidansu salele, da zuwansa ya aika yaro yaimasa sallama dashi, yaron ya fito yace wai bayanan,takaici ne ya dira a zuciyar sa ya juya yashiga mota ya tayar yana tafiya a hankali, yana fita dg lungun gidan zai hau titi yahangi salele ya taho,hamdala yai yai saurin parkin ya fito,kira y kwallawa salele, jin da salele yai ankira sunansa ne yasashi juyawa sukai arangama da sadik, karasawa yai inda yai parkin yana washe baki yace da sadik lallai kaga MIJIN HAJIA tawaru ta warware maka kenan da hajiyar taka irin wannan dalleliyar mota haka, haushine ya kama sadik jin salele yace MIJIN HAJIA cikin fusata yace dallah malam wace warewa bayan dukunkunewa tai, dariya ?salele yai yace mekuma yafaru?nan sadik ya kwashe duk yadda sukai da hajiya yafadawa salele, shi kanshi salele kasa magana yai saidaga baya yace lallai kam t dukunkune, amma shawarar dazan baka yau yau da daddare kasan yadda zakai ka gudo dg gidan hajiya kazo ka kwana anan shagona dasafe sai ka tafi tinda hajiya batasan gidan nanba kuma batasan kauyen kuba balle tabika kaga dole ta hakura inyaso inka dawo kwayi wacce zakuyi kadai je kauyen, murnace ta kama sadik gami dacewa shiyasa nake sonka mutumina suka tafa, godiya sadik yaiwa salele yace saina zo din,sukai sallama. Sauri yai ya je yakarbo dinki yakawowa hajiya ransa kal da shawarar salele har Allah Allah yake dare yayi ya gudu,dinkin hajiya ta gwada gami da juyi ta kalli sadik tace ya kaganni habibi gobe, mirmishi yai yace ai zakiyi kyau tace bari kawai Allah dai ya kaimu goben yace amin. Agogo hajiya ta kalla tace habibi gaskiya nagaji d kallon nan bacci nakeji kaga 9:00pm tayi kataso mu kwanta, murmishi yai yace hajiyata gashi habibin naki yana son kallon film din yaimasa kyau ya zai kenan "Oh shiri yatashi kenan tsakanin masoya" kallon satai irin kallon masoya ido cikin ido tace to gaskiya ni kahakura mukwa.………,kafin takarasa yai kissin dinta yace hajiyata tai hakuri habibinta ya gama kallo, noke kafada tai alamar a'a lallai su hajiya a dole sai anyi acting irin na yara haka sadik yaita lallaba dakyar ta yadda saida ya rakata har daki ya kwantar da ita atsakiyar gado gami da yimata liff liff irin n yara sannan ya dawo palo yana godiya ga Allah, xama yai yacigaba da kallo saidai hankalinshi baya tare dashi, saida ya daidaici hajiya tai nisa da bacci sannan ya kashe TV din ya nufi gate ,maigadi ne yace da sadik ranka ya dade bada mota zaa fitaba ne, yace eh ba nisa inda zani shiyasa, adawo lafiya yai masa ya fito ya dau hanya sai gidan su salele. Karfa 10:00 na dare tayi salele yaga sadik shuru baixo ba har yafara tinanin ko bazai zobane sai yaji sallamar sadik ya shigo cikin shagon, shewa sukai gami d tafawa salele yace nazata baxaka zoba yace ai saida nabari tai bacci sannan na taho, shewa harda tafa hannu sukai, salele yace angaida MIJIN HAJIAni kuma sanda sukai shewa nace su sadik duniya tai dadi har ansamu damar shewa. Can kuwa hajiya baccin take tayi bata farkaba sai 12:00 na dare, ganin ba sadik ba alamarsa ne yasa tai saurin miqewa ta fito palo, wayam tagani ba sadik tashiga tinanin ina sadik y tafi, karfim hali tai tafito gurin maigadi ta tambayeshi yace mata tabbas yafita amma baudawoba, juyawa tai takoma daki tana cewa aranta dama da abinda sadik ke nufi tinda tace zasu kauye ya musa mata ta kudirce a ranta lallaifa ba fashi gobe zatasa c.i.d dinta su rakata kauyen ko tambaya ne tayi indai dan garin ne bazai buyaba, haka taita tunanini har bacci ya dauketa. Sadik kuwa kwana sukai suna zabga hira da salele dan bacci barawo kasa daukarsi yai sai chasar hira suke, sadik jinsa yake wasai dashi zuciyarsa shar da ita saidai idan ya tuna inya kawo deeja nan garin ya zai ringa kwana agunta ne sai jikinsa yai sanyi, hakadai sukaci gaba da hira har akai kiran assalatu. *YAU TAKE LAHADI………* Hausawa sunce rana bata karya saidai uwar diya taji kunya kuma rana dubu ta barawo rana daya tak tamai kaya, duk abin d akasawa rana zaizo dan haka ni AYUSHA nake cewa ina fata makaranta littafin MIJIN HAJIA sun shirya tsaf domin zuwa kauye ganewa………… dan yau take *LAHADI* ranar d xaa ware tsakanin tsaba d tsakuwa. Inkun tabbata kun shiry ku biyoni ………………… Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. …………Story:-Hawwa Saleh. 146-150 *LAST PAGE* *TO DAY IS SUNDAY* Allah ya kawomu wannan rana wadda bahaushe ke mata kirari da rana bata karya saidai uwar diya taji kunya, ranar d zaa ware zare d abawa,ranar da zaa ware tsakanin tsaba da tsakuwa,ranar da ido zai raina fata, ranar nadama da dansani,ranar tonan silili, ranar gori harda goriba,Allah y rabamu d irin wannan ranar amin. _Ina fatan makaranta littafin MIJIN HAJIA sun gama shiri dan anjima kadan zance ku biyo bayana_ Da safiyar wannan ranar ne sadik yai sallama da salele ya nufi hanyar tasha, motar d zata sadashi da mahaifarsa y hau,cikin lokaci kadan motar ta cika driver ya dau hanya,tsabar farin cikin d sadik ke ciki bazai misaltuba bai ankara ba yaga har anzo inda zai sauka,dakatar da drivern motar yai t hanyar cewa akwai mai sauka nan mota t tsaya ya sakko ya tari mashin ya hau dan ya karsa dashi ciki kauyen. _lokacin nace da makaranta littafin MIJIN HAJIA kubiyoni_ Kofar gidan ardo sadik y umarci mai mashin ya tsaya ya sauka, ya biyashi kudinsa _lokacin nima d tawagata muka karaso_, kai tsaye sadik ya shiga cikin gidansu a dakin dake bakin zaure ya iske ardo yana jan carbi kasancewar safiyace bai fito shan hantsi kan dakali ba,sallama yai masa cikin sakin fuska ardo ya amsa, jin dadin ya cika alkawarine yasa ardo yin haba haba dashi tare da umartarsa y zauna, guri sadik ya nema ya zauna suka gaisa cikin nutsuwa,ardo ne yake cewa d sadik ya hanya amma kayi sammako, sadik yace ai motar sassafe na biyo dan ina idar da sallahr asuba nai azamar tahowa,ardo yace koda najifa ai gara da ka iso da wuri dan mutafi da wuri ko madawo muma d wuri sadik yace ai shiyasa nai sammako, _nan na barsu suna hirar da da uba nace bari kuma mu leka gidan hajiya danjin yata tashi._ Misalin karfe 7:30 da rabi na safiyar wannan ranane hajiya taiwa c.id dinta waya suzo maza maza tanason ganinsu,angama hajiya sukace mata, wanka tashiga tai sannan ta shirya cikin kaya na gani nafade tsayawa baku labari ma daukar lokacine shiya nace ku taho kugani da idonku, dining ta nufa tai breakfast sannan ta dawo palo ta hakince tana jiran karasowar su, jin shirun da hajiya tai ne yasa ta kara kiran wayarsu suka sanar da ita suna hanya,tace sai sun karaso,10:15 daidai suka karaso cikin gidantsayawar motarsu d hajiya taji ne yasanyata yin ajiyar zuciya, sallama sukai tai musu izini d sushigo, bayan sun gaisane take fada musu cewa kauyen d sukaga sadik zasu kaita, batare d bata lokaciba suka amsa mata dacewa angama hajiya muna saurarom fitowarki a waje,yawwa tace musu suka mike sukai waje. Acan kauye kuwa labari ya zaga gari cewa yau deeja zata tafi birni, kowa sha'awa yake inama yarsace dansu zuwa birnima wahala yakewa mutanen kauyen,dan haka mutan kauyen suma sukace sai sunwa deeja rakiya har titin daxasu hau mota, bangaren deeja kuwa murna bazata misaltuba lokacin da sadik ya karasa gidansu dan sanar mata ta shirya ya karaso dan da wuri yakeson sutafi dan su baffa sudawo suma da wuri,sallama sukai tashige gida dan shiryawa,cikin murna take fadawa inna cewar su shirya sadik yazo yace kuma d wuri zasu tafi, farin ciki d murna inna takeyi hatta kanwar deeja murna takeyi yar uwarta zata tafi birni. Karfe 11:00 hajiya ta fito parkin space din gidanta har lokacin c. id din suna tsaye suna jiran ta, daya dg cikinsu ta mikawa key din motarta tace yai driving dinsu sukuma sauran su wuce gaba suna binsu a baya, haka akai kuwa b bata lokaci suka dau hanyar kauyen. Can kauye kuwa shiri y kammala t kowane bangare, inda aka fito d kayyakin deeja yan rakiya zuwa bakin titi kowa y dauka, dungumawa sikai suka nufi titi gaba dayanasu suna tafiya rafrafraf sina hira nan danan sai gani mukai mun kusa d titi, wata dalleliyar motace t kunno kai da wata n biye da ita saurin matsawa mukai dan kamar zasu bigemu muke gani,ganin motar dake biye a bayan dayar ne y sanya sadik yin saroro danya shaida motar sarai t hajiyace. Hajiyace ke cewa matukin motar y tsaya su tambayi wadannan mutanen tun kafin suyi nisa cikin kauyen, batare d ya musa mataba yai parkin gami d fitowa, inda tini daya motar tayi gaba, ganin motar hajiya ta tsaya ne yasa sadik kara daga kafa yana sauri, mutumin d yafito dg motar ne yatsai d wani saurayi yace d dan Allah malam ina tambaya, saurayin ya tsaya yace Allah isa nasani, yace masa dan Allah yasan wani sadik a kauyen nan sunan mahaifinaa ardo? "faduwace tazo daidai d zama ashe nasiru ake tambaya", nasiru y ce eh yasanshi gashi can ma kunyi sa'a dan birni yanzu zasu tafi da matarsa shine zamu rakasu titi,lokacin d mutumin y juya yake fadawa hajiya abinda nasiru yace masa ne nasiru ya kwallawa sadik kira, chak sadik ya tsaya batare d ya juyoba,hajiyace ta zaro ido tace what?,gami d fitowa daga cikin motar, ganin sadik ya tsaya kamar wanda aka kafene yasa ardo dake biye dashi cewa ya naga katsaya?ko ka manta wani abune?shidai sadik har lokacin bai motsaba bai kumayi magana ba,muna yan rakiya tsayawa mukai mukai chirko chirko ganin mai gayya mai aiki jagaban tafiya shima ya tsaya. Takowa hajiya tai d kafarta har inda sadik yake, gabansa ta tara ta tsaya shikuwa ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa dogoshi,can gefe guda innace d deeja a tsaye, daya barin kuwa ardone shima y kama kugu inda mukuma yan rakiya muka zagayesu. Dandan dandan dandan ga akuya ga kura,yau ake yinta g sadik, deeja, ardo, inna da yan rakiya, nikuwa nace wannan shine ana dara ga dare yayi, can ardo dake gefe abin nabashi mamaki ne ya karaso yace baiwar Allah meke faruwa na? Har lokacin sadik ya kasa motsi kamar wanda aka dasa, lokacin d hajiya ta dafa kafadar sadik ne gaba daya kallo ya koma sama yau g shaho ya dau giwa,tana cewa sadik ka munafimce ni, ka cuceni ka ha'inceni, sadik ashe kai butulune macuci azzalum……………bata karasa ba inna ta karaso tace ke baiwar Allah yazaki zo kina wannan maganganu na batanci a bainar jama'a , daga mata hannu hajiya tai cikin kaushin murya tace ke rufemin baki anata d'an marayan zaki wayake ta d'an gwani kakkausa, tsit inna tai hajiya taci gaba dacewa kinsan abin da ke tsakaninmu d shi ne da zaki tsomon baki, har lokacin sadik baice kala ba bai kuma dago ba kansa na sunkuye tabbacin munafikine,hajia taci gaba dacewa dama tinda naga take takenka nasan kai munafikine, cin zarafi da wulakanci, tonon silili da gori b wanda hajiya bataiwa sadik a bainar jama'a ba,saida ta zayyane musu kaf abinda yafaru tindaga aurensu har zuwa yanzu, mamakine ya kama mutanen gurin kowa yana Allah wadai d son abin duniya irin na sadiki,shiko gogan naka ba abinda yakeyi sai kuka shabe shabe, nadama da danasanin aure hajiya yake kawai a ransa, dan takaici ardo kasa magana yai tinda hajiya tafara magana saida takai aya sanna ya ninfasa yace da sadik banida abin cemaka sai godiya,nayi nadamar haihuwar ka sabida bata amfanan komaiba sai bakin ciki, gashi ka janyo min tijara da cin zarafi a abainar jama'a amma banma bakiba n barka da hakkin wannan cin mutuncin da kajowon dan bakai akaiwa ba ni akaiwa da zan zauna agari ni mutane zasuita zindena suna nunani duk inda na zaga ana cewa ga wanda dansa ya janyomasa tijara da bankada sabida yaje birni yai auren da ake kira MIJIN HAJIA,nagode kwarai ardo yana kaiwa nan ya juya ya nufi hanyar gidansa cikin kunar zuciya. Allah wadaran son abin duniya da son xuciya mutanen gurin suka dingayiwa sadik ihu d dankira afili,sanan hajiya tace kuma kai gaggawar sakina gami d dungure masa kai tace kwadayayye ta juya ta tafi, gani hajiya ta tafine nima nace da yan rakiyata suzo mutafi,muna tafiya sauran mutan kauyen suka watse suna Allah ya kara maganin mai kwadayi kenan dama ai duk wanda yahau motar kwadaya ba indazata saukeshi sai tashar wulakanci gashi kuwa anzo tashar ta sauke sadik, watswa mukai mukabar sadik a tsaye agun kamar bishiyar d aka dasa.atake agun Kuwa inna tace Aikuwa nima nan n tafi d yata, bazamu hada zuriya d irin kwadayiba abarwa jikokina abin gori a gari ,danhaka zaman ku d da deeja y Kare daga yau, inajiran K aiko mana d takardartakwadayayye . Abin duniya ya ishi Sadik, yarasa abinda ke mishi dadi, juyawa yai yana yiwa mahaifarsa kallon bankwana, saboda y kudiri aniyar bazai kara zuwa ba har abada gudun wake wake da dankira na yan kauye Gani g wane dai ya ishi wane tsoron Allah, kuma ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka,Allah karka nuna mana ranar nadama d danasani dan kayace a baya ake barinta.Manzon Allah SAW yace "mai hankali shine wanda ya wa'azantu da waninsa",Allah yasa wannan littafi yaxama wa'azi tsakanin alumma, amin. *ALHAMDULILLAH!!!* *GODIYA* Dukkan yabo d godiya sun tabbata ga ALLAH, Al-kaliqu wanda ya halicci sama d kasa batare da dogaroba, tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta baki daya wanda akai duniya da lahira danshi, akai wuta da aljanna dan masoya da makiyansa, d yabani ikon kammala wannan littafi MIJIN HAJIA,Allah y bamu ladan daidai din d mukai ya yafe mana kuarakuran d mukai acikinsa bisa tuntunben hannu d harshe.Amin. *INA ALFAHRI DAKU:-* Mahaifiyata Allah y kara miki lafiya da nisan kwana mai amfani, Mahaifina da yarigamu gidan gsky ubangiji yai masa rahma ys aljnn makoma d sauran alummar Annabi.Amin. *ABOKANAN TAFIYATA:-* 'Yan uwa najini Hafsat, Hajara, Aminatu, Asma'u d Musa,Allah y iya muku a rayuwarku. *YARA MANYAN GOBE:-* Fatima (Ihsan),Ahmad,Usman (Sudaiz),Al-ameen, Abdurrahman (Haneef) d Hajara (Ihsan),Allah yai muku albarka. *KULLIN KUNA RAINA:-* Masoyana Ummukhulsum (Mmn afeefa),Abeeda, Baseera,Deeja,Aysha (Mmn zahra),Lubabatu, da Takwarorina Aysha Iliasu Bauchi State,Aysha Iliasu Zamfara,Marubuciyar kinmin halacci wato Aysha Tsafe, Allah yabar kauna cikin aminci, Amin. *BAZAN MANTA DAKUBA:-*Aysha (Ummu Abdullah), Mmn Musaddiq d Mmn Eeman,Allah y barmu tare,Amin. *GAISUWATA A GAREKU:-* Aysha Humaira (Melody),Aysha Bawa, Aneesa Abubakar Rimi (Aneelurv), Huwailat (Mrs jee),Hawwa Jidda AKA, da sauran Online Hausa Writers. *JINJINATA GAREKI:-* 'yar uwa, kanwa kuma abokiyar shawara Hawwa Saleh,Allah ya barmu tare har aljanna,Amin. *SAKON KARSHE:-* Zuwa g masu karanta littafina nagode Allah y saka muku da Alkhr ya faranta muku a rayuwarku,Amin. *TAKU HAR KULLIN:-* Ayusha Iliasu nake cewa Tammat bi hamdillah,sai kunjini a littafi nagaba. Ayushailiasu.blogspot.com
