Tuesday, 25 October 2016
RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 01-05 Tafe suke suna sauri ganin alamun hadari ya gangamo, ba abinda ake illa iska mai hade da kura, Aysha ce rike da hannuwan kannanta Asma'u ,Halifa da Amina dan tsallako katafaran titin dazai sadasu da gida, awannan lokaci masu ababan hawa suma saurin suke dan ganin sun isa gida kafin ruwan ya tsuge,kimanin mintina talatin suka shude musu tsaye abakin titin har akafara yayyafi, hakan yasanya Ali mai rake dake hada kayan sana'arshi taimaka musu wajen tsaida motoci, Sun mushi godiya tare da shigewa cikin gida cikin murnar dawowa batare da ruwan ya musu duka ba. Bari guda kuwa Hajiya Hafsatu tashiga damuwa ganin yarannata basu dawo daga makarantar islamiyya ba, tanajin sallamarsu tasauke wata ajiyar zuciya tare da godiya ga Allahu subhanahu wata ala. Muryar kakarsu ce ke tashi take kwallawa Aysha kira, Aysha, Aysha cikin rawar murya Aysha ta amsa, nan kakar kecewa zokije gidan dan tani maigoro kisayomin goro zuciyata tashi take da kyar zan iya bacci daran yau idan banciba ga kuma dare yayi, yusufu almajiri na yai mun sallama sai gobe balle na aikeshi ya sayo min. Cikin damuwa Hajiya Hafsatu mahaifiyar Aysha tace Aysha yi sauri kije ki karbo kudin ki sayo mata kan ruwan ya kara karfi, bani da zabi daya wuce karbar kudin da ficewa dan sayo goran. Futowarta daga gida kenan aka tsuge da ruwa, akwai tazara tsakanin gidansu da gidan da ake saida goran kafin tadawo ruwa ya mata duka, jikinta ya fara rawar sanyi. Zazzafan zazzabine ya lullube ta wanda yakaita ga kwanciya asibiti. RAYUWA AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 06-10 Alhaji Sadiku Saleh shine mahaifin Aysha , mahaifinshi Alhaji Saleh yanada matan aure guda biyu. Hajiya Aisha ita ce uwar gida da Hajiya Bilkisu amarya, Hajiya Aisha nada yaya biyu maza yayin da Hajiya Bilkisu tanada yaya uku maza. Hajiya Aisha itace mahaifiyar Alhaji Sammani , da Alhaji sani yayinda hajiya Bilkisu ita ta haifi Alhaji Sadiku da Alhaji yusuf da kuma Alhaji Ali,Sadiku shine karaminsu. Kasancewar zaman bahaushe a da da zumunci yafi danko zakaga yan uwa suna zaune a guri daya cikin gida daya kowa da bangarenshi ko kuma gida jikin gida. Haka rayuwar wadannan bayin Allah ta taso cikin So da kaunar juna, daya bayayin abu batare da shawarar dan uwansaba. Aladar dan bahaushe ta dogaro dakai yasanya kowanne cikinsu yana gudanar da kasuwancinsa daidai gwargwado . kasancewar tun asalin bahaushe ba cima zaune bane mutum ne dayasan ciwan kansa ta hanyar amfani da karfin jikinsa da basirar da Allah yai Mishi wajen ganin yasamarwa kansa abubuwan bukata nayau da kullum. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 11-15 Alhaji Sammani shi Allah y daukaka ya baiwa tarin dukiya mai yawa, mutum ne mai tausayi da taimakon na kasa dashi, duk wani abu da zai taso na taimako duk girmanshi akakai gabanshi zaiyi iyakar kokarinsa wajen ganin ya magance shi, Allah y azurtashi d matan aure guda biyu da yara goma babban dansa wanda yasanyawa sunan mahaifinsa Alhaji Saleh yayinda sauran yarannasa suka hada da Aminu, Salihi, Fatima, Hadiza, Abdullahi, Juwairiyya, Zainab, Maryam