[7:32pm, 11/5/2016] Hawwa: [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 66-70 Wannan rana ba karamar wahala deeja tasha ba shi kanshi sadik saida y tausaya mata, ganin takasa mikewa yasanya sadik kuka gami da bata hakuri itama deejan kuka takeyi ganin jinin da tai a jikinta da bata taba ganiba, haka yaita kokari wajen ganin y gyara deeja, wanka y fara yimata sannan ya gasata a ruwan zafi, takusa awa daya ckn ruwan sannan ya umarceta ta tashi, ckn ikon Allah yaga ta taso nan murna t ishi sadik sbd deeja da kafarta taje daki dg bandaki, d yai zaton ko wani gagarumin abune y sami deejan sabida yaga ranar d yatare d hajiya hakan bata faru g hajiyanba. Albrk d yabo ba irin wadda deeja bata samuba a gurin sadik a wnn safiyar jiyai ashe hajiya fankoce ba abinda yake sha a gurinta sai wahala, yanxu yasan yayi aure d sanin dadin auren,rirutawa d tattali ba wacce bayaiwa deeja sakamakon jinta dayai gargarrrrr d ita ba alamar kwancewar noti,yini yai yana dawainiya d deeja koda tai yinkurin yin wani abun saiya hanata. A bangaren ardo kuwa farin ciki y mamayeshi ganin dan nasa cikin farin ciki da amaryarsa, km yaga har sadik ya kwana 5 baida alamar tafiya birni, yau d la'asar sakaliya ne sadik yaje gaida mahaifinsa, tarar dashi yai a kan dakali yana hutawa, sun gaisa yake tmbyr sa deeja yace lafiya lau take,madallah yace sukaci gaba d hira can ardo yake tambayr sadik yaushe zai koma birni,dammm yai sannan yace inasa rai jibi zan koma, nan ardo yake cemishi inson samune ya tafi da matarsa,yankewa gaban sadik yai ya fadai gami d zaro ido yace baffa ai banida inda zan ajiye deeja a birni nima a shagon abokina nake,ardone yace to yanxu tinda kayi iyali saika kama daki ai,gyara zama sadik yai gami da yar dariya yace baffa kenan kasan kuwa daki a birni tsadane dashi bazan iya biyan kudinba dan albashina ma bazasu isa nai wahalar gida sanna n biya hayaba, ardo yai mamakin jin kofofin d sadik kemasa duk ta inda ya bullo saiya bille kmr mara gaskiya baisan kuwa mara gaskiyar bane cigaba sukai d hira har aka kira sallahr magriba. A wannan daren sadik yaso kara aikata abin da ya aikata a daren jiya saidai y hakura sakamakon rashin samun hadin kai gurin deeja sbd ba karamar gurzuwa taiba dan har lokacin jikinta ciwo yake,duk d haka sadik bai hakura ba saida ya hana deeja ishashshen bacci. Can bangaren kuwa hajiya t gama zaucewa da tunanin sadik, mafarke mafarke d sumbatu b irin wanda bataiba sanadiyyar rashinsa,farin ciki d nisha yai kaura dg gareta,in ka kalli fuskarta zaka rantse bata taba walwala d fara'a ba,duk tafita hayyacinta kamar bata taba tarayya da d'a namiji ba,abinci kuwa bata iyaci ta maida tunani d kuka y zama abinci d abin shanta duk sanida sadik bayanan ni shatuwalle su hajiya har dasu kuka,wannan shine sabon salo tusa a loudspeaker. Da zarar mun hada ido d ita sainai mata alamar taban tausayi da zarar t juya baya kuwa na tintsire d dariyasu hajiya anfada tafkin kogin son sadik shiko yanacan y manta d batunta. Haka sadik y cinye mako guda yana shan amarci har yaji bayason yai nisa d deeja dan yanxu tafiye masa kwanciyar hankali akan hajiya,kuma a ranar yai shirin komawa garin kaduna,sadik d deeja ba irin kukan rabuwar da basuyi dan iya zamansu sun shaku d juna haka y lallabata sukai sallama gami da yimata alkawarin zai dunga zuwa duk sati, gidan ardo ya nufo yai masa sallama tare d sanar masa yanan tafe duk karshen mako,daga nan bai zame ko inaba sai tashar mota. Cikin farin ciki nishadi ya baro mahaifar tasa dan a lokacin yagama tinani da tanadin abinda zai zayyanawa hajiya da zata yadda dashi batare da samun matsala a gurinta ba. Ayushailiasu.blogspot.com [7:14pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 71-75 Tinda sadik y taho deeja take cikin kunci saboda bataso tafiyar sa ba, taso ace koda zai taho sutaho tare gata gashi saidai hakan baisamuba sbd kasancewar sadik baida gaskiya. A cikin mota kuwa gaban saadik sai dukan uku uku yake, fargabar irin hukuncin d Hajiya zata yanke mishi yake kanya farga har sun iso garin kaduna, achaba y tare y hau tare d umartarsa y kaishi gidansu abokinshi salele wanda suke koyarwar guri daya, salele saurayine Mai hangen nasa d zurfin tunani kullum suka hadu d sadik nasiha zakiji yanaimasa tare d tunatar dashi duk wanda y hau motar kwadayi zata saukeshi a tashar wulakamci, kullum yana nuna mishi wadatar zuci ita tafiyewa dan Adam zaman lfy, dariya Sadik yakeyi tare d cewa lallai abokina n yarda har yau a duhu kanka yake, sanadiyyar haduwata d hajiya n keta hazo n ziyarci kasashen laraba harma dana masu jajayen kunnuwa, inci Mai kyau n sha Mai kyau, n kwana a AC, direba y jani a mota, duk wani abun rayuwa danake bukata van rasashi b, sannan kana batun n rabu d hajiya, inma mafarki kake toka farka maganganunka kuma shiga suke suna futa kamar busar iska,zama d Hajiya yanxu n fara, dama zuwanai n sanar dakai nayi aure AURe ,dariya kabiru yayi tare d cewa mutumina wasa kake, n tabbatar hajiya bazata amince K auri wata diya mace a duniya mace aba, murmushi Sadik yayi yace bansanar d itaba, kaikadai n budawa sirrina ina fata zaka rikemin, abin y baiwa kabiru mamaki shidai Sadik yama fara bashi tsoro ,Adduar fatan alkhairi yai mishi d fatan zaman lfy, Sadik y zaro wayarshi daga aljihu y mikawa kabiru tare d cewa ajiya n kawoma, yanda n baka ita haka dan Allah karka kunna, kabiru yace karkasamu damuwa, yanda kace haka zaayi. Sukaiwa juna sallama Sadik y nufi gidan hajiya. Bangaren hajiya Kuwa tin abinnadamunta, harta fara tunanin cewa d gayya habibinnata y kashe wayarsa, inba hakaba kullum saita kirashi fiye d sau 30 ,harsai cajinta y Kare zata hakura d dialling number dinsa, ta dau alwashin cin zarafinsa, tare d alkawarin yanda y wahalar d ita, saita gasashi itama. Ayushailiasu.Blogspot.com [7:35pm, 11/5/2016] Hawwa: [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 76-80 Kwance take bisa lallausan gadonta tayi lamo d ita, idonta a lumshe kmr mai bacci saidai b baccin take ba dan yai kaura dg idonta tunini kawai take ya rayuwar habibinta take, sabida mai ya nisanceta tsahon sati daya, daga sama taji sallama kmr a mafarki, firgigit t juyo gami d sake murje idonta, tabbas b mafarki takeba sadik tagani suna hada ido ya karaso d sauri ya rumgumeta tare d sumbatarta waishi a lallai yana nuna yai missing dinta alot, batasan ya riga ya gama shirya irin karuwanci alalan geron d zai mataba dan yasanta da son a nuna mata salon soyayya kmr wata juliat ko lailah majnoon,abin nemane ya samu matar falke ta haifi jaki tini hajiya ta fara mayar masa d martani, sundau lokaci a haka harsaida suka fita a hayyacinsu,suka lula wata duniyar daban kasancewar hajiya a matse take, saida komai y kammala sannan suka dawo wnn duniar tamu.duk wani cin zarafi d Hajiya tai alkawarin yiwa sadik amma t kasa. Lokacin d suka dawo hayyacinsu ne y karewa hajiyar dake kwance kallo ya rausayr da murya tare d kashe ido kmr dan daudu, kwantowa daidai kirjinta yai yace hajiyata meya sameki naga kin rame? ko rashin lafiya kikai? Marairaicewa tai cikin shagwaba tac haba habibina ba dole na rame ba sabida rashinka kusa dani kasanyani cikin kogin tunani nakasa ci na kasa sha bacci yai kauracen, banajin nishadi da walwala sbd rashinka,tsayawa n zayyana muku abinda hajiya take fadawa sadik na irin kewarsa da tai zaa dau shafuka baa gamaba, take sadik yaji tausayinta gami da bata hakuri ta hanyar cewa shima haka y tsinci kansa sabida rashinta kusa dashi. Wannan ranar hajiya kasa bayyanawa sadik bacin ranta tai na tafiyar da yai har sati daya saboda kawai tanadon ya biya mata bukatarta da tasaba duk dare gashi tai sati guda bata samuba. Sunyi sallar azahar suka nufi dining,ranar abinci ma abaki sadik kebawa hajiya dan ya nuna mata har ynx tana zuciyarsa,amma a bangaren zuciyar tasa ba haka bane deeja ce kwance a cikinta kawai sabida kwadayi dason abin duniya yasa sadik bazai iya rabuwa da hajiyar ba amma deeja tafiye masa nutsuwa yanxu,abinci yake bata suna hira take cewa habibina ai ban taba tsammanin zaka iya kwana daya batare daniba,fuska y canja yace haba hajiyata kinsa ni nakine fa, tace ai abin ne yaban mamaki meya zaunar dake ka barni inata adduar Allah ys lafiya dai,daidai lkcn ya kara kai spoon daidai bakinta t kauda kai alamar takoshi, ajiye spoon din yai ya nisa gami d ajiyar zuciya alamar mara gaskiya shafa keyarsa yai yace wllh hajiya ina zuwa kauye baffa yace dama ni yake jira zanmasa rakiya wani kauye ashe b ranar zamu dawoba, hmmmm tai tace amma ba irin kiran wayarka da banyiba switched off yace wllh service ne babu a garin ,karshema aka sace ta, shiyasa kikaji bankirakiba ,hakadai sukaitayi intace kaza yace kaza,su sadik akwai kofofi kamarta chali har saida yaga hajiya tana dariya sbd duk sanda zai mata magana da alamar raha, wasa da tsokana yake mata.tare d shafo wani sashe n jikinta Palo suka dawo suka xauna sukaci gaba da sheka soyayya dan wani abu d hajiya taiwa sadik batasan ina labe b zaro ido d tsoratar da nai ne yasa biron hannuna ya fadi kasa jikake 'kirrrrr, jin karar ne yasa sadik juyowa nan mukai ido hududashi ya dokan uwar harara d sauri nadau biyona na felle a miliyan ?karyacewa hajiyarsa labe nake musu ta zauneni niko gani yar firit dani kmr allura. Ayushailiasu.blogspot.com [5:04pm, 11/5/2016] A AYSHA: 👱🏻👱🏻👱🏻MIJIN HAJIA👱🏻👱🏻👱🏻 ✍🏻………Written:-Ayusha Iliasu. 👂🏻………Story:-Hawwa Saleh. 81-85 I DEDICATED DIS PAGE TO NAMESAKE AYSHA BAWA( GENTLE) *After 2 weeks* Sadik ne zaune cikin staffroom y hada kai d guiwa ya rasa abinda yake masa dadi sabida yaiwa deeja d ardo alkawarin zai dinga zuwa duk karshen mako gashi yanzu har mako biyu ya wuce baije ba, tinani kawai yake yadda zaiyi, wace karyar zaiwa hajiya ta barshi ya kara xuwa kauye dan yanxu a matse yake yaga deeja,gashi kuma hajiya takasa ta tsare bata barinsa ya sake kamar da, haka y gama tinaninsa har aka tashi baisami mafita ba. Can kauye kuwa Ardo ya tashi hankalinsa sbd rashin ganin sadik gashi har yau alhamis zaa cinye sati n uku baizoba,ardo baiyi kasa a guiwa ba da yammacin wnn ranar ya tashi yaje gidansu a bokin sadik, yana isa ya tarar dashi a dandali suna shan rake, suna kwasar hira d abokansa,takaicine y kama ardo a zuciyarsa yana cewa duba dan Allah gwanin sha'awa yara sunata hira amma nawa dan ya tafi birni yabar mahaifarsa .da yananan da mai zaikawoni gurin wnn yaran, karasawa yai garesu yai musu sallama, cikin nutsuwa suka gaisar dashi y amsa tare d cewa nasiru abokin sadik din yanason magana dashi, gefe suka koma yake sanar dashi zuwa yai don Allah ya kira masa sadik a waya yaji ko lapiya sunata tsumayin ganinsa har gashi zaa cinye mako na uku shuru,take nasiru ya zaro wayarsa dake aljihu y lalubo wayar sadik bugu daya aka cemasa switched off maana akashe take, nan ya fadawa ardo , godiya ardo yai masa tare d rokonsa dan Allah anjima ya sake kiransa sannan ya fadamasa lafiya suna tsimayinsa,amsa masa yai dacewa insha Allah zan kirashi kuma zanzo har gida nafada maka yadda mukai nan sukai sallama ardo ya nufi gida cikin zulumi. Dazarar sadik ya dawo dg makaranta hajiya zata karbe wayar data saimasa tinda y dawo dg kauye, sbd yace waccan ansace, tare d sabon sim card ta kashe, bazaa kunnaba sai gari ya waye zai tafi makaranta ,shima dan tanason ta ringa kiransa ne danjin muryarsa,ace warta wai sadik ba shida wanda zai kirashi a waya inba itaba,balle kuma ta barshi ya fita hira majalisa, hatta jam'in masallaci hajiya ta hana sadik zuwa duk abin duniya ya taru yai masa yawa.maganin Mai kwadayi 😂😂😂,kuda wajen kwadayi akan Mutu. Bayan sallar magriba nasiru ya sake kiran wayar sadik akashe haka y je yafadawa ardo baisamu wayarba, sannan ya kara masa da cewa ya tura masa sako (text message ) inya bude wayar zai gani, godiya ardo ya kara yimasa, bacci a wannan ranar ardo kasawa yai sbd zulumi d tunanin wane hali sadik din yake ciki,abinda yafi damun ardo shine deeja d aka rabo d iyayenta. Yau juma'a sadik ya gama shirin tafiya makaranta, sallama yaiwa hajiya cewa yatafi nan taimasa adawo lafiya tare d cewa habibina kafa kulamin da kanka kasan weekend zaa shiga,karasawa yai yamata kiss gami dacewa angama hajiyata ya fito, yana fitowa bai zame ko inaba sai gidansu salele dan karbo wayar da yabashi ajiya sbd ya manta bai fada masa jiya da aka tashi dg makarnanta ya taho masa d ita yau ba,mamakine ya kama salele ganin sadik ya biyo ta gidansu, sun gaisa yake cewa wayarnan xaka bani, yadda sadik y baiwa salele wayar nan a kashe haka y dakko ya danka masa karbayai yaimasa godiya ya juya yace saika karaso. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: 👱🏻👱🏻👱🏻MIJIN HAJIA👱🏻👱🏻👱🏻 ✍🏻………Written:-Ayusha Iliasu. 👂🏻………Story:-Hawwa Saleh. 86-90 Kunna wayar sa ke da wuya da zummar kiran nasiru ya tambayeshi lafiyar gidansu sakon da nasirun yaimasa a daren jiya yashigo cikn habzari y bude y karanta hankalinsane ya tashi da jin sakon mahaifinsa, tinani y shigayi y zaai ya je kauye ayau ko gobe, duk da sadik bai samu mafitar yadda zai yaje kauyeba ya kira nasiru byn sun gaisa yake sanar dashi yaga sakonsa,dan Allah yaje y fadawa ardo gobe yanan tafe sannan yace masa aikine yai yawa yara sun kusa fara jarrabawane shiyasa baizoba, nan nasiru yace insha Allah zaije ya fadamasa, sallama sukai yaimasa godiya ya nufi hanyar makarantarsu jiki a sanyaye. Wannan ranar sadik kasa tabuka komai yai a makaranta idan monitor tazo tai kiransa saiyace yana zuwa dalibai suita jiransa amma shiru har period din tafita baijeba. Uban tagumi ya zuba a ckin staff room yarasa madafa,salelene ya taso dg gaban table din d yake xaune y karaso inda sadik yake dafashi yai yace mutumina lafiya kake kuwa yau?ko hajiyarce ta tabaka ne? Ajiyar zuciya sadik yai sannan y nisa yace kaidai bari kawai wllh kaga tinda nadawo dg kauye yau sati uku kenan bankomaba km nace d baffana da matata zan dinga zuwa duk karshen mako,gashi yanxu bankoma b harsaida baffa yasa akaimin waya, yar dariya salele ya saki yace to meya hanaka xuwa? Yace wllh hajiyace ta hanani sakewa nan sadik y kwashe duk abinda hajiya tak masa na takurawa y fada mishi,shiru sukai n wani lokaci sannan salele yace sadik ba irin shawarar d ban bakaba game d auren hajiya kashafawa idonka toka kai, ka biyewa son zuciya da kwadayi, ai gashinan dama duk wanda y hau motar kwadayi bazata saukeshi ko inaba sai tashar wulakanci, gashinan kazana MIJIN HAJIA ai. Haushine y kama sadik saboda maganganun salele sun masa ciwo ransa y baci saidai bai nunawa saleleba y daure yace abokina kabani shawara kawai yadda zanyi dan nace afadawa baffana gobe zanzo,tinani salele y shigayi can yace dashi kasan ydd zaai? Aa ya cemasa, yace idan kakoma kacewa hajiya principal yace gobe zaka kai students escortion saboda karatowar jarrabawarsu,kaga dole tabarka kazo kana fitowa saika cale kauye, wani ihu sadik y saki tare d rungumeshi yana nagode d shawararka mutunima suks tafa, tafawar dasu kai tai daidai d kada bell time din tashi yayi sabida ranar juma'ace d wuri ake tashi,wayar daya karba a gurinsa ya mikamar yace ka ajiyen gobe inzan wuce zanzo n karba, dariya salele yai ya karba ya sa a alhihunsa. Cikin murnar samun mafita sadik y karasa gida lkcn hajiya ta dau wanka tana jiran dawowar habibinta, jin sallamarsa ne yadawo d hnkalinta bakin kofa ckn fara'a yaxo y rungumeta, sannu d xuwa taimasa gami dacewa habibina kahuta kaci abinci sai kai wanka zamu fita,zumudine y kama sadik ckn wage baki y amsa mata, kashe ido hajiya tai cikin shagwaba t matso d bakinta daidai kunnensa tace habibina kasan inda zamu?shima cikin shagwaba y matso kusa d kunnanta yace saikin fada hajiyata, tace gidansu abdul zamuje yaronsa baida lafiya zamu je mudubashi amma sai munfara zuwa store an saimusu kayan dubiya, yace to bari naje na watsa ruwan naci abinci sai mu tafi, cikin tsokana tace ko nazo naimaka wnkan, dariya yai yace saidai in kinyarda kisake wankan sai muyi tare,murmushi sukaiwa junansu sannan ya shige daki. Ayushailiasu.blogspt.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 91-95 Fitowa yai cikin milk din shadda dinkin boda wadda akaiwa aiki da bakin zare tai masa kyau yasa bakin takalmi covered, agogon daya sama abin kallone shima black, kallo daya zakai masa kasan ya hadu to d core, yadda fatar jikinsa ke sheki zaka tabbata yana jin dadi sosae,kamshi ne kawai ketashi n designer perfume din d hjy t sayo mishi a london, ya taje sumar kansa d sajensa sun kwanta sunyi liff, duk wata budurwa mai ji da kanta inta kalleshi sau daya zata ji sanshi,sadik kenan yaro dan kwalisa, kamshin tiraren d yake tashine ya tabbatarwa da hajiya cewa angon nata ya hadu, yana karasowa suka kashewa juna ido gami dace masa woawwww habibina, hakika tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wanna sura mai kyau d nutsar da zuciya, gaskiya habibina ka hadu kayi kyau, gaskiya nayi dace da samun wannan halitta kyakkyawa, murmushi ya sakarmata mai dauke d sakonni kala kala yace haba hajiya banda zuga fa har nakaiki kyau? itama murmushin taimasa tace ai habibi tsayawa na lissafama irin haduwar dakai zamu bata lokaci. Lokacin daya tako zuwa gareta ne tai saurin cewa tsaya tsaya dole nadau pix din wannan kwalliyar ko naringa kallonta nasamu nutsuwa,chak ya tsaya yana yar dariya, wayarta ta dakko datake ajiye a gefenta taimasa pictures sannan y karaso y zauna daf da ita. Kallo ta kare masa tace anya kuwa habibina zamu fita unguwarnan?kallonta yai yace saboda me hajiyata?tace jikina yai sanyi ne saboda wannan kyau d kwalliyar daka dauka, dariya yai yace to saime? tace kaga fa har store zamu tsoro nake kar wata taganka taimin snatchin taga dan saurayi hadadde, kissindinta yai yace kin manta ni nakine, aa ban mantaba, yace to kibar wannan tinanin kuma ki rubuta ki ajiye sadik nakine har abada,huggin dinsa tai tace shikenan habibi amma ina tsoron yanmatan yanzu shiyasa banason ka ringa yawan fita waje, dariya yai yace to mutafi ko, tace ai bakaci abincinba yace ai tinda naganki naji na koshi, marairaicewa tai tace plxxx kaci ko kadan ne banason ulcer ta kamaka ko kasha drink, yace to bari nasha drink kawai tare d mikewa ya nufi fridge ya dakko,abin na bawa sadik haushi duk ji dashi d hajiya take bai isa takawo masa abinci ba saidai komai yai da kansa badai taimasa kamar yadda kowace mata kewa mijinta. Niko nace Allah y kara kwadayi mabudin wahala kenan kuma dama inda kwadayi da wulakanci ai kadan ma kagani sadik tafi tafi ma da sannu reshe zai juye d mujiya saika koma MIJIN HAJIA na kwarai. Atare suka jero suka fito parking space din gidan, motar hajiya suka nufa da take rife da tempol, duk irin wannan gayun da sadik yai da kansa ya cire tempol din yasa a boot sannan ya zo y budewa hajiya motar tashiga sannan shikuma je ya shiga drivers seat kasancewar shi zaiyi driving din, tada motar yai tare d yiwa gate man horn ya bude musu lokacin nai tsalle d ihu n kwashe d dariya ?saboda tino sadik danai y gama cire tempol din d aka rufe motar yana karkade kurar da ta sauka jikin gogaggiyar shaddarshi maganin dan iska karen maguzawa kenan, ai dama hajiya tasan sabida kudinta sadik ya yadda ya aureta da batada sisi bazai rabeta ba. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 95-100 Mall suka fara zuwa sukaiwa fauzan son din Abdul shopping din kayan dubiya suka zarce gidan,a tare suka shiga palon sallamarsu tai daidai d fitowar matar Abdul maryam dg kitchen, ganin hajiar su abdul sun jero d sadik ne yasa maryam tai saqare ya jakar gyartai akwanika,kasancewar abdul ya sanar da ita cewa hajiyarsa zatazo ita d mijinta, mamakine ya kama maryam da alamu ydd hajia ta riko hannun sadik shine mijin nata, dan a iya sanin d taiwa hajiya batasan wannsn yaron d sukaxo dashi tareba kuma bata taba ganin mijin d hajiya ta auraba balle ta tantance, dariyar yake maryam ta amsa sallamarsu tare d yimusu iso zuwa ckn palon, ganin sun zauna daf d junansu ko kunya hajiya batajiba a gaban surukarta, yasanya maryam tabbatar d cewa shine angonnata. Har kasa maryam t tsuguna ta gaida hajiya tare d sadik ckn girmamawa suka amsa tare d tanbyr jikin fauzan, kitchen ta nufa ta kawo musu abinci d drink d ruwa, sun dansha drink din sannan suka mika mata kayan dubiya tai musu godiya suka taho, tinda suka taho maryam b abunda take banda mamakin son zuciya d son kuruciya irin ta hajiya data auri dan cikinta dan baifi sa'an abdul ba.dariya tayi a zuci hahahhh tace wannan kece hajiyar gidigo. Acan kauye kuwa bayan sallar juma'a nasiru ya nufi gidan ardo dan ya shaida masa sakon sadik,yana isa kofar gida ya aika yaro ayomasa sallama d ardo,yaron d ya aika ya fito yace yana zuwa, b jimawa ardo y fito, ganin nasiru ne ya sanyashi yin fara'a, bayan su gaisa ne yake shaida masa cewa sadik yace yananan zuwa gobe,jin wannan labari ba karamin dadadawa ardo rai yaiba, godiya yai masa tare d cewa Allah y kaimu goben sukai sallama ardo ya koma cikin gida, yana shiga ya aiki yaron mirigayya ladingo yaje ya fadawa deeja gobe sadik zaizo , da gudu yaro ya tafi ya fada mata,jin yarom yace d deeja gobe babansu zaixo ne ya sanya deeja murna d farinciki nan take ta shiga shirye shiryen tarbar miji. Bayan sallahr magriba sadik d hajiyarsa na zaune suna kallo a palo, gyaran murya sadik yai yace hajiyata tace naam habibina yace gobe in Allah y kaimu principal yace zamu kai dalibai escortion saboda sun kusa fara jarrabawa, shagwabewa hajiya tai tace amma meyasa principal zai min haka baisan weekend likacina bane zaice kuje gobe, gaskiya baxakaje ba kawai kabani number dinsa nakirashi na fadamasa wani malamin ya wakilceka kana da uziri, gaban sadik ne yai mugun faduwa ya zaro idoyace haba hajiyata kinsan harkar aiki b yadda bata kamawa kiyi hakuri baxamu dadeba zamu dawo,dagewa hajiya tai itafa Allahn katafar sadik bazai jeba hakan yasa hankalin sadik yai kololuwar tashi ya rasa yadda zaiyi can dabara ta fado masa, take y fara yiwa hajiya abubuwan da tafiso cikin hikima ya shawo kanta ta yadda zaije. A wannan daren sadik ya farantawa hajiya yadda bata zataba duk dan t yarje mishi zuwa escortion ,dan cimma burinsa n xuwa kauye, saboda haka ya jajirce kasancewarsa gwarzo jarumin namiji irin wanda hajiya takeso don yana biya mata bukatarta fiye d zatonta. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 101-105 8:00 na safe bayan sadik ya gama breakfast ya shirya tsaf , lokacin hajiya n kwance tana bacci bama tasan ya shirya haryai karin kumalloba, nemar gefen gadon yai ya zauna yana karewa haiya kallo tare d tunanin hikimar d zaiyi wajen tashinta yace yatafi, gefen fuskarta ya shafa d lassausan hannu sa da yake ta kamshin perfs take hajiya taji wannan kamshin ya ziyarci hancinta, ido ta bude a hankali taga sadik ne zaune kusa d ita, bude baki tai d niyyar magana yai saurin manna mata kiss take tai shiru, rike kuncinta yai d hannayensa y matsar d bakinsa daidai nata yace hajiyata nifa nagama shiri zan wuce kallonsa tai tace harka shirya d sassafe zaku tafi yace yanxufa 8:30 tayi dandai kina baccine shiyasa kike ganin safiya ce, murmushi tai daga baya kuma d ta tuna sadik fa tafiya zai ta bata rai tace gaskiya habibina dolece zatasa kafita yau kodai kajirani na shirya mutafi tare,wani abu yaji ya tsirga masa a cikin jinansa zarrrrrr sai kawai y daure bai nunawa hajiya firgicin da yaji a zuciyarsa, murmushi ya sakarmata yace kin manta bani kadai bane da dalibai zamu,huggin dinsa tai tace adawo lafiya ka kulamin da kanka kaji habibina Allah y kiyaye hanya, amin yace tare d saurin mikewa ya nufi kofar fita.hamdallah y shiga jerowa a zuciyarsa Yana fitowa bai zame ko inaba sai gidansu salele dan karbar ajiyar wayar, yana zuwa cikin hanzari suka gaisa, salele na cewa mutumina plan dinmu yahau ashe, ajiyar zuciya yai yace dakyar ba ai sai da naci kwakwa kfn ta yadda dan harcewa tai zata boyini ko nabata number principal takirashi,dariya ce ta subucewa salale batare d yai niyyar yiba, karbar wayar yai sukai sallama ya nufi tashar motar da zata sadashi d mahaifarsa. Tin asubar ranar asabar deeja d tatashi tai sallahr asuba bata kara rintsawaba tashiga gyare gyare, ta share dakinta tsaf tare d lailaye gado ta kunna tiraren wuta ko ina y dau kamshi sannan tai wanka ta shirya tsaf ckn riga d skirt n material sun matakyau, abinka d diyar fulani ta gyare gashinta sannan ta zubo dashi har gadon bayanta, nima saida na yaba kwalliyar nan kafin ango sadik y yaba dan nasan baxai ki yabawa ba, guri t nema t zauna ita a lallai tsumayin karasowar sadik take wata zuciyar t raya mata ,"dama ace sadik ya shanyaki yaki zuwa naga y zakiyi safiyar ranar deeja ko karin kumallo bataiba sabida zumudin tarbar ango. 10:30am daidai sadik y sauka a kauyensu,kofar gidan mahaifinsa ya nufa suka gaisa, ardo ba karamin farin ciki yaiba d ganin sadik, nan suka taba hira yake bashi labarin zulumin da suka tsinci kansu sabida rashin zuwansa nan shima ya bashi hakuri d hada karya d gaskiya ya shararamasa,ardo ne ke cemasa amma ai zaka kwana biyu ko? yace masa a'a yau zai juya,fada ardo ya fara yimasa ta inda yake shiga batanan yake fitaba har yana cewa zai hanashi komawa birnin tinda hakane ya xai auro yar mutane ya shalla ya barta, jikin sadik duk yai sanyi dajin kalaman mahaifinsa ya kasa magana, lokacin ardo ya kara d cewa lallai tinda haka zai ringa yi inya shuda ya tafi sai an nemeshi baxai waiwayi iyalinsaba to ya nemi daki a birni ya tafi da matarsa, ganin ran mahaifin nasa ya baci ne yasa ya bashi hakuri tare da alkawarin insha Allah zai nemi daki, sallama sukai ya bashi tsarabar dayayo musu sannan y mike cikin rashin kuzari ya nufi gidansa. Ayushailiasu.blogspot.com [5:05pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. 