da Zahrau. Yayin da yara suka taso sukakai munzalin shiga makarantar boko da islamiyya, yanasawa a hada yaran kaf da yayan makwabta yasanyasu a makarantar , shi ke daukan dawainiyar su ta biyan kudin makaranta harma da jigilar kaisu yau d kullum. Ahaji Sammani mutum ne me zumunci da San 'yanuwansa hakan tasa harkokin kasuwancinsa suka kara fadada har zuwa kasashen turai, duk lokacin da zai tafiya yakan dauki guda acikin matansa Yatafi dasu. Yanada katafaren kamfanin sarrafa gyada a garin Kano, Lagos Kaduna da Zariya, daga baya ya kara bude saban kamfanin jirgin sama Mai jigilar alumma daga wannan gari zuwa wani gari. Taimakon da Alhaji Sammani yake bai tsaya anan ba duk shekara zai zabi makwabta da wasu daga ma'aikatansa da yanuwa ya biyawa kudin hajj dan sauke farali. Harkokin kasuwancinsa na najeriya yabarsu a hannun yan uwanshi, yayinda karamin kaninsu Sadiku shi yazamo sakatarensa. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 16-20 Alhaji Sadiku mahaifin Aysha yazamo mai gaskiya rikon amana da takatsantsan dan ganin ya sauke nauyin da Allah y dora musa, ana cikin wannan hali wata rana tafiya takama Alhaji Sammani zuwa kasar turkey Ahanyarsa ta dawowa ciwansa na asthma ya tashi kafin wani lokaci rai yayi halinsa, karkaso kaga tashin hankali gurin wannan zuria saboda Alhaji Sammani yazamo majibancin alamuransu. An share makoki, babban dan Alhaji Sammani wato Saleh wanda akafi kira Alhaji karami . Ya kammala karatunshi na secondary, yacigaba har ya zuwa Jami'a. Alhaji karami ya taso a gata dukkannin kannan mahaifanshi na kaunar shi saboda yanda yake girmamasu ya daukesu tamkar su suka haifeshi. Har awannan lokaci ragamar kasuwancin mahaifinsa na hannun kannanshi, bayan da ya kammala jami'a ne yaga yakamata ya karbi harkokin kasuwancin,nan akai gumurzu daga wasu daga cikin kannan iyayennasa. karshe aka yanke shawarar ya koma kaduna dan tafiyar d babban reshen kamfanin dake acan. A lokacin da mahaifiyarshi ke sanar dashi cewa yanxu tinda kagama karatu, ga aiki kanayi yanada kyau ace ka ajiye iyali, cikin murmushi y Kalli mahaifiyar tashi yace Umma aini na samu macen da nakeso. Cikin jin dadi ta tanbayeshi yar wana attajirin ce kokuwa yar sarauta, nan ya zaro idanunsa tare da cewa Umma wana irin attajiri ko sarauta kuma .ni auren zumunci zanyi, cikin rawar baki ta tanbaya auren zumunci kamar yaya, yace eh Aysha nakeso, salati ta fara da tafa hannu cikin kidimewa. Duk yara matan dasuke garin Kano karasa wadda xaka zaba sai Aysha,tace towaima Wacce Ayshar kake nufi ? nan ya sanar da ita cewa babbar yar Alhaji Sadiku kanin mahaifinsa. RYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 21-25 Hajiya Zuwaira mahaifiyar Alhaji karami ta tsinci kanta cikin rudu dajin babban dan nata zai auri Aysha, take taji kiyayyar Aysha da uwarta ta shiga zuciyarta. Yinin wannan rana bata cikin nutsuwarta sallamar kanwarta Uwale shi yadawo da ita daga zurfaffan tunanin data jefa kanta ciki. Sun shige daki tasanar da 'yar uwartata halim da take ciki, dariya Uwale tai tace haba yaya ke kika haifi Alhaji karami kokuwa shine y haifeki, ki futo ki