106-110 Deeja n zaune ba abinda take illah tinanin sadik kardai bazai zoba dan ganin rana tayi har 11:00, kamar daga zama taji sallamar sadik dan ta tabbatar wannan muryar tasace take taji farinciki y mamaye zuciyarta, amsa sallamar tai tare da tasowa ta fito, tana dago labule suka hada ido da sauri ta karasa ta rungumi shi tana mai tsananin nuna farin cikinta sabida ganinshi,kayan hannanusa ta karba tanai mishi sannu d zuwa,hannunsa yasa y tallafo daidai kugunta suka jera daki, suna shiga wani kamshine ya kawowa hancin sadik ziyara take yaji jikinsa ya mutu,lemon da tahada masa d meat pie din d tai dan tanadin zuwanshi ta kawo masa sannan taiwa kanta mazauni kusa dashi, ganin deeja tasha kwalliya y sanya sadik mantawa d maganar da sukai d ardo, bayan sun gaisa yasha lemo d meat pie ne suka fara bayyanawa kansu missin din junan da sukai,a wannan lokacin ne sadik yace dani nafiya naci duk inda yai saina biyoshi ynx d ranar ma zan musu labe d gudu y fatattakoni yace baxan dau rahoton basaidai kuyi hakuri masu bibiyata dan nima dakayar nasha d ya tisoni a dari saidana fadi na kuje guiwa. Jin sadik ya daina sumbatu deeja ta daina yan koke-koke ne yasa na tabbatar komai ya kammala tsakaninsu, cikin sanda nai sadaf-sada nakoma na rakabe dan nacigaba d gashi suya sai ranar sallah ,deeja na hango tana kwance a kan kirjin sadik tana bacci shima baccin yake yi, aikuwa ba inda zan matsa n samu guri n zauna ina jiran su tashi dan ci gaba da gashi. Bayan sallahr azahar ne sadik badan y soba yaiwa deeja sallama dan komawa birni,deeja rasa abinda yake mata dadi tai dan jin sadik yau zai tafi, haka sukai sallama ba yabo ba fallasa a fuskarta,ya damka mata sabuwar wayar nokia Dan su dinga gaisawa, deeja tayi murna d kyautar wayar dya Mata,gidan ardo ya nufa shima yai masa sallama, nan ardo ya kara jaddamasa bukatarsa ta neman daki, gidan su nasiru ya ratse suka gaisa tare da yimasa godiyar isar masa d sakonsa,sannan ya nufi tashar mota. Karfe 4:10pm sadik ya sauka a garin kaduna, gidansu salele ya fara zuwa dan kaimasa ajiyar wayar daya karba, salele ne kecewa har kadawo d wuri haka hararara sadik ya doka masa yace hakane wuri?4:30 takusafa kaga natafi inbaso kake hajiya ta gane ba, dariya salele yai yace angaida MIJIN HAJIA saboda tsabar haushi sadik bai tanka masaba ya juya yanufi gidan iko wato gidan hajiya. Agogon dake makale a dakin hajiya ta kalla karfe 4:30pm amma ba alamar sadik, sakawa da kuncewa tashigayi a zuciyarta tana cewa wannan wana irin escortion ne tin 8:30am har gashi 4:30pm tayi? wata zuciyar ke fada mata anya kuwa ba kauye sadik ya tafiba yau fa asabar ba wani raka dalibai? ajiyar zuciya tai tace lallai kuwa idan hakane zan ci zarafin sadik, zandau kwakkwaran mataki akansa, tana kaiwa nan yai sallama. Ayushailiasu.blogspot.com
[4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 11-15 Soyayya ake t garari tsakanin hajiya d angonta Sadik ,tsawan satin d sukai Sun gurji juna san ransu, hajya jinta take bazata iya rayuwa b habibintaba yayinda shi Sadik Kuwa farinciki y mmayeshi y tsinci kanshi cikin sabiwar duniya d bai taba kisima akwai irinta a doran kasa b. Duk dare sai sunfuta shakatawa sune yau suje nan cin dinner gobe sujecan suci kosuyi takeaway, Rayuwar Sadik t canja baki daya jinsa yake tamkar yafi dukkan mutanen duniya jin dadi. Ana cikin wannan hali dama watan maulidi y kusa hajiya t biya musu ita d habibinta dan suje su yi ummara habawa murna gun Sadik har goya hajiya yayi dan murna tare d zagayawa d ita cikin palour karshe y direta kan gadansu n sunna, a wannan rana Sadik y farantawa hajiya fiye d tunaninta, takara alfahari dashi zamowa miji agareta. Cikin one week suka kammala shiri suka dane jirgi dan lulawa kasa Mai tsarki, cikin jirgi tsoro dik y mmaye zuciyar Sadik jinsa yake tamkar jirgin zai fado sai hirji yakeyi yana ambaton Allah,abinka d farin shiga, fuskantar yanayin d yake ciki yasa hajiya kwantowa jikinsa tana mishi magana kasa kasa tamkar Mai rada, haba swithat ina tare d kai b abinda zai sameka, relaxed nan d yan muntuna zamu sauka, Mutanan cikin jirgin saimamaki suke ganin hajiya n shisshigewa yaro karami wanda baifi saan dancikinta b, ita Kuwa hajiya ko ajikinta, tasanyawa idanunta toka tana balla bushasha tare d warwasawa . Jirgi yayi landing inda akasanar dasu sun iso, hamdala Sadik yayi, mafarkinsa y fara zamowa gaskiya yau shine yazo birnin madina garin manxo yana da Yakinin indai yana tare d Hajiya zai xiyarci kashenshen turai ya dau alwashin zama d hajiya cikin so d kauna tare d sama mata farinciki fiye d yanda take mishi. Sunsauka a masauki, katon dakine Mai dauke d palo d toilet, wanka suka farayi sannan suka kwanta bacci dan rage gajiya d hutawa [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 15-20 A wannan tafiyar d su hajiya sukai sun kara fahintar cewa zama d masoyi b abinda ya kaishi dadi ,shikuwa Sadik yayi experiencing abubuwa d dama, dama masu kudi haka suke enjoyin rayuwa, lallai mutanan kauye Sun zama sorry, yakara kyamar talauchi d talaka ,kaji karfin hali shida arxikin yakeci amma y fara gudun talaka. Hajiya ta kashewa Sadik manyan kudade d ta bashi tsoro duk wani abu d ya bukaci tasai mishi bata nuna gazawarta . Bayan dawowarsu gida Nigeria, hajiya t Bukaci Sadik daya ajiye aikinshi, ita aganinta wahala yakesha, tinda yana tare d ita, babu abinda Zai nema ya rasa, tinani y shigayi n ganin cewa anya hakan Kura hanyace Mai bullewa, yasha matukar wahala kan Allah y taimakeshi y samu, yasha yin kwanaki batare d yaci wani abuba duk sanadiyyar rashin aikinyi, cikin fargaba yace hajiya ni aganina ai aikina bazai zamo takura gareniba tinda n rigada n saba shekara d shekaru, hajiyance t batarai tashiga yin fadace fadace, danma inasan taimakonka n rabaki d talauci d wahala shine zaka badan kasa a ido too shiknn, t nuna alamun yin fishi, hankalin Sadik yayi kololuwa wajen tashi ganin y batawa hajiya rai, kusa d ita y dawo y fara lallashinta d kalamai masu nutsar d zuciya, y fara zolayanta d kalamai dadada da suka sanyata dariya harda kyakyatawa hajiya macece dakesan agirmamata a kuma kambamata, shikuwa Sadik y lakanci abarshi dan haka yake binta yanda takeso. Rayuwar jin dadi suke gudanarwa, indai b Sadik aiki y futaba too suna tare d Hajiya,duk tafiye tafiyen d takeyi kasashen waje dan saro kaya tare suke zuwa, kafarta kafarsa, shike daukar mata jaka d sauran kayayyakin bukata,duk wani aiki n wahala d hajiyan y kamata tayi y dauke Matashi [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 20-25 Yau kimanin wata shida auren hajiya d Sadik, kullum Sadik y kwanta bacci mafarki yake d ardo, tinyana sharewa har abin y komamai jiki duk dare sai yayi. Acan kauye Kura ardo yashiga halin kunci rashin sanin takamaimai halin d dannasa yake ciki, ba abinda yafi daga Mai hankali illa yayanshi, kullun basu d zance saina mahaifinnasu, abinda yafi daga hnklin ardo shine tin tafiyar Sadik birni bai taba shafe wata biyu baizo garesu ba, amma gashi yanxu har kusan wata bakwai, jikin ardo yayi samyi addua y shigayi Allah dai yasa lafiya, kullum cikin baiwa yaran hakuri yake tare d cemusu insha Allah yana nan zuwa ya ganku. Tunani yakeyi wacce dabarar zaiyi dan hajiya t kyaleshi yaje koda kwana dayane yaje y dawo, suna kwance yai gyaran murya yace hajiyata, farincikina, abar alfaharina, guda tamkar d dubu gareni, habawa nan hajiya taji wani farinciki y mamayeta tare d washe hakora, ya kara d cewa ranki y dade inaso zanje gaida kanin baffana dazu akaimin waya baida lafiya, hajyance tace to ai b matsala yaushe kakeso muje? gabansa yajji ya fadi, y kara d cewa ai ina tunanin b sai kinjeba tinda kinada abubuwan yi d yawa, ba wani dadewa zanyiba kwana biyu kawai zanyi, hajiyance tace habibina yanxu kana tunanin zan iya yini batare d Kai gefenaba balle kwana har biyu,inma mafarki kakeyi to ka farka hakan b mai yiwuwa bace, ai bazan iyaba sai ciwo y sameni, kaka tsara kaka, ya kara d cewa To shiknn zanyi kwana daya sai n dawo, hajya tace aa kafata kafarka, shiru yai yana tunanin ai bama zai taba yiwuwa yatafi d Hajiya, balle har y gabatar d ita g ardo matsayin mata, abune wanda ba Mai yiwuwa bane, inbaso yake ardo y tsine Mishi b, yace har yakai yayi aure b tare d saninsuba,da kyar y shawo kan hajiya t abari nan gaba saje tare amma yanxu zaije ayini daya y dawo, nanne fa hankalin hajiya y dan kwanta tare d murmushi a fuskarta ,bata kawo komai azuciyartaba, tace yawwa habibina har hankalina y kwanta, sai K musu tsaraba kace injini kannazo gaidasu har gida, yake yayi tare d cewa angama ranki shi dade, dubu ashirin t bashi tace yai musu tsaraba, dubu goma kuma y rike saboda halin hanya [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 26-30 D sassafe y tashi, dokin san y je yaga yayanshi d mahaifinshi, baccin safiya ma ayau gagarar shiyayi har hajiya t gane irin farincikin d yake ciki tamkar wanda yai shekaru baije ba, misalin karfe goma yaiwa hajiya sallama Dan tafiya, sai hajiya tace habibina kodai nataso mutafi banasan kayi nesa dani zanshiga tunanin,yace ai mungama magana tinjiya hajiyata tace to ko da direba zaku tafi dan hankalina zaifi nutsuwa,cikin dabara y karaso kusa d ita yana cewa haba hajiyata kikwantar d hankalinki indai nine Sadik namiki alkawarin nakine kedai har abada, dadine y kara lullube hajiya, kiss tamishi a kunci sannan tace safe journey. Fitar shikeda wuya kasuwa y shiga dan sayawa mahaifinnasa shadda hade t takalmi d turare, d turmin zani guda biyu dan adinkawa yayansa takalma d yari d dankunne saboda gabatowar karamar sallah, y hada d yan tsince tsincen d zai rarrabawa yan uwa, tsarabar da bai taba yi ba tim zuwansa burni, atasha y kara musu d biredi d kuma gugguru( popcorn). Mota ta daga misalin karfe daya ya isa mahaifarshi, wani dadi yaji hade d farinciki tamkar wanda ke dauke d kayan nauyi axuciya aka saukemai, ,ardo yayi farinciki d ganin dannasa saboda farinciki har kwalla yayi tare d cewa yanxu Sadik abinda kayiwa yaranka ka kyauta katafi tsawan wani lokaci b aike b zuwa, aikoba komai ganinka ko aiken gaisuwa zai sanya hankalinmu y kwanta,a halin yanxu tsufa y kamani yaci ace kana waiwayo gida,inba mutuwa akwai larura kosokake sai ance n mutu zakazo, ardo cikin goge kwallar Data kara zubo masa y kara d cewa duk laifina dana bari katafi batare d nasamarma iyali anan ba, da kanada iyali dole K dinga waiwayomu, Sadik ya shiga bawa ardo hakuri tare d karyar cewa yayi ciwone wanda y kaishi harda kwanciyar asibiti,n tsawan lokaci shiyasa baizoba ,y baiwa ardo hakuri, tare d alkawarin insha Allah hakan bazai kara faruwaba, duk cikin yayan ardo yafi ji d Sadik kasancewarshi y rabu d mahaifiyar Sadik din tin yana kankani, Sadik y sha wuya gun Matar ardo hinde kanya girma, duk cikin yayan ardo Sadik yafi mishi biyayya shiyasa yake kewar dannasa, ardone ya aika cikin gida akira Mishi yaran Sadik, suna futowa sukai ido biyu d abbansu habawa d gudu suka karaso wajen d yake zaune suka haye kanshi suna murna d farinciki, uba d yaya sai allah ,shima murnar y shigayi ganin yaran Sun fara girma, mita suka shiga yimasa abba ka tafi K barmu, dan Allah abba inzaka tafi zamu bika, shiru kawai yayimusu, tare d tanbayarsu bayan rabuwa, duk suka gaya mishi irin azabar d matar ardo ke musu, kuma ardon baida bakin d zaimata magana, ya shiga gida Sun gaisa d matar ardo, b laifi t amsa b yabo b fallasa sabanin d dabata amsa gaisuwarshi, gaskiyar bahaushe d yake cewa kowa y bar gida ...........,duk d irin daular d Sadik yake ciki sai yaga zama d iyaye, yaya da yanuwa b abinda yafishi dadi Ayushailiasu.blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 31-35 Sun zauna suna hira d ardo nan yake sanar d ardo cewa ayau zai juya yatafi, abin y daurewa Ardo kai, gyaran murya ardo din yayi yace sadiku sai kace Wanda ake kora, duk d tsawan lokacin daka dauka bakazoba shine zakace haka, kasa yayi d kai yana cewa walhi ardo aiyukane sunmin yawa, dayake yanxu anmaidani babbar sakandari ta maza bakamar d, danake a firamare ba, Ardo yace too b laifi Allah y kara daukaka, ya dauko tsarabar daya kawo ya bawa ardo tasa tare Data yaranshi, yabawa matar ardo hinde mayafi, malam yayi farinciki d wannan tsaraba tare d yiwa dannasa Adduar samun nasara a rayuwa. Ardo ke tanbayar Sadik tinda ayanxu kana d jinjinar sanaa yakamata ace ka ajiye iyali, gabansa ne y fadi daya tuno d Hajiya, cikin in ina ta mara gaskiya yace e e e ardo in insha Allah zan yi kokarin n nemo innakoma, dariya ardo yayi irinta manya yace Sadik agida nan kauye nakeso ka zabi yar uwarka bafulatana konina zabarma kamar wancan karan, gumine y fara tsattsafowa Sadik jin ardo yace zai zabar mishi mata,y shiga uku dan inhakan t tabbata baisan wana hukunci hajiyan zata yanke mishi dawana idan zai kalli hajiya yace mata zai kara aure, kaka tsara kaka dinfa kenan. Lokaci daya yaji cikinsa y kurda, yana d bukatar zagawa amma haka y daure suka ci gaba d magana Shirun dayai ne ya sa ardo cewa too tinda yau zaka koma b batun kazaba, Da zaka kwana zuwa gobe kasuwar garinnan zataci saika zaba cikin yammatan garinnan anma yanxu na dau nauyin zabama, zannema ma yarinya Mai hankali d nutsuwa, Allah yaima albarka ,abinda nakeso dakai nan d karamar sallah ya zamo katanadi duk wani abuna bukata dan gudanar d auren,zan tura komai d ake bukata kafin zuwanka, godiya y shiga yiwa ardo, badan xuciyarshi tayi na am d hukuncin ardon ba Y zaga gidajen yanuwa d abokan arziki, karshe yayima ardo sallama ya dauko hanyar dawowa kaduna cikin kasala d rashin walwala sabanin yanda ya tafi, misalin shida y isa gidan hajiyarsa, a bangaren hajiya wunin ranar cikin rashin walwala tayi n kewar habibinta, jitake dama tabishi sunje tare, jitake tamkar bazai dawoba, jin sallamar shiyasa tai ajiyar zuciya, tare d amsamushi, oyoyo habibina tashiga fada, welcm back. Ayushailiasu.Blogspot. Com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 36-40 DEDICATED TO ABEEDA (HUMAIRA B NOVEL GROUP) Hajiya tayi murna d dawowar Sadik Matuka jitake tamkar ta goye shi dan murna, tataimaka mishi y rage kayan jikinshi ya fada toilet danyin wanka y rage gajiya. Sadik y shiga halin damuwa, tunani yakeyi n makomatshi inhar hajiya taji abinda ardo ke shirin kullawa babban tashin hnklinshi d hajiyan batasan hayar iyaye yayi aka daura musu aure ,abin duniya y taru yayi mishi yawa, yarasa mafita gashi tinda y auri hajiya y rabu d dukkan abokanshi shi a ganinsa wai yafi karfin ajinsu ayanzu kinga d ko shawararsu y nema dansamun mafita. Karshe ya yanke shawarar sanar wada hajiya danta samar Mai mafita, wata zuciyar ke gargadinsa Sadik K rufawa kanka asiri inbaso kake hajiya taci zarafinkaba, yanda take jida kai ,aibazata so taga wata mace ta rabeka ba. Sadik y shiga damuwa matuka, y shiga yawan tunanin d yasanya hajiya t gano yana cikin matsala, tanbayarshi ta shigayi habibina lfy KuWA, naga tinda kaje qauye ka dawo baka cikin nutsuwa, koduk rashin lafiyar baffannaka ne ya sa haka,yake yayi tare d cewa ko daya wallahi hajiyata, kamar y gaya Mata saikuma y waske yace wallahi ardone yace lallai yanada bukatar wasu kudade daga gareni zai siya wata gona nikuma a yanxu b kudi hannuna, murmushi tayi tare d cewa haba habibi dan wannan yar matsala kankanuwa saika nemi hanamu kwanciyat hankali, nawa ardon keda bukata? Yace dubu dari biyune ba yawa, hajiyance tace ai kafi karfin komai agurina kofin haka ardo y tanbaya ni Mai iya badawane duk sanadiyyar kaunarka Da nake ka futar damuwa a ranka duk randa K shirya zuwa K sanar dani sainabaka saboda murna baisan lokacin d ya yi hugging dinta, soyayi y dagata yayi juyi d ita cikin palon amma kasancewarta lukuta ya kasa koda dagata, yayi yayi amma ina, y gagara abinka d dan santolo l Ayushailiasu.Blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 41-45 DEDICATED TO MARIYA AHMAD ILIASU Tindaga wannan rana sadik y rage nuna damuwar d yake ciki gaban hajiya, gefe daya yana murnar kyautar kudin d hajiyat zata bashi, tin tsawan rayuwarshi bai taba rikesu a dunkule lokaci gudaba. Yagamayin budget din yanda zai sarrafa kudin, dama akwai yan kudade a hannunshi, zai hade su yayi hidimar biki sannnan kuma y kara gyare dakin d marigayyiya tsohuwar matarshi tazauna ciki dan amaryar t zauna, dan bazai taba zuwa d ita burniba balle asirinsa y tono agun hajiyarshi Akwana atashi b wuya bangaren hajiya jinta take tafi kowacce mace saa a duniya tinda ta mallaki santalelan saurayi sankowa kin WAnda y rasa, burin hajiya ace yau t samu ciki,t haifi diya macen da zatayo mahaifinta. yau ne akatashi d azumin watan ramadan, kuma sadik yanasane d cewa ardo yace ana sallacewa zai mishi aure, ranar d azumi y kai shabiyar y Sanar d Hajiya cewa zaije yiwa su ardo sannu d shan ruwa, ta hada mishi goma shatara t arziki, buhun shinkafa dana gero d sikari d wake d Mai da turmin xani d shadda yakaiwa su ardo, tsoro kayan suka baiwa Sadik yace hajiya ai sunyi yawa, amma sai cewa tayi kafi gaban haka gareni, dukiyata duka zan iya salwantarwa dan samarma farinciki, hade d jimillar kudi dubu dari biyu, kasuwa yafara zuwa y hada lefe daidai gwargwado irinna mutan kauye, tare d yin tsaraba, tasha y nufa, yai sa a saura mutum daya mota t cika yana shiga mota t daga sai mahaifarsa.ardo d yaranshi sunyi farinciki d zuwan Sadik din. Ayushailiasu.Blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 46-50 DEDICATED TO MRS JEE (Allah y kawo Baby muzo musha suna Cikin sakin fuska d nuna tsantsar farincikiy ya tarbi dannasa, tare d tambayarshi aiki d abokan zamanshi, Sadik yace duk suna lfy,sunmace agaisheku. Y gabatarwada ardo dukkannin kayan d y hado n hidimar auren tare d kaiwar d Hajiya t bawa yakai injita, amma sai yace d ardo awajen aiki aka rabamusu kayan abinci n azumi, ardo sai godiya yake, y kasa rufe bakisaboda murna, a hsashen d yake akalla kayan abinci zasukai mishi wata shida kofiye d haka. Bayan y dan huta ardo ke sanar dashi matar d ya zaba Mai, shiru Sadik yayi tare d sunkuyar d kai nuna alamun biyayya, fargabarshi Allah dai yasa b adangi ardo ya saboo mishi matarba gudun tonan asirinsa, ardo y cigaba d cewa b wata bace illa deeja kanwarka yar wajen kanwar mahaifiyarka, gabanshine yai muguwar faduwa, bai so haka, amma bashida zabi saina amincewa, tare d kara yiwa ardo godiya. Kamar yanda ardo y tsara ankai kayan lefe d sauran kayayyaki n bidiar auren fillo, ansa biki sati uku masu zuwa, ardo y barwa sallahun jigilar d dawainiyar gyaran gurin d amarya zata tare. Yaje ya ga deeje ,b laifi yarinya ce kankanuwa wadda batafi shekara 15 ba, amma kyakkyawar gaske, idanuwanta su sukafi daukan hankalin Mai kallonta kasancewarsu dara dara kuma sexy, sai pointed noise d dankaramin bakinta, kirjinta cike yake Da dukiyarsu t fillo, doguwace, gata d shiru shiru, magana ma bata dameta ba, ba laifi y yaba d ita, amma hankalinsa n kan hajiya Da irin wadaka datake ,d ace babu auren hajiya kansa, yasan zaiji dadin zama d deeje kasancewarta Mai tarbiya d kawaici. Ya tanbayeta irin abubuwan d take bukata n game d aurennasu, kunya t hanata cewa kanxil, kuji yarinya Mai tarbiyya " sabanin yammatan wannan zamani wanda kan saurayi y fara tambayarsu abinda suke bukata su yi masa dogon lissafi " Ganin bata d niyyar cewa komai yasa y bata daidai karfinsa , yaimata sallama kancewa gobe zai koma birni kan bakin aikinshi. Ayushailiasu.Blogspot.com [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 51-55 DEDICATED To AYSHA BAWA Sunyi kwanan hira d ardo, inda y dinga bawa ardo labarai n mutanan burni d irin zamantakewar rayuwarsu, ardo Kuwa jiyake d Da hali d zai fiso Sadik yabaro birni y dawo kauye su cigaba d rayuwarsu, saboda yanajin dadin zama d dannasa, amma yasan hakan b abubane Mai yiwuwaba. Sadik y sanardashi gobe zaikoma saboda yawan ayyukan d ya baro. Washegari yazaga gidajenyanuwa, yaiwa ardo alkawarin yana lissafe d ranakun d akasa, insha Allah cikin satin zai zo dan ayi shaanin biki dashi, ardo yaso Sadik y dauki hutu koda n satine saboda bikin amma yasan hakan b mai yiwuwa bane, haka sukai sallama y baro kauyen. Tinda y cika umarnin mahaifinshi y tsinci kansa cikin matsanancin farinciki, yadau alwashin kan cewa bazai taba barin hajiya t gano auren d ardo ke shirin yimasa, sun cigaba d gudanar d rayuwarsu kamar yanda suka saba shida hajiyarsa, duk wani abu d yake bukata kan y furta hajiya t gamayimai, y manta d wani abu waishi talauci ,direba kekaishi aiki y daukoshi, yaso hajiya ta saimishi mota, ta mishi alkawarin insha Allah akwai kudadenta da take tsimaye, suna futowa inshaa Allah zata saya mishi Akwana atashi b wuya, shirye shiryen bikin Sadik d deeje y kankama, ardoma y kammala gyarawa amarya sashen d zata tare, abangaren Sadik Kuwa y shiga damuwa, wacce karyar zai yiwa hajiya danta barshi yai kwanaki koda biyune. Suna kwance, bacci yama fara daukan hajiya, yadan bubbuga hannunta, tare d cewa hajiyata, cikin magagin bacci tace na am habibi ya akai, yace dazu ardo y kirani, yake sanar Dani lallai lallai gobe naje yanada bukatar ganina, mutssike idanuwa tayi tare d mikewa zaune tace inceko dai lfy habibi, yace tonimadai tinda y kirani n kasa samun nutsuwa, addua t shigayi Allah dai yasa lafiya, yakara d cewa inshaa Allah d asuba zanyi sammakon tafiya ,hajiya cikin tausayawa d jimami tace Allah y kaimu asuban fatana dai Allah yasa lafiya, yace amin.ganin t amince d batunnashi hartana Addua Allah yasa kiran n alkhairi yaji dadi aranshi, cikin nutsuwa y shirya, d kanta takaishi hartasha tare d bashi kudi y zuba a aljihu saboda bukatun d kantaso b shiri wannan ai shine MIJIN HAJIYA Ayushailiasu.Blogspot.com [5:36pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 55-60 I Dedicated this page to Sistr jidda (Admin hausa novel group 1) Ardo yayi murna d zuwan dannasa akan lokaci, ko ina ka juya wasanni ake gudanarwa kofar gidan ardo n murnar auren sadik. Ansha shagalin biki sosae inda y banbanta da wancan auren nasa kai hatta bukukuwan da akeyi a garin wannan y banbanta dashi saboda wayewar da sadik yai a birni da irin kaya da kudin d aka kashe,duk inda ka zaga a kauyen ba abinda ake sai maganar bikin sadik da irin shagalin da akai. Daren ranar juma'a aka kawo amarya kasancewar anriga an daura aure tin bayan sallahr juma'a,aladar garin ce randa aka daura aure ranar ake kai amarya sannan kashe gari ayi budar kai da jere da daddare a raka ango dakin amarya. Bayan anyi budar kai da daddare abokan sadik su biyu suka rakashi daki amarya andan taba hira sanna sukai addua d fatan alkhr, suka kara yiwa sadik nasiha akan hakkin aure duk d sunaan ba auren fari ne gareshi ba, yaji dadin adduar d nasihar sannan ya rakosu bakin kofa sukai sallama yai musu godiya suka tafi. Deeja tinda suka shigo tsoro y darsu a zuciyarta, jikinta yai sanyi,takurewa tai a bakin gado lkcn d yashigo y umarceta tasaki jikinta danya lura d yanayin da take ciki, ckin lallami yashawo kanta har sukaci abinda ya shigo dashi n amarci, ganin tsoron d deeja keciki ne ya sanya sadik daga mata kafa badan yaso ba, hira suka fara tabawa gyangyadi ya fara daukar deeeja,ganin hakane ya sa sadik umartarta dataje t kwanta. A wannan daren bacci barawone y sace sadik badan yasani b saidan kogin tunani d kewar hajiyarsa da yakeyi d tunanin irin karyar d zai mata yasamu mafita a gunta, itakuwa deeja baccinta take bilhakki batamasan yanai ba wai kunu a wani gida,dg karshe tunani yazo masa ya kashe wayarsa ydd hjyar zatai ta kira a kashe inyaso inya koma ta tambayeshi sai yace mata tafiya sukai d Ardo kuma kauyen da sukaje ba service shiya ya kashe wayar. Jin kiraye kirayen sallahr asuba ne ya farkar da sadik, cikin hanzari ya mike gami d ficewa ya dauro alwala sannan y dawo ya tashi deeja datake shara baccinta dan tayi sallah, yana fitowa bai zame ko inaba sai masallaci,bangaren deeja ma tana tashi alwala ta dauro ta dawo daki t gabatar da sallahr asunba,zama tai inda tai sallah dan jiran shigowar angon nata amma shuru takeji kmr an shuka dusa,shikuwa sadik daya fito dg masallaci bai tsaya ba sai a kofar gidansu dan ya gaida mahaifinsa. Lokacin da gari yai shaaaaa (yai haske) deeja t muke tanufi bandaki danyin wanka,fitowarta dg bandaki tai daidai d shugowar sadik da gudu ta karasa daki tai maza ta zura hijab dinta sbd daurin kirjin datai wai a lallai ita kunya dariya abin y baiwa sadik a zuciyarsa yace ni danake d hajiya harda wani abu d mace zata boyen, karasawa dakin yai yana tsokanar deeja d cewa dan kin ganni kike gudu harda sa hijab to kwalliyarma ni zanyi miki naga tafadi wai kwarkwata ta kada kudi ido ta zaro tace aa kayi hakuri zanyi d kaina, yace to meye na gudu dan kin ganni? bakomai tace masa yai dariya yace to ayi kwalliyar nagani, lkcn ta rissina tace masa ina kwana? ya amsa da lpylau amaryata, murmushi ta sakar masa wanda saida hakoranta suka bayyana tare d dinful dinta kyanta ya kara bayyana a gareshi take yaji kauna d kwadayin son y kasance d ita ya kamashi. Shiri tsaf tayi ckn atampha riga d zani sunyi mata kyau, tayi kwalliyarsu irin ta fulani wdd takara futo mata da dogon hancinta d dara daran idanunta, duk ji da birnancin da sadik yake saida ya yaba kyan da tai, tsam y taso dg mazaunin da yake ya dawo kusa d ita y zauna, lkcn d ya janyota jikinsa ya matseta ta saki wata yar kara sbd jin zarrrr wani saban yanayi dataji yana yawo ckn jininta,cikin kidimewa sadik ke tambayarta lafiya,kallanshi tai d sexy eyes dinta take yaji wasu sakonni suna shiga jikinsa, jin sallamr yaron d ardo ya aiko ya kawo musu karin kumallo ne ya katse su dg kallon junan dasuka dau lokaci sunayi. Ayushailiasu.blogspot.com