nuna mishi kada ya sake y furta wannan magana ga kowa balle kannan mahaifinsa suji kadama abun yazamo rigima. Godiya tai mata, tare da alkawarin sanar dashi hakan t wayar salula. Alhaji karami na office yaji kira ya shigo mishi, ganin sunan d ya baiyana jikin screen din wayar sawa gabansa ya fadi, cikin gaggawa ya danna tare d karawa a kunne. Tamkar yana gabanta ya rissina tare d gaisheta, ta amsa cikin kulawa irin ta da da uwa, ta gargadeshi kan cewa wannan mgna da sukai karya sake y sanarwa da Aysha balle dangin babansu, sai yace Hajiya wannan magana bata waya bace kibari insha Allah cikin weekend zanxo miyi maganar cikin nutsuwa . Cikin dare Alhaji karami y kasa bacci juyi kawai yake daya rintse ido siffar Aysha ce ke yawo a kwakwaluwarshi, Aysha fara ce, doguwa, tanada round face wadda ke dauke da dara daran idanuwa, pointed noise, bakinta dan karami abin sha'awa idan tana magana, Allah y hore mata dukiyar fulani wanda suka taimaka wajen kara futowa da kyawunta, ga hips wadanda idan tana tafiya suke jan hankalin mutane, ba maza kadaiba, har mace zataso ace itace. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 26-30 Gefe daya kuwa aisha Da iyayenta basusan wainar Da ake toyawa ba, wannan lokacin tana makarantar secondary aji hudu wato SS1. Karatu kawai tasanya agaba ka in Da na in, mahaifiyarta batada addua har kullum sai Adduar Allah ya sada diyarta Da miji nagari. Aysha kawace ga zainab kasancewarsu sa annin juna, komai tare sukeyi , zainab kanwar alhaji karamice wadda take autarsu, gata yasa tazamo sangartacciya sai abunda takeso takeyi, ba wanda yake mata fada. Tinda Zainab taji cewa yayanta aysha yakeso tadaina kulata kota biyo mata makarantar islamiyya sai tace ta tafi ita b yanzu zata je ba Mahaifiyar Zainab din kuwa ta canjawa aisha fuska ko gaisuwarta ala dole take amsawa,wanda ada har kudin makaranta take bata ,abin ya daurewa aysha kai ita dai tasan wani Abu bai shiga tsakaninsu tsakaninta d kawarta Zainab. Bayan antaso su daga mkranta sai taga Zainab tana sauri zata tafi, kwalla mata kira ta Zainab, zainab, banxa tai da ita tacigaba d tafiyarta, da gudu tazo ta sha gabanta tare d rike hannunta zainab lafiya meke faruwa naga kwana biyu kin canjamin Budar bakin Zainab keda wuya sai cewa tai ancanja miki din. Bari kiji wallahi idan takamarku bin malamai keda uwarki, kunje kunyiwa yayana asirin da zai aureki to wallah karyarku ta sha karya, yayana ba abunda zai ci dake, yar matsiyata kije ki gayawa uwarki taje tasa akarya asirin datai inba haka ba kuwa saikin gwammace mutuwarki akan rayuwarki da yayana. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 31-35 Cikin tashin hankali Aysha ta dawo gida ,cikin gudu ta karasa dakin mahaifiyarta tana momy, momyna, Hajiya hafsat tayi mamakin jin irin kiran d 'yar tata take mata, lokacin tana daki tana gyaran wardrobe. Tafada kan cinyar momy tafashe da azababban kuka, momy ke tanbayarta lfy, waye y rasu. Takasa bude baki balle tai mgna,momy kuwa t zuba mata ido, saida tai mai isarta sannan tace momy Zainab ce. Hajiya Hafsat tace Zainab kuma fada kukai, dan kunsamu sabani d ita zakizo kina wannan