[3:33pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIYA … Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa saleh. Page 1 Sadik ne cikin rawar jiki yake yiwa hajiya barka d zuwa, jikinsa sai bari yake tamkar mazari ,ko kallo bai ishi hajiyan ba ,balle t amsa mishi, mafici ya dakko yana mata fifita dan rage mata zufar d take, kasancewar lokacine na zafi, rana ta kwalle, tare d cewa ranki y dade bari akawo miki abin jika makoshi naga kamar agajiye kike, batare d tace komai b ya mike yanufi fridge din dake dakin ya dauko pure water hade d maltina y dire a gabanta,kokarin balle murfin yake, ta daga mishi hannu dan dakatar dashi tare d cewa banida bukatar sha. Mayarwa yayi y ajiye tare d neman guri kasan carpet y zauna, itakam ta hakince kan Two seater. Sun dauki tsawan lokaci a haka sannan tace ina abinci, inafata ka gama, nan sadik y tuna cewa y dora abinci a kitchen cikin sauri y mike y nufi madafin dan dubawa amma ina shinkafar t gama babbakewa, gumine y fara tsattsafo mishi gudin bala'in hajiya dan yasan bazata ragamishi ba, watakila abin ba'a masifa d balai zai tsayaba karshe ta mishi abinda tasaba. Muryarta yaji tanacewa yanake jin kaurine a gidan, kitchn din t karaso, cikin kunar zuci tace ohooo saboda bakasan zafin nemaba, shiyasa ka barmin abinci a wuta har ya kone,to wallahi saika biyani, a albashinka nawannan watan saika bani dubu goma n almubazzarancin dakayimin d abinci, dago kai yai cikin matsanancin tashin hankali bakina rawa yace hajiya dan girman Allah kiyi hakuri yanxu xankara dora wata, kimin afuwa kinsan albashin nawa dududu baifi dubu talatinba, inkika dauki dubu goma ai kudin sunkare dame zan biyawa yayana kudin makaran…………… kanya karasa ta katse shi da hanyar cewa rufemin baki mace kawai, sunan anhalicceka cikin maza amma bakada wani katabus lallai ka tabbatar kanna futo daga wanka ka dafamin wani abincin, kafara wucewa ka hadan ruwan wannka, tsaki tayi tare d juyawa t bar Kitchen din. [4:40pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 2 Toilet y shiga tare d hada mata ruwan wanka, showwer cream d soso d sauran kayayyakin wankanta ya kaimata, zuwa yai tare d rissinawa yace ranki y dade angama,Hannuta daga mishi alamar taji. kitchen y koma kan wani lokaci yagama hada mata jalop din spaghetti, kaji wata masifar magidanci a kitchen. Da kanshi yai serving dinta, tagamaci y kwashe y maida kayan Kitchen ,side table din palon tadan taba d hannu saitaga kura t biyota, tace sadik anya yau ka yi mopping palonnan Kuwa yace eh walhi hajiya kina fita nayi, ta ce to bai fitaba akara, batare d yace komaiba y mike y hado ruwan kumfa d klin yafara cika umarnin hajiya. Dare nayi suka nufi makwanci, hajiya t gama shirin bacci ta baje kan sofa dake kan gadan iskar fanka n ratsata, dalilin d yasanya takasa rabuwa d sadik daya ne kasancewarshi gwarzon namiji a makwanci, duk d tarin dukiyar datake d ita, amma ta ke aurenshi, macece mabukaciya b kowane namiji bane zai iya d itaba, amma Sadik yana kokari wajen biya mata bukatarta, can gefe yake kwance kan katifarsa d pillow, muryar hajiya ce tafara kiranshi habibina, bacci y dan fara daukanshi baiji kiranba ganin tayi har sau uku b amsa, yasa ta taso d kanta ta iso gareshi kan katifar, cikin bacci yaji alamun hannu n shafashi, abinka d me nema, b shiri y bude ido yai kwalli d hajiya, dama a ka'ida saidai ita t bukaceshi amma shi baida wannan damar duk d kasancewar shi miji gareta. [4:41pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 3 SANARWA Ina sanar d ma'abota karanta novels dina, ansamu canjin sunan littafinnan daga mijin tace zuwa mijin hajiya, asanadiyyar cewa, wata yar uwa tayi shi abaya. Yayinda bukatar hajiya ta tashi idanuwanta rufewa sukeyi ruf, bata nutsuwa sai ta cimma bukatarta, duk yayin data bukaceshi baya iya musa mata badan komai b saidan bayasan abinda zai bata ranta tai fishi dashi harya kai ga rabuwarsu, shi dai Sadik Allah yayishi mai san abin duniya, cikin zakuwa yai magana yace ya akai hajiyata, ita kuma t washe fararen hakoranta tare d mishi rada a kunne murmushi yayi tare d mikewa suka koma kan gadon mulkinta, hajiyar ta rigada tasan dan abun hannunta Sadik din ke shanye dikkanin cin kashin da take Mishi ,yayinda bukatar hajiya t biya Kuwa zata sallameshi y koma makwancinsa bata damu d tasa bukatar ba, nan bacci nannauya zai dauketa ta saki lebe da saleba taita gwauron munshari shikuwa yayi kasake yana juyi baccin ya gagari idanunsa. Da asubar fari d yaji anyi kiran sallah zaimike daga kan katifar shi,ya nufi bayin dake palo dan dauro alwala,saboda hajiya ta mishi kashedi tsakaninsa d bandakinta sai wanki, danbata yarda t hada bandaki d bawantaba acewarta, kujiyemin tabaya ta rago. Sannan ya dawo daki cikin dabara zai dinga dan bubbuga Mata kafa gudun karta tashi d Ciwonkai t balbaleshi d bala'inta ,sai y tabbatar t bude idanu sannan zai nufi masallaci danyin sallah. A kullum idan hajiya t tashi tashiga toilet dukkan wani kaya n jikinta nan zata ajiyewa Sadik dan y wanke mata, daidai d pant, bra d sauran kananun kayanta shike wankewa tinda t aureshi t sallami dukka yan aikin d ke gidan. Shikuma Sadik dayake mutumin kauye ne, baisan wata rayuwa t wayewa ba sai haduwar shi d hajiya, matar shi dasukai auren fari yar garinsuce, bata taba zuwa binniba koda d ziyara, irin aurennan n ladan noma akai musu dan haka baisan jin dadi n zaman aure b saita sanadin hajiya. Hajiya samira macece Mai ji da gayu, Mata ce agun Alhaji bello naira, shahararren dan kasuwa dake zaune garin kaduna, yaransu biyu maza Allah yai mishi rasuwa sanadiyyar accident, bayan sadakar bakwai akai musu raban gado hajiya ta samu wawayen kudade d sukaso zautata, kasancewarta mace tilo ga marigayin, yayanta Kuwa kowanne ya gama karatu harma Sun ajiye iyali a wannan lokaci. [4:41pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA …Written:-Ayusha Iliasu. …Story:-Hawwa Saleh. Page 4 SANARWA Ina sanar da ma'abota karanta novels dina, ansamu canjin sunan littafinnan daga mijin tace zuwa mijin hajiya, asanadiyyar cewa wata yar uwa tayishi a baya. Sadik farine dogo Mai fadin kirji, yanada suma wadda ta kwanta a kanshi d fuskarshi,sajanshi ya kara Mishi kwarjini, inbaiyi maganaba zato zakai wani balarabe ne, yazamo mutum Mai tsafta baisan kazanta kokadan shiyasa zaka ganshi neat koyaushe ko yanmatan birni ne suka ganshi sa kyasa. Asalin Sadik bafulatanine usul gaba d baya, tin yana yaro iyayenshi suka fahinci yanada basira danko makarantar allo sukaje in anyiwa yayyanshi karatu basa rikewa sai kaga suna tanbayarshi y maimaita musu karatun in andawo Gida, baffanshi yasanya shi a makarantar boko t garinsu ,yazamo yaro Mai kokari yana zuwa n daya, bayan Sun kammala firamare sai ardo yace bazai barshi y cigaba d karatuba ya dawo su fantsama kiwo wanda y zamo shine gadansu iyaye d kakanni, d kyar shedimastan makarantar y samu nasarar shawo kan ardo y amince Sadik y cigaba d karatun sakandire a makarantar maza ta gwamnati dake garinnasu, kasancewar makarantar t kwanace inya tafi baidawowa sai anyi hutu, sannu a hnkli a kwana atashi shekara shida suka kammala karatun, komawarsa gida yasa ardo koya Mishi dabaru n kiwo tare d bashi tsatsiba d surkulle irinnasu n fillo, dan yanaji ajikinsa nan gaba dannasa zai zamo gwarzon namiji a fagen kiwo, wannan lokacine ardo ya zaba Mishi yar abokinsa Mai suna ladingo ya auramishi. Sun zauna lafiya d ladingo harta haifamishi yara uku duka Mata, agun haihuwar n hudu rai yai halinsa, a wannan lokacinne Sadik yaga zaman kauye ya daina mishi dadi, kullum y kwanta bacci mafarki yake d birni, wai gashi cikin wani tankameman gida yana wadaka ,dan haka y tashi hankalinsa shifa ala dole birni zai taho neman kudi. Ardo b yanda y iya, y kyaleshi y tafi birnin tare d Adduar samun nasara, nan yasaida yan shanunsa guda biyu dayake kiwo tare d akuyarsa guda daya ya hada kan kudi y nufi tashar motar dan hawa motor d zata sadashi d garin gwamna. [4:41pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 5 Zuwanshi kaduna yafara aikin gadi a wani katafaren Hotel, kasancewar garin kaduna garine na masu ilimi, sai Sadik y tsinci kansa d shaawar komawa makaranta dankaro ilimi ya samu nasarar shiga fce zaria, inda aikin gadin nasa ya koma na dare,cikin ikon Allah sadik y samu shaidar karatun koyarwa wato NCE, haka yaci gaba d aikinsa na gadi bai fasaba duk da karatun da yai. A kwana a tashi ba wuya girin Allah yasamu aikin koyarwa awata makarantar sakandire t yammata dake kaduna, yana samun yan kudadensa dai dai gwargwado, abinka d mai jar fata inkaga Sadik y dau wanka kaikace wani attajirine ko babban ma'aikacin gwamnati, mutumne mai barkwanci da san raha, duk wata daliba mai jida kanta a makarantar d yake koyarwa jitake dama yace yanasonta kaji mata sudai suga Namiji kyal kyal ko baida ko sisi sai su soshi, azatansu kuma maikudine boyewa kawai yake. Wata rana sunje escortion wuraren shakatawa n garin kaduna d daliban makarantarsa, Sadik na daya daga cikin organising committee n escortion din, ita kuma hajiya lokacin zaai bikin danta sunje zasu kama gun dan gudanar d shagalin bikin, tinda hajya t kyalla ido t ga Sadik, hankalinta yatashi, mace mai san abu mai kyau d tsafta duk d manyan mutanen dakeso su aureta bataji zata iya aurensuba amma lokaci daya taji kaunar dan saurayi dan caras gwanin ban sha'awa mai jini a jika son kowa kin wanda y rasa t mamaye zuciyarta, cikin dabara ta zame t bar kawarta hajya asabe dasukajegun tare t nufi inda t hango Sadik d wasu tsirarun dalibai ,karasawa gun tai d sallama, y amsa mata cikin sakin fuska, t nuna alamun tanasan mgna dashi sukaja gefe hajya cikin dabara tace bawan Allah ganinai kanamin kama d wani dan uwan babana bello cikin yar faraar nan tasa har fararan hakoransa suka bayyana abinda y kara jefa hajiya cikin tafkin kaunar dan saurayin ta kara jin ya shiga ranta yai malemale a kalbinta, ya amsa d cewa banda dan uwa Mai suna bello, saidai ko in yanayi kikaga ko kama, cikin dabara tace inba damuwa inasan kabani phone numbr dinka kogaisawa ma dingayi, ta kara rausayar d kai tare d fari d idanu tace inceko ba damuwa, kasaqe sadik yai ya jakar datai kwanika sannan ya nisa yace to badamuwa, sunyi exchanging numbers yaimata sallama y koma bakin aikinshi, mamakine y cika zuciyar Sadik yana tunanin dole akwai wani abu d hajiyan keso dashi inba hakaba mezaisa t karbi lambarsa hartanai masa wasu salo da sarrafa harshe wajen magama, haka yaita tunani tsawan yinin ranar. Bayan sallar magriba yaji wayarshi tai ringing mamaki fal zuciyanshi ganin lambar hajiya, danna alamar dauka yayi tare d karawa a kunne Sun gaisa hajiya t kara d cewa kiranai nai ma bangajiya cikin karya murya kai kace yarinya ce mai jini ajika, sadik kuwa jiin kalaminnata yai tamkar a mafarki yace hajiya aike y cancanta naima nida narigada nasaba d hidima t dalibai, nan ta bukaci tanasan su gana inba damuwa, acewarta wata muhimmiyar magana zasu tattauna karshe sun tsaida magana karshen sati zaikaimata ziyara gidanta, tindaga wannan lokaci hajiya ta tsiri tura masa love n sweet text message morning, afternoon, evening n nigh, abin y fara dauremishi kai me matar nan ke nufi dashi, amma duk d hk bai taba bata amsaba . Ranar lahadi karfe hudu mota t saukeshi a tamfatsetsan wani gida Mai dauke d garkamemen gate, waya y kira y sanar d ita zuwannasa Mai gadine yaimai iso har zuwa babban palan saukar baki, hajy tasa ankai mishi abinci d sha kala kala, cikin shiga t alfarma kekyace wani shahararren biki ko gasar kwalliya zata tafuto kamshine kawai ke tashi jikinta,rausaya take tana karairaya, tinda y kalleta sau daya baikara yarda Sun hada idoba, kokarin rissinawa yake dan gaisheta ta dakatar dashi t hanya cewa haba habibina cikin sauri y dago ido y kalleta cikin razana aransa yace matarnan tasan Kuwa abinda take fade, bayan Sun gaisa hajiya taci gaba d magana tana yarfe haannu kamar me yar maryo tana sanar mishi kudirinta nason auranshi, cikin tsoro yace gaskiya hajiya magana t gaskiya bazan iya aurenkiba saboda dalilai masu yawa, cikin mamaki tace meye dalilanka da suke neman datsen farin cikim da nake daf da burin samu?. Amsa ya bata cikin rawar murya da sarkewa jikinsa na rawa dan ya gama tsorata da hajiya ta hanyar cewa banida karfin d zan iya aurenki balle rikonki, cikin murmushin da ya kashewa sadik jiki ta bashi amsar karkaji komai amincewarka kadai nake d bukata, shiru yayi sannan yace to shiknn hajy kibani lokaci zanyi shawara, shiga dakitai ta hado mishi turarurruka tsadaddu d rapa ta yan dari biyar biyar takawo mishi d farko Kin karba yayi ganin ranta y dan baci yasa y karba sukai sallama. Tinda y tafi gida yashiga kogin tunanin daular d hajiyan keciki d irin kyautar datamishi, Sadik mutum ne maisan yaji dadi bayasan wahala ko kadan karshe y yanke shawarar amincewa d bukatar tata, ko banza dama a matse yake shekara bakwai rabanshi d Rayuwar aure tinda matar shi tafari ladingo t rasu, ko banxa yasan zai huta d jikin hajiyar, baisan mijin hajiya zai koma ba. [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 6 Kullin hajiya zata kirashi tana mishi tini game d shawarar daya yanke amma baibata ansa ba, tinda t fuskanci zai ja mata rai yasa ta fara mishi barin kudi, boutique take zuwa t sai Mishi kananun kaya n kece raini hade d designers takalma d shirts, lokacin daya Sadik yakoma dan birni, duk gurin d y gifta yammata n hadiyar yawu jisuke dama saurayinsune,shegu kudi masu gidan rana. Ganin canjin rayuwar daya samu lokaci daya, kaunar hajya t fara samun gurbi cikin zuciyarshi daidai d pocket money hajiyan ke bashi. Abinka d kwadayayye d san y huta y ji dadi, y fara demanding manyan kudade daga hannunta, ko alamar gezau bataiba, haka rayuwar t cigaba d gudana, kullum gidan hajiya yake cin sanwar rana d dare kujifa masu karatu, kuda wajen kwadayi akan halaka. Ganin shakuwa t karu tsakaninsu, yasa hajya kara bijiromai d batun aurensu, ai abin d kunya y bijire mata, dan ayanxu daidai d abokai y canja duk alfarmar inuwar hajiya dayake shaka. Sun tsaida magana kancewa nan d two week's zai turo magabatansa a daura musu aure, hajiya Kuwa sai shiri take n amarcewa, musamman tai aike maiduguri dan hado mata kayan daka n maida tsohuwa yarinya, zuciyar kuruci dangin hauka kenan "Oh su hajiya angirma baa san an girmaba " saboda doki ji take tamkar wannan shine aure n fari gareta. Ita ta tanadi sadaki dubu dari t baiwa sadeek ya baiwa iyayensa dan gabatarwa g iyayenta, sanin halin ardo yasa bai tinkareshi d batun aurennasaba dan yasan bazai taba amince mai b. Tinani ya shigayi yanxu maiye abinyi, can zuciyarshi t bashi amsar yaje yayi hayar dattijo Mai kamala dan zuwa karba mishi auren hajiyar bai sha wuyaba wajen samu, akwai wani dattijo Mai saida sigari a bakin layinsu, yaje y shaka mishi kudi masu gidan rana, dattijo yaga banza sai washe hakora yake yana gdya harda risinawa, gyaran murya Sadik yayi tare d gaya mishi bukatar da yasanya shi zuwa gunshi, dariya dattijon yayi yace yaro karkaji komai, mukai kawalcima balle hada sunnar maaiki saw, karkaji komai yaushe ne daurin auren, Sadik y gaya mishi,dattijon yace abinda zakai yanxu ka tanadar mana manyan kayan dazamu sanya ran daurin auren mu uku d abokaina sai kuma kudin d zaa hayo motar da zamuje daurin auren ,gdya Sadik yashiga yiwa dattijon, tare d mishi sallama, farinciki fal zuciyar Sadik bai tsaya ko inaba sai kasuwar bacci ya sayo shadda fara bandir uku ya zarce gun tela ya bada dinki sannan y nufi gida, kudi kare magana kenan. Kubiyoni dan jin cigaban labarin mijin hajiya da yadda auren kwadayi zai kasance. Taku har kullum…………………………Ayusha Iliasu. [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 7 Shirye shirye sunyi nisa bangaren hajiya, har gagarumar walima tai shirin yi a wannan rana ita d kawayenta. A daya barinma sadik y gama komai sai lokaci ake jira. Rana bata karya saidai uwar diya......... A yau jumaa ta kama ranar daurin auren hajiyar d zankadeden saurayi Sadik ,dattijo d abokanan biyu sunsha farar shadda Mai hade d malun malun wadda akaiwa aiki d bakin zari kaikace wasu attajiran mutane ne, a irin turarukan d hajiyan take baahi ya dakko musu sukafeshe jikinsu sai kamshi ke tashi kai kace shahararrun 'yan kasuwa ne masu juya naira t zama dala. Farar jeep zundumemiya Sadik y hayo akasuwar saida motoci dake kaduna dubu goma awa biyu, suka shiga mota dattijai uku a baya sun kame, ango Sadik kuma y kame a gidan gaba yayi kwam ya drawing yayinda Mamallakin motar ke jansu, sulululu tafiyar kasaita motar take, wato a hankali kaikace zuriar sarauta ko ta wani shugaba mai fada aji ce. Taro yai taro waje yacika dankam da mutane lokacin tawagar gidan ango suna karaso gun iyayen hajiya, waliyyinta y zamo babban wanta, Sun gabatar d sadaki lakadan dubu 100,take jamaar gurin suka shaida auren hajiyar d angonta Sadik, bangaren yanuwan hajiya sai yabawa Sadik suke ganin shi dan manyan mutane sannan sankacecen bafulatani usul. An gama daurin aure inda makida da maroka kebin ango dan samun na koko, kirari suke shekawa ango mai tsuma jiki, nan y fiddo kudi y basu baisan adadinsu b saboda kirarin ya ratsashi,lokacin d kowa y watse sadik yabaiwa dattijan da ya hayo kowanne dubu biyar biyar sukai godiya y koma gida ya dau wanka, waya y dauka y kira hajiyar cewa gashinan isowa tai murna d hakan tare d cewa yayi sauri dan gaisawa d qawayenta. Isarsa gidan keda wuya kowa cikin mamaki suka zuba mishi ido, kowacce d abinda take kissimawa a ranta, wasu ji suke dama sune zasu yi karai d wannan saurayi san kowa kin Wanda y rasa kuji mata masu zuciyar yara angirma baasan angirmaba, yayinda wasu ke tir d alamarin aransu cewa suke hajiya taji kunya t rasa wanda zata Aura sai saan danta, su aganinsu abin b tsari, yayinda wasu ke yaba kyawunsa. Bangaren hajya Kuwa jinta take tamkar sallah, bakinta yaki rufuwa sai faraa d dariya take take zubawa kmr gonar auduga hango kanta kawai take daren yau,zata tuna da, zata gwangwaje, ta shana ta wartsake ta barbaje tare d fantamawa,jitake dama tin yanxu kowa y tashi y barmata gidan ita da danshilan angonta. [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ……Written:-Ayusha Iliasu. ……Story:-Hawwa Saleh. Page 8 Misalin karfe takwas taro y tashi kowa y tafi gida, yakasance daga hajiya sai habibinta, sunan d ta lakaba mishi kenan,suna zaune palo suna cin dinner, gasassun kaji ne wanda aka bankaresu hade d lafiyayiyarn madarar shanu sukeci,ji sukai anfara knockin kofar falo, cikin mmki hajiya t tashi abin y bata mmki waye zai kawo mata ziyara a wannan lokaci, tana budewa sukai ido biyu d yayanta wato abdulrahman d abdussalam ,Hjy bataji dadin wannan ziyarar tasu b amma bata nuna musu afuskaba, tare suka karaso palour azatansu zasuga babban mutum Mai kamala matsayin mijin ummantansu amma sukai gamo d bafulatanin saurayin da bai wuce sa ansuba abin y sosa ransu, amma zamowar uwa aba Mai daraja haka suka dan risina suka gaidashi tare d gaisar d hajiyan, juyawa sukai d zummar tafiya, hajyn ce tace bazaku zauna mudanyi hiraba, cikin takaici sukace ai dama gaisheki mukazo yi, haka suka futa kowa n saka abu cikin zuciyarshi, wannan wace irin rayuwace inba zuciyar yara b Me zai hadata aure d wannan matashin. Futarsu keda wuya hajiya t dawo gun zamanta, tamanta d bacin ran data hango fuskar yarannata, sukaci gaba d cin kazar su, hajiyan ke bashi a baki shima ya bata, Sadik sai yake gani kamar a Film wai shine yau yake rayuwa irinta turawa, kaunar hajiya t kara shiga jini d tsokarshi, bayan Sun kammala suka dan karasa kallon Series din d akeyi a TV, karfe goma suka nufi daki. Hajiyance tayi shirin yin wanka, ta nufi bandaki kome t tuna saita dawo inda Sadik ke zaune tamkar dasashi akai mamaki yake irin daular da aka zuba cikin dakin wai shine zai kwana kan lafiyayyen gado hade d A.C tana ratsashi. Karasowa kusa dashi tai tare d jawo hannunshi habibina zomuje ka cudamun bayana, zaro idanu yai cikin in ina yace cuda baya hajiya ai inda soso koke zaki iya cudawar, cikin shagwaba ke kyace wata kankanuwar yarinya teen age ce tana wani bubbuga kafa akasa tamkar yanda yara sukeyi, pls habibina ,kasancewar bayasan bacin ranta ya amince tarike mishi hannu suka nufi toilet. Tabb abin kunya girma y fadi rakumi y shanye ruwan 'yantsaki?Ala sittiri bukui dai su hajiya. [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. Page 9 salo kala kala ta dinga yima sadik a toilet tin yana jin kunya baya biye mata har saida tasa ya saki jiki da ita ya biye mata suka yi wanka cikin tsantsar kauna,taimasa wankan dole yai mata itama,tin a toilet hanklin Hajiya y gama tashi ganin irin baiwar halitta d Allah yaiwa angon nata, karamin towel ta dauro wanda iyakacin kirjinta ya rufe mata bai karasa cinya sosaeba,hk shima sadik y dauro sabon towel din data tanadar mishi,tare suka jero dg toilet din suka fito hajiya sai rausaya take tamkar wata sabon shigar aure jin ta take tamkar budurwa yar shekaru 17. Gaban dressin mirror suka zauna kan wani karamin capet inda ta fiddo kayan shafa ta mika wa sadik, nan yai sororo dashi ya kawar kauye baki bude yace hajiya mezanmiki da…………………,bata barshi ya karasa ba ta shagwabe masa tare d narkewa kamar wata dadys pet ta kwanto kirjinsa "wai wayaga gursimeti"tace habibina shafamin zakayi ckn shagwaba take maganar "Ohh ni 'yatasu a lallai hajiya sai antuna da wai", shiko gogan naka cikin zakuwa ya karba ya kama shafamata lungu da sako na jikinta b inda bai shafeshi da maiba, lokacin d y iso kan kirjinta jitai kamar t sume saboda wasu sakonni dake ratsa jinin jikinta d tsokarta d kayan kamshi ba, saida ya gama tsaf yafara shafawa nasa jkn tai sauri tace haba habibi ai aramawa kura aniyarta, yar dariya yai nan tafara shafe shi harda inda ta dokanta su gamu dashi ta shafe shiko sadik tuni ya fara limshe ido kmr wnda ya kwana bai barci ba. Sun gama shiryawa inda suka dauro alwala tare da gabatar da sallahr da Annabi y umarci maaurata dayi dan neman albrkar aure, suna idarwa ta umarceshi da su taso dan kai hakarkarinsu kasa, gado suka nufa suka kwanta, tinda suka kwanta sadik ya gagara motsin kirki sbd jinsa da yai a lausassan gadon da baitaba zatoba harsaida hajiya ta shafi kirjinsa sannan ya dawo hayyacinsa,habibina tinanin me kakeyi haka banason ka ringa yawan tunanifa jiyai ta janyoshi wuf saigashi y fado kirjinta abinka da siririn yaro, kankameshi tai tsam lkcn ninfashinsa yake kaiwa d komowar sabon alamarin d yaji, lifff yai a jikinta ya kasa aiwatar da komai irin n maaurata. A wannan daren dai hajiyace taita romancing din sadik idonta ya rufe kissin dinsa take kota ina tin baya iya mayar mata harsa da ya maida mata d martani ba karamin lokaci suka shafe a hakaba kfn kwallo ya samu nasarar fadawa raga ba dan ba karamin wahalar da sadik hajiya taiba duk da ya dade yana kishir ruwan abun amma har tafishi,basu dawo hayyacinsu ba saida nauyayyen baccin daya daukesu ya sakesu sannan suka farka. Misalin karfe uku na dare , hajiyace ta fara tashi sannan ta tashi sadik sukaje suka dauro alwala, lokacin da suka dawo makwanci hajiya ta bukaci sadik da su karadan ita bata koshiba,take sadik ya ce gsky ya gaji ganib t bata rai ya amince d bukatar ta suka kara lulukawa duniar jin dadi."lallai hajiya abin nema yasamu matar falke ta haifi jaki". [4:42pm, 11/5/2016] A AYSHA: MIJIN HAJIA ………Written:-Ayusha Iliasu. ………Story:-Hawwa Saleh. Page 10 Tsawon wannan daren kwana maauratan sukai suna abu daya, sun gurji juna son ransu basu suka hakura b saidan jin kiran sallahr asuba,kasancewar sadik duk inda yake yana kula da ibada, sallah a jam'i bata wuceshi sai dole haka itama bangaren hajiyar tana kula d ibada daidai gwargwado. Wanka yaje ya farayi tare da dauro alwala sannan itama hajiyar taje tayi wankan, tana fitowa yace yatafi masallaci badan tasoba ta barshi ya tafi taso suyi sallahr a tare, dan yanzu jitake kmr zaa kwace mata shi batason yai nisa da ita sbd kasancewarsa gwarzon namiji. Nauyayyen baccin gajiyar hidimar biki da hidimar kwanan da sukayi sina duty ne ya debesu lkcn da sukai sallahr asuba basu suka farka ba sai karfe goma na safe. Wanka sukayi inda hajiya ta shirya ckn wata tsadaddiyar red gown ta (english wears) rigar ta karbi jknta, hk shima sadik ya sanya red t-shirt n blue jeans kayan sun masa kyau kai kace rainon turai ne. Jerowa sukai dg bedroom rike d hannun juna gwanin shaawa dan har pix nai musu sbd kyan d suka yi dining suka nufa inda aka jere cima iri iri domin yin breakfast, a tare suka zauna kan kujerun dining din suna fuskantar juna, soyayya ruwan zuma. Sun ciyar da junansu saida suka tabbatar kowa ya koshi sanna hajiya ta taso ta rungumo angon nata suka nufi palo, soyayya tsantsa nagani a wannan guri wacce hajiya takewa sadik dan kallo ya barku yan uwadan hajiya tasha alwashin saitai teaching din sadik da salo d sarrafa harshe iri iri na soyayya saita koya masa love harda lovayya ma wanda sadik baisani ba tsahon zamanshi d mirigayya ladingo.banda abin sadik ina ladingo ina sanin samfurin soyayya . Yinin wnn ranar amarya hajiya bata bar sadik y leka koda kofar gidaba tana manne d abinta, in kuwa kinga t matsa dg kusa dashi tofa dalili ne mai karfi dan duk ydd sadik keda maitar bin jam'i saida y hakura a sbd hajiya jitake in tafita xaa dauke mata shi, dan jinta take a ranar tamkar bata taba tarayyar aure d wani namiji b sai sadik. A zuciyar sadik dinma haka abin yake dan amaryar tasa tagama malemale a xuciyarsa har tunani yake dm hk auren yake d dadi ashe a baya b aure yaiba dan tsawon zamansa da ladingo bata taba kwatanta masa irin abubuwan da hajiya tai masa ba daren jiya, yadda yaga tana sarrafashi tamkar fulawar d xaai different snacks da ita,karasa tinanin sa yai d cewa woawwwww gsky nayi dace d hajiya ta iya soyayya da kalamai masu dadi gsky matan birni sunyi, sun gama haduwa.