gursheken kuka, tashi tai tabar mata daki saboda takaici. Ayshar tashi tai tabi momy zuwa parlour ta zauna kusa d momy nan t labarta mata maganganun d Zainab tagaya mata. Ta tambayi yar tata cikin tuhuma d zargi, dama yace miki yanasanki shine baki taba gayaminba a matsayina n mahaifiyarki? aysha tace wallhi Momy bai taba gayan haka ba, asalima gaisuwa kadai ke hadani dashi in mun hadu. Momy tace to shiknan karki kulata kuyi fada kinji diyata, karkifasa biya mata makaranta kullum kije tinda tare kuka saba zuwa. A wannan rana mamaki da tunani y cika zuciyar Hajiya Hafsa Allah yasa wannan magana kar ta baiyana balle wani yaji, sabida tasan diyar tata bazata taba jin dadin auren Alhaji karami ba saboda kiyayyar d 'yanuwansa suka fara nunawa Abu. Adduarta cikin kowacce sallah itace Allah y zabawa Aysha miji nagari wanda zai riketa amana d gaskiya. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 36-40 A can kaduna kuwa Alhj karami yana t tunanin t yanda zai shawo kan mahaifiyarshi t amince Mishi d samun cikar burinshi Yagama sawa ranshi Aysha ce abokiyar rayuwarshi, duk wani numfashi dazaiyi kara jin kaunarta yake a ranshi, shima yana mamaki yanda lokaci daya y fada tarkon sonta. Da misalin karfe goma jirgin su yasauka a filin sauka d tashin jirgin sama n Malam Aminu Kano. Sani direba ne ya daukoshi zuwa gidansu, dakin mahaifiyarshi y shiga, tayi murnar ganin dan nata. Hajiya Zuwaira macece maisan yayanta bataso taga abinda zai bata musu rai,haka zalika bata wasa d farincikinsu komai nata zata iya badawa dan farincikin 'ya'yan nata. A wannan lokaci ne taga alamar rama a jikin dannata, take tambayarshi koyayi ciwo ne? yace a'a Hajiya yanayin aikine da zurga zurga badan t yarda b, aka bar mgnar. Cikin kwantar d kai tare d kwlla a idanunsa yake sanarwa da mahaifiyar shi irin kaunar d yakewa Aysha, shi kansa y rasa yanda zaiyi. Idan ban aureta b Hajya b matar d xan iya zama d ita. Ganin dannata n zub d hawaye, ta amince d batun nashi dan farincikinsa, amma kasan zuciyarta ta kullaci Aysha d mahaifiyarta tare d cin alwashin ramuwa g asirin d sukaiwa dan nata. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 41-45 Alhaji karami y samu tsantsar farinciki, tare da godiya g Allah da yasanya Hajiya tai accepting bukatarshi, tare d yimata Adduar Allah y kara tsawan kwana Mai amfani d karin lafiya. Gefe guda kannansa abun duniya ya ishesu, saboda sunci burin yayannasu y auri 'yar manyan mutane masu naira yanda za'a yi bikin d ba'a taba yiba a danginnasu. Kwata kwata sundaina sakarwa Aysha fuska ko a hnya suka hadu tai musu magana banxa zasuyi mata hade d tsaki. A sanadiyyar karan tsanar d suka doramata, tadau alwashin ko yayannasu Yafurta yana sonta zata ba shi hakuri yaje ya nemi wata badan bata sonshi be, sai dan samun kwanciyar hankalinta. Tanada burin samun So da kauna daga dangin duk namijin da zai zamo miji gareta, dan samun zaman lfy d zuriya Dayyiba. A hankli magana ta fara zaga dangi cewa Alhaji karami yace Aysha yake so, mafi yawa dg cikin dangi bakin ciki suke dan ji suke dama 'ya'yansu yace yanaso. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 46-50 Washegari lahadi Alhaji karami ya je yasamu mahaifin Aysha dan sanar dashi bukatar shi tasan ya auri diyar shi, cikin farinciki ya amsa Mishi tare d mishi alkawarin cewa ya bashi ita, yaje su fuskanci juna. Alhaji Sadiku yayi farinciki tare d kwalla saboda ya tuno dan uwansa Marigayi Alhaji Sammani, dayana raye da sai yafi kowa farin ciki. Bazai taba mantawa b wataran suna zaune d yayannashi yace,da badan zamani y lalalace ba inada sha'awar muyiwa yaranmu auren zumunci, Alhaji Sadiku yace abine Mai kyau hakan, sai dai yaran wannan zamani ka haifesu baka haifi halinsu ba, kar mu hada abu karshe daya ya bijire muxo muji kunya, tuna wannan hira ya kara masa kwarin gwuiwa tare da alkawarin tabbatar d wannan alamari. Hajiya Hafsatu t kawo wa mijinta abinci suna dan taba hira, ya daga kai ya kalleta, yace Hafsatu yau fa ranar farinciki ce gareni, naso ace yaya Sammani yana raye muyi sharing wannan farin cikin, tace lafiya Alhaji meya faru, cikin zakuwa y shaida mata, fuskarta b yabo b fallasa, tace Allah y tabbatar d abinda yafi alkhairi, Alhj Sadiku yace hakanma shine alkairi, abinda nakeso dake kisanarwa da Aysha dan kowana lokaci daga yanxu zai iya zuwa gareta dan su fuskanci juna, tace to Alhaji za'a gaya mata. Washegari Alhaji Sadiku y tara 'yan uwansa maza ya sanar dasu, kowa yayi Adduar Allah yasa ayi damu, yasa kuma mutuwa ce zata raba. RAYUWAR AYSHA ( TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA LIASU 51-55 Sati n zagayowa Alhaji krmi ya sauka garin Kano musamman dan ganawa d hasken zuciyarsa wato Aysha. Tin safiyar waannan rana jikin Aysha yai sanyi, komai takeyi cikin karfin hali takeyi. Hajya Hafsatu ce karfin shirya abinci d za'a sauki Alhj karamin. A bangarenshi kuwa sabbin English wears y zarce Boutique y siyo duk dan y burge Aysha. Shi mutum ne marasan hayaniya, baida surutu, idan kaji tashin muryarshi to cikin abokan shine ana hirar kwallo (football). Misalin karfe hudu n yamma y futo daga wanka, cikin sauri y sanya kayan tare d taje sumar shi, turarukan shi gaba daya sai da ya fesa, wani irin kamshi sassanya ne ya cika dakin, duk d kasancewarshi Namiji bai fiya amfani d turaruka masu karfin kamshi ba. Misalin 3:30pm suka gama hada Ginger drink, Hajiya Hafsat ta umarci 'yar tata taje tai wanka ta shirya, nan Aysha taje ta shirya cikin atanfarta mai adon pink (Super exclusive)ta kafa daurin dankwali tamkar gwaggwaro batare d tayi make up ba kwalli lip balm kawai ta sanya. Ba karamin kyau kayan sukai mata ba, tamkar wadda zata futa wani gagarumin biki ko competition. Hajyn ce ta zabo mata mayafin (Veil) daya dace d kayan tare d yari, sarka d zobuna (custumes),turare Mai kamshi t fesa wa 'yartata, addua fal zuciyarta idan da alkhairi Allah y tabbatar d wannan alamari in babu Allah yayiwa diyar tata canji d mafi alkhairi. RAYUWAR AYSHA (TRUE LIFE STORY) BY AYUSHA ILIASU 56-60 Misalin karfe 4:00pm ya iso kofar gidansu Aysha, kai tsaye sallama yayi tare d shiga cikin gida, bangaren Hajy Hafsatu mahaifiyr Aysha y nufa, tana zaune a palour suna kallo tare d yaranta, cikin fara'a ta amsa sallamar. Har kasa ya durkus.
Subscribe to:
Posts (Atom)