Tuesday, 25 October 2016
RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 01-05 Tafe suke suna sauri ganin alamun hadari ya gangamo, ba abinda ake illa iska mai hade da kura, Aysha ce rike da hannuwan kannanta Asma'u ,Halifa da Amina dan tsallako katafaran titin dazai sadasu da gida, awannan lokaci masu ababan hawa suma saurin suke dan ganin sun isa gida kafin ruwan ya tsuge,kimanin mintina talatin suka shude musu tsaye abakin titin har akafara yayyafi, hakan yasanya Ali mai rake dake hada kayan sana'arshi taimaka musu wajen tsaida motoci, Sun mushi godiya tare da shigewa cikin gida cikin murnar dawowa batare da ruwan ya musu duka ba. Bari guda kuwa Hajiya Hafsatu tashiga damuwa ganin yarannata basu dawo daga makarantar islamiyya ba, tanajin sallamarsu tasauke wata ajiyar zuciya tare da godiya ga Allahu subhanahu wata ala. Muryar kakarsu ce ke tashi take kwallawa Aysha kira, Aysha, Aysha cikin rawar murya Aysha ta amsa, nan kakar kecewa zokije gidan dan tani maigoro kisayomin goro zuciyata tashi take da kyar zan iya bacci daran yau idan banciba ga kuma dare yayi, yusufu almajiri na yai mun sallama sai gobe balle na aikeshi ya sayo min. Cikin damuwa Hajiya Hafsatu mahaifiyar Aysha tace Aysha yi sauri kije ki karbo kudin ki sayo mata kan ruwan ya kara karfi, bani da zabi daya wuce karbar kudin da ficewa dan sayo goran. Futowarta daga gida kenan aka tsuge da ruwa, akwai tazara tsakanin gidansu da gidan da ake saida goran kafin tadawo ruwa ya mata duka, jikinta ya fara rawar sanyi. Zazzafan zazzabine ya lullube ta wanda yakaita ga kwanciya asibiti. RAYUWA AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 06-10 Alhaji Sadiku Saleh shine mahaifin Aysha , mahaifinshi Alhaji Saleh yanada matan aure guda biyu. Hajiya Aisha ita ce uwar gida da Hajiya Bilkisu amarya, Hajiya Aisha nada yaya biyu maza yayin da Hajiya Bilkisu tanada yaya uku maza. Hajiya Aisha itace mahaifiyar Alhaji Sammani , da Alhaji sani yayinda hajiya Bilkisu ita ta haifi Alhaji Sadiku da Alhaji yusuf da kuma Alhaji Ali,Sadiku shine karaminsu. Kasancewar zaman bahaushe a da da zumunci yafi danko zakaga yan uwa suna zaune a guri daya cikin gida daya kowa da bangarenshi ko kuma gida jikin gida. Haka rayuwar wadannan bayin Allah ta taso cikin So da kaunar juna, daya bayayin abu batare da shawarar dan uwansaba. Aladar dan bahaushe ta dogaro dakai yasanya kowanne cikinsu yana gudanar da kasuwancinsa daidai gwargwado . kasancewar tun asalin bahaushe ba cima zaune bane mutum ne dayasan ciwan kansa ta hanyar amfani da karfin jikinsa da basirar da Allah yai Mishi wajen ganin yasamarwa kansa abubuwan bukata nayau da kullum. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 11-15 Alhaji Sammani shi Allah y daukaka ya baiwa tarin dukiya mai yawa, mutum ne mai tausayi da taimakon na kasa dashi, duk wani abu da zai taso na taimako duk girmanshi akakai gabanshi zaiyi iyakar kokarinsa wajen ganin ya magance shi, Allah y azurtashi d matan aure guda biyu da yara goma babban dansa wanda yasanyawa sunan mahaifinsa Alhaji Saleh yayinda sauran yarannasa suka hada da Aminu, Salihi, Fatima, Hadiza, Abdullahi, Juwairiyya, Zainab, Maryam da Zahrau. Yayin da yara suka taso sukakai munzalin shiga makarantar boko da islamiyya, yanasawa a hada yaran kaf da yayan makwabta yasanyasu a makarantar , shi ke daukan dawainiyar su ta biyan kudin makaranta harma da jigilar kaisu yau d kullum. Ahaji Sammani mutum ne me zumunci da San 'yanuwansa hakan tasa harkokin kasuwancinsa suka kara fadada har zuwa kasashen turai, duk lokacin da zai tafiya yakan dauki guda acikin matansa Yatafi dasu. Yanada katafaren kamfanin sarrafa gyada a garin Kano, Lagos Kaduna da Zariya, daga baya ya kara bude saban kamfanin jirgin sama Mai jigilar alumma daga wannan gari zuwa wani gari. Taimakon da Alhaji Sammani yake bai tsaya anan ba duk shekara zai zabi makwabta da wasu daga ma'aikatansa da yanuwa ya biyawa kudin hajj dan sauke farali. Harkokin kasuwancinsa na najeriya yabarsu a hannun yan uwanshi, yayinda karamin kaninsu Sadiku shi yazamo sakatarensa. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 16-20 Alhaji Sadiku mahaifin Aysha yazamo mai gaskiya rikon amana da takatsantsan dan ganin ya sauke nauyin da Allah y dora musa, ana cikin wannan hali wata rana tafiya takama Alhaji Sammani zuwa kasar turkey Ahanyarsa ta dawowa ciwansa na asthma ya tashi kafin wani lokaci rai yayi halinsa, karkaso kaga tashin hankali gurin wannan zuria saboda Alhaji Sammani yazamo majibancin alamuransu. An share makoki, babban dan Alhaji Sammani wato Saleh wanda akafi kira Alhaji karami . Ya kammala karatunshi na secondary, yacigaba har ya zuwa Jami'a. Alhaji karami ya taso a gata dukkannin kannan mahaifanshi na kaunar shi saboda yanda yake girmamasu ya daukesu tamkar su suka haifeshi. Har awannan lokaci ragamar kasuwancin mahaifinsa na hannun kannanshi, bayan da ya kammala jami'a ne yaga yakamata ya karbi harkokin kasuwancin,nan akai gumurzu daga wasu daga cikin kannan iyayennasa. karshe aka yanke shawarar ya koma kaduna dan tafiyar d babban reshen kamfanin dake acan. A lokacin da mahaifiyarshi ke sanar dashi cewa yanxu tinda kagama karatu, ga aiki kanayi yanada kyau ace ka ajiye iyali, cikin murmushi y Kalli mahaifiyar tashi yace Umma aini na samu macen da nakeso. Cikin jin dadi ta tanbayeshi yar wana attajirin ce kokuwa yar sarauta, nan ya zaro idanunsa tare da cewa Umma wana irin attajiri ko sarauta kuma .ni auren zumunci zanyi, cikin rawar baki ta tanbaya auren zumunci kamar yaya, yace eh Aysha nakeso, salati ta fara da tafa hannu cikin kidimewa. Duk yara matan dasuke garin Kano karasa wadda xaka zaba sai Aysha,tace towaima Wacce Ayshar kake nufi ? nan ya sanar da ita cewa babbar yar Alhaji Sadiku kanin mahaifinsa. RYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 21-25 Hajiya Zuwaira mahaifiyar Alhaji karami ta tsinci kanta cikin rudu dajin babban dan nata zai auri Aysha, take taji kiyayyar Aysha da uwarta ta shiga zuciyarta. Yinin wannan rana bata cikin nutsuwarta sallamar kanwarta Uwale shi yadawo da ita daga zurfaffan tunanin data jefa kanta ciki. Sun shige daki tasanar da 'yar uwartata halim da take ciki, dariya Uwale tai tace haba yaya ke kika haifi Alhaji karami kokuwa shine y haifeki, ki futo ki nuna mishi kada ya sake y furta wannan magana ga kowa balle kannan mahaifinsa suji kadama abun yazamo rigima. Godiya tai mata, tare da alkawarin sanar dashi hakan t wayar salula. Alhaji karami na office yaji kira ya shigo mishi, ganin sunan d ya baiyana jikin screen din wayar sawa gabansa ya fadi, cikin gaggawa ya danna tare d karawa a kunne. Tamkar yana gabanta ya rissina tare d gaisheta, ta amsa cikin kulawa irin ta da da uwa, ta gargadeshi kan cewa wannan mgna da sukai karya sake y sanarwa da Aysha balle dangin babansu, sai yace Hajiya wannan magana bata waya bace kibari insha Allah cikin weekend zanxo miyi maganar cikin nutsuwa . Cikin dare Alhaji karami y kasa bacci juyi kawai yake daya rintse ido siffar Aysha ce ke yawo a kwakwaluwarshi, Aysha fara ce, doguwa, tanada round face wadda ke dauke da dara daran idanuwa, pointed noise, bakinta dan karami abin sha'awa idan tana magana, Allah y hore mata dukiyar fulani wanda suka taimaka wajen kara futowa da kyawunta, ga hips wadanda idan tana tafiya suke jan hankalin mutane, ba maza kadaiba, har mace zataso ace itace. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 26-30 Gefe daya kuwa aisha Da iyayenta basusan wainar Da ake toyawa ba, wannan lokacin tana makarantar secondary aji hudu wato SS1. Karatu kawai tasanya agaba ka in Da na in, mahaifiyarta batada addua har kullum sai Adduar Allah ya sada diyarta Da miji nagari. Aysha kawace ga zainab kasancewarsu sa annin juna, komai tare sukeyi , zainab kanwar alhaji karamice wadda take autarsu, gata yasa tazamo sangartacciya sai abunda takeso takeyi, ba wanda yake mata fada. Tinda Zainab taji cewa yayanta aysha yakeso tadaina kulata kota biyo mata makarantar islamiyya sai tace ta tafi ita b yanzu zata je ba Mahaifiyar Zainab din kuwa ta canjawa aisha fuska ko gaisuwarta ala dole take amsawa,wanda ada har kudin makaranta take bata ,abin ya daurewa aysha kai ita dai tasan wani Abu bai shiga tsakaninsu tsakaninta d kawarta Zainab. Bayan antaso su daga mkranta sai taga Zainab tana sauri zata tafi, kwalla mata kira ta Zainab, zainab, banxa tai da ita tacigaba d tafiyarta, da gudu tazo ta sha gabanta tare d rike hannunta zainab lafiya meke faruwa naga kwana biyu kin canjamin Budar bakin Zainab keda wuya sai cewa tai ancanja miki din. Bari kiji wallahi idan takamarku bin malamai keda uwarki, kunje kunyiwa yayana asirin da zai aureki to wallah karyarku ta sha karya, yayana ba abunda zai ci dake, yar matsiyata kije ki gayawa uwarki taje tasa akarya asirin datai inba haka ba kuwa saikin gwammace mutuwarki akan rayuwarki da yayana. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 31-35 Cikin tashin hankali Aysha ta dawo gida ,cikin gudu ta karasa dakin mahaifiyarta tana momy, momyna, Hajiya hafsat tayi mamakin jin irin kiran d 'yar tata take mata, lokacin tana daki tana gyaran wardrobe. Tafada kan cinyar momy tafashe da azababban kuka, momy ke tanbayarta lfy, waye y rasu. Takasa bude baki balle tai mgna,momy kuwa t zuba mata ido, saida tai mai isarta sannan tace momy Zainab ce. Hajiya Hafsat tace Zainab kuma fada kukai, dan kunsamu sabani d ita zakizo kina wannan gursheken kuka, tashi tai tabar mata daki saboda takaici. Ayshar tashi tai tabi momy zuwa parlour ta zauna kusa d momy nan t labarta mata maganganun d Zainab tagaya mata. Ta tambayi yar tata cikin tuhuma d zargi, dama yace miki yanasanki shine baki taba gayaminba a matsayina n mahaifiyarki? aysha tace wallhi Momy bai taba gayan haka ba, asalima gaisuwa kadai ke hadani dashi in mun hadu. Momy tace to shiknan karki kulata kuyi fada kinji diyata, karkifasa biya mata makaranta kullum kije tinda tare kuka saba zuwa. A wannan rana mamaki da tunani y cika zuciyar Hajiya Hafsa Allah yasa wannan magana kar ta baiyana balle wani yaji, sabida tasan diyar tata bazata taba jin dadin auren Alhaji karami ba saboda kiyayyar d 'yanuwansa suka fara nunawa Abu. Adduarta cikin kowacce sallah itace Allah y zabawa Aysha miji nagari wanda zai riketa amana d gaskiya. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 36-40 A can kaduna kuwa Alhj karami yana t tunanin t yanda zai shawo kan mahaifiyarshi t amince Mishi d samun cikar burinshi Yagama sawa ranshi Aysha ce abokiyar rayuwarshi, duk wani numfashi dazaiyi kara jin kaunarta yake a ranshi, shima yana mamaki yanda lokaci daya y fada tarkon sonta. Da misalin karfe goma jirgin su yasauka a filin sauka d tashin jirgin sama n Malam Aminu Kano. Sani direba ne ya daukoshi zuwa gidansu, dakin mahaifiyarshi y shiga, tayi murnar ganin dan nata. Hajiya Zuwaira macece maisan yayanta bataso taga abinda zai bata musu rai,haka zalika bata wasa d farincikinsu komai nata zata iya badawa dan farincikin 'ya'yan nata. A wannan lokaci ne taga alamar rama a jikin dannata, take tambayarshi koyayi ciwo ne? yace a'a Hajiya yanayin aikine da zurga zurga badan t yarda b, aka bar mgnar. Cikin kwantar d kai tare d kwlla a idanunsa yake sanarwa da mahaifiyar shi irin kaunar d yakewa Aysha, shi kansa y rasa yanda zaiyi. Idan ban aureta b Hajya b matar d xan iya zama d ita. Ganin dannata n zub d hawaye, ta amince d batun nashi dan farincikinsa, amma kasan zuciyarta ta kullaci Aysha d mahaifiyarta tare d cin alwashin ramuwa g asirin d sukaiwa dan nata. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 41-45 Alhaji karami y samu tsantsar farinciki, tare da godiya g Allah da yasanya Hajiya tai accepting bukatarshi, tare d yimata Adduar Allah y kara tsawan kwana Mai amfani d karin lafiya. Gefe guda kannansa abun duniya ya ishesu, saboda sunci burin yayannasu y auri 'yar manyan mutane masu naira yanda za'a yi bikin d ba'a taba yiba a danginnasu. Kwata kwata sundaina sakarwa Aysha fuska ko a hnya suka hadu tai musu magana banxa zasuyi mata hade d tsaki. A sanadiyyar karan tsanar d suka doramata, tadau alwashin ko yayannasu Yafurta yana sonta zata ba shi hakuri yaje ya nemi wata badan bata sonshi be, sai dan samun kwanciyar hankalinta. Tanada burin samun So da kauna daga dangin duk namijin da zai zamo miji gareta, dan samun zaman lfy d zuriya Dayyiba. A hankli magana ta fara zaga dangi cewa Alhaji karami yace Aysha yake so, mafi yawa dg cikin dangi bakin ciki suke dan ji suke dama 'ya'yansu yace yanaso. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 46-50 Washegari lahadi Alhaji karami ya je yasamu mahaifin Aysha dan sanar dashi bukatar shi tasan ya auri diyar shi, cikin farinciki ya amsa Mishi tare d mishi alkawarin cewa ya bashi ita, yaje su fuskanci juna. Alhaji Sadiku yayi farinciki tare d kwalla saboda ya tuno dan uwansa Marigayi Alhaji Sammani, dayana raye da sai yafi kowa farin ciki. Bazai taba mantawa b wataran suna zaune d yayannashi yace,da badan zamani y lalalace ba inada sha'awar muyiwa yaranmu auren zumunci, Alhaji Sadiku yace abine Mai kyau hakan, sai dai yaran wannan zamani ka haifesu baka haifi halinsu ba, kar mu hada abu karshe daya ya bijire muxo muji kunya, tuna wannan hira ya kara masa kwarin gwuiwa tare da alkawarin tabbatar d wannan alamari. Hajiya Hafsatu t kawo wa mijinta abinci suna dan taba hira, ya daga kai ya kalleta, yace Hafsatu yau fa ranar farinciki ce gareni, naso ace yaya Sammani yana raye muyi sharing wannan farin cikin, tace lafiya Alhaji meya faru, cikin zakuwa y shaida mata, fuskarta b yabo b fallasa, tace Allah y tabbatar d abinda yafi alkhairi, Alhj Sadiku yace hakanma shine alkairi, abinda nakeso dake kisanarwa da Aysha dan kowana lokaci daga yanxu zai iya zuwa gareta dan su fuskanci juna, tace to Alhaji za'a gaya mata. Washegari Alhaji Sadiku y tara 'yan uwansa maza ya sanar dasu, kowa yayi Adduar Allah yasa ayi damu, yasa kuma mutuwa ce zata raba. RAYUWAR AYSHA ( TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA LIASU 51-55 Sati n zagayowa Alhaji krmi ya sauka garin Kano musamman dan ganawa d hasken zuciyarsa wato Aysha. Tin safiyar waannan rana jikin Aysha yai sanyi, komai takeyi cikin karfin hali takeyi. Hajya Hafsatu ce karfin shirya abinci d za'a sauki Alhj karamin. A bangarenshi kuwa sabbin English wears y zarce Boutique y siyo duk dan y burge Aysha. Shi mutum ne marasan hayaniya, baida surutu, idan kaji tashin muryarshi to cikin abokan shine ana hirar kwallo (football). Misalin karfe hudu n yamma y futo daga wanka, cikin sauri y sanya kayan tare d taje sumar shi, turarukan shi gaba daya sai da ya fesa, wani irin kamshi sassanya ne ya cika dakin, duk d kasancewarshi Namiji bai fiya amfani d turaruka masu karfin kamshi ba. Misalin 3:30pm suka gama hada Ginger drink, Hajiya Hafsat ta umarci 'yar tata taje tai wanka ta shirya, nan Aysha taje ta shirya cikin atanfarta mai adon pink (Super exclusive)ta kafa daurin dankwali tamkar gwaggwaro batare d tayi make up ba kwalli lip balm kawai ta sanya. Ba karamin kyau kayan sukai mata ba, tamkar wadda zata futa wani gagarumin biki ko competition. Hajyn ce ta zabo mata mayafin (Veil) daya dace d kayan tare d yari, sarka d zobuna (custumes),turare Mai kamshi t fesa wa 'yartata, addua fal zuciyarta idan da alkhairi Allah y tabbatar d wannan alamari in babu Allah yayiwa diyar tata canji d mafi alkhairi. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 56-60 Misalin karfe 4:00pm ya iso kofar gidansu Aysha, kai tsaye sallama yayi tare d shiga cikin gida, bangaren Hajy Hafsatu mahaifiyr Aysha y nufa, tana zaune a palour suna kallo tare d yaranta, cikin fara'a ta amsa sallamar. Har kasa ya durkus.
Subscribe to:
Posts